Uncategorized

MEEMA FAROUK Page 21 to 30

Su ma dariyan suke taya shi ban da MEEMA da ido ta zuba musu tunda ba ta fahimta

Gaishe da su yayi kafin ya mayar da hankalin sa kan MEEMA yana tsokanar ta

Ita dai murmushi kaɗai take mishi har suka gama cin abincin suka koma Parlour

A nan ya ɓata lokaci kafin yayi musu sallama ya tafi. Dama ya zo wajen MEEMA amsar Laptop ne kasancewar ita ta taho da shi lokacin da suka tashi daga aiki tunda nashi ne.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

               Horn tayi har kusan biyar kafin me gadi ya buɗe mata ƙofa. Ta shige da motan ta zuwa wajen parcking. Fitowa tayi ta nufi Part ɗin su da ke a cikin gidan

Tana shiga parlour’n Momy da Abdul dake magana suka tsayar da maganar suna kallon ta

Ita kuma kai tsaye kan kujera ta nufa ta zauna tana ajiye numfashi

“Har kin dawo?” Cewar Momyn still tana kallon ta

“Eh.” Ta bata amsa a taƙaice. Sai kuma tace, “Momy da zan fita naga wasu ƴan jarida sun shigo nan gidan.”

“Nan gidan kuma?” Tafaɗa Momy mamaki cike a fuskar ta

Shima Abdul ya ƙara da cewa, “kina nufin ƴan jarida suka shigo gidan nan? To waye ya gayyato su?”

Tsaki ta ja da cewa, “waye kuwa ban da Yaya Umar. Wajen shi suka ce sun zo.”

Momy tace, “Mata ne ko maza?”

“Mata ne su biyu suka zo, Ni ban ma ga sun yi kama da ƴan jarida ba gaskiya.”

Momy tace, “ba na tunanin Umar Faruk zai gayyato su nan gidan duk da dai ban sani ba, amma kin san zaɓe ya kusa nan da kwana huɗu dole dama zasu takura masa, but mun yi maganar da shi kuma na san bazai ƙetare magana ta ba, babu wani amfanin yin hira da ƴan jarida bare har su tako wannan gidan.”

“Gaskiya ne Momy, Ni ina ga wankin hula yana so ya kai mu ga dare.” Abdul yafaɗa fuskar sa babu walwala ko ɗigo. “Momy i hate this Guy wlh! na gaji na gaji da ganin shi kiyi wani abu don Allah, Nima fa Ina so na fara watayawa a ƙasar, don Allah jibe yanda ya jajibo wani siyasa saboda iyayi don ya ga uban shi yayi, so nake yi Ni in gan Ni a matsayin sa Momy amma ba shi ba, Ni ya kamata nayi suna ba shi ba Momy. Sannan a kan wannan siyasan kowa zai san waye shi and kowa zai san arziƙi mu muke ci a gidan nan. Wannan ai tonon asiri ne.”

Ajiyan zuciya Momy ta sauke tana kallon shi tace, “kayi haƙuri Abdul da sannu burin mu zai cika, da sannu komi zai kasance namu, Ni fata na ba na so muyi wani abun da zai ja hankalin police a gidan nan, ka san yanda muka kashe Nusaiba a gidan nan, mun bata guba ta ci daƙyar muka samu muka tsallake zargin ta, ba don mun biya ASP kuɗi me yawa ba ba na tunanin zai goge hujjojin da ya samu a kan gaskiyar guban da aka bata, so dole sai da dabara burin mu zai cika a kan Umar Faruk, muna da sauran lokaci da zamu aiwatar da shirin mu, yau saura kwana huɗu ayi zaɓe, kafin lokacin dole zamu cika burin mu a kan shi, sai dai wani ba shi ba.”

Duk kan su murmushi ne ya suɓuce a fuskar su

Yayinda Luwaira wacce fuskar ta babu walwala ta buɗe baki da ninyan yin magana sai suka ji Nocking a bakin ƙofa

Shiru duk suka yi ko wanne yana kallon ƙofan. Sai da aka sake Nocking ɗin ne kafin a tare Momy da Abdul suka amsa, “yes. Waye ya shigo.”

Hafsah da Yusra ne suka fara shigo wa kafin shi ya biyo bayan su. Kamar yanda ya saba yayi shigan shi na manyan kaya, farar shadda wacce sai maiƙo take yi tsaban sabunta da ɗaukan guga, tamkar wani ango sabida kyawun da yayi, gaba ɗaya turaren sa ya cika parlour’n da ƙamshi. Da gudu yaran suka isa wurin Momy suna rungume ta. Yayinda shi kuma ya taho a cikin ƙasaitan sa ya sami wuri a kan kujera ya zauna

Momy sai rungume yaran take yi tana musu maraba da zuwa fuska a washe

While Abdul yace, “to ku taho nan mana yara na, Momy kaɗai kuka sani ne?”

Da gudu suka dawo jikin shi suna kiran sunan shi da, “Uncle Abdul.”

Ya rungume su yana cewa, “yauwa babies ɗina.”

Umar Faruk da ke murmushi sabida yanda suke nuna wa yaran shi ƙauna sai ya mayar da idon shi kan Momy yace, “dama zan fita ne ina da meeting sai zuwa dare zan dawo, kuma ba na so su zauna su kaɗai, idan na dawo komin dare zan zo in ɗauke su.”

Momy cike da fara’a tace, “ok babu damuwa my son. Ka kula da hanya ka san zaɓe ya kusa, kar ka soma ka fita kai kaɗai ka je da masu tsaron ka Please my son. Allah ya kiyaye ya dawo min da kai gida lafiya, Allah ya bada sa’ar abun da aka je nema kaji ko?”

Cike da jin daɗi wanda ya nuna a fuskar shi yace, “Amin Momy. Sai na dawo.” Ya ƙare maganar da tashi tsaye. Idanun sa a kan Luwaira yace, “Luwaira babu addu’a kamar muna faɗa?”

Murmushi tayi tace, “haba yaya ko zan yi faɗa da kowa ai bazan yi da kai ba. Ina jiran Momy ta gama nata ne Nima inyi maka nawa special.”

Murmushi yayi da cewa, “no ba na tunanin naki ne special ke dai kar ki ɓige da daɗin baki. Na Momy na ne special. Yanzu dai yi min naki in tafi.”

Daga Momy har ita dariya suka yi

Momy tace, “yauwa ɗan albarka ashe dai ka gano ta.”

Murmushi yayi kaɗai

Luwaira tace, “to Yaya Allah ya tsare ya kare hanya.”

“Amin my dear sister. Ban manta da maganar ki ba idan na dawo zamu tattauna ko zuwa gobe.”

Washe baki tayi tace, “to Yaya.”

Daga nan fita yayi bayan ya sake yiwa yaran shi Ba-bye.

                 Yana fita Momy ta kira Talatu me aikin ta tace, “kwashe su ki wuce da su ɗakin ki ku zauna tare.”

“To Hajiya.” Tafaɗa tana jan hannun yaran

Sai Hafsah ta ɓata fuska tace, “Ni bazan je ba wajen Uncle Abdul zan zauna, ai yace zai kai mu shan Ice cream.”

“No Hafsa ki je wajen ta ai ba yanzu zan fita ba, yanzu akwai abin da zan yi zuwa anjima sai mu je ko?” Yafaɗa hakan da murmushi a fuskar sa yana riƙe da kumatun ta da hannayen sa biyu

Murmushi tayi masa sannan ta bi bayan Talatun da ke riƙe da Yusra suka wuce

Tafiyan su Luwaira ta ja dogon tsaki tace, “wlh Momy na tsani yaran nan sosai kamar yanda na tsani uwar su. Ni ban ga amfanin su ba, kamata yayi su ma a aika su inda uwar su ta tafi.”

“To abin hauka ne ashe? Ki bar maganar yaran nan ƙananan alhaki, idan mun gama da uban su zamu dawo kan su. Shirin mu kawai na plan A. Yanzu zamu mayar da hankali, idan haƙan mu be cidda ruwa ba zamu sauya wani shawaran. Abdul kai yanzu ya kamata ka samo mana waɗanda zasu yi aikin nan, in two days komi zai kammala ba na son a wuce wannan ranan.”

“An gama Momy. Bari in je akwai inda zan je yanzu. Idan na dawo zamu yi magana.”

“To.”

Daga haka ya tashi ya fice

Luwaira kuma ta dawo kusa da Momyn tana ɓata fuska da cewa. “Ni Momy meyasa baza ku amince da nawa plan ɗin bane? Gaskiya ba na jin zan haƙura da shi cikin sauƙi haka. Ku taimaka min Momy.”

“Ban san shirmen banza ke Luwaira. Wai meyasa kike haka ne sai mun kai magana ki dawo damu baya? Gwara ma idan zaki cire wannan shirmen naki a zuciya ki cire shi tun wuri, baza ki taɓa auren Umar Faruk ba, ke ma kin san da haka kar ki sake zuwar min da wannan maganar. Dalla tashi ki ban wuri.”

Zumɓura baki tayi tana ƙunƙunai kafin ta tashi ta wuce

Ita kuma ta ja dogon tsaki tana bin ta da mugun kallo. “Idan ba iskanci irin naki ba ko mu mun amince shi zai amince ne? Ba na tunanin zai taɓa auren ki tunda yana kallon ki a matsayin ƙanwar shi ce. Kina so ki mayar da mu baya naga alama zamu dena saka ki a aikin mu, duk wannan abin da nake yi ina yi ne duk don ku amma ke ta banzan shirmen ki kike yi, to sai dai ki mutu kuwa don baza ki taɓa auren shi ba.” Haka Momyn ta ci gaba da faɗa ita kaɗai duk da ita Luwaira tuni ta wuce ɗaki abun ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button