MEEMA FAROUK Page 21 to 30

Wayance wa Murjanan tayi tana sakin guntun murmushi da cewa, “Please barrow me your phone because I don’t have a card in my own, I want to make a phone call with my friend’s”.
Mamaki ne ya hana MEEMAN motsi illa kallon ta da take yi. Bata ce komi ba dai ta ɗauki wayan ta miƙa mata
Sai da tace, “You did not remove the code.”
Sannan ne ta tuna ta cire mata ta miƙa mata
Murjana ta so ta ga yanda take cirewan ne, but yanayin yanda take sauri wajen danna code ɗin yasa bata fahimci komi ba, dole ta amshi wayan don kar ta gane wani abu, ta samu wuri a gefen gadon ta zauna sannan ta saka Numban Abba ta kira sa. Yana peaking tace dashi, “hello Murjana ce”. Shiru tayi tana sauraron sa sai kuma tace, “eh na amsa wayan amma ban ga yadda ta cire ba”… “Ok to”. Daga nan sai ta katse wayan ta goge Numban ta miƙa mata tana sakin guntun murmushi da cewa, “thanks”.
Gyaɗa mata kai kawai tayi ta amshi wayan ta ajiye, sai dai ta kasa ci gaba da abun da take yi domin har yanzu mamakin ta take yi. Ganin ta ƙi tashi a wurin sai ma kwanciya da tayi shiyasa ta kashe computern tare da miƙe wa ta kai ta ajiye a cikin Trolly ɗin ta, sai ta koma can gefen gadon ta soma dealing Numban Ishaq, sai dai har yanzu ba ya shiga that’s why ta mayar da akalan kiran ga Esha. Gyara zaman ta tayi jin ta ɗauka ta sauya harshe zuwa larabci suka soma waya, sun jima suna waya duk a kan Ishaq ne da yanda za’a yi Eshan ta je gidan su ta duba mata shi, sai ta samo mata Numban shi
Murjana na zaune tana jin ta sai dai ba ta fahimtan komi shiyasa ta tashi ta fice
Fitan ta yasa MEEMAN ta tsakaita wayan tare da yin ma Esha sallama sannan ta ajiye wayan. Shiru tayi tana me faɗa wa tunani, a haka har aka kira sallah ta tashi tayi ta koma ta sake kwanciya, ko fita ta ci abinci ta ƙi yi
Sai ga Murjanan ta zo kiran ta, “su ci abinci”.
She looks at her in amazement, sai dai bata ce komi ba and she got up and followed her
Suna zaune duk kan su a saman dainning
Da sauri Sajjad ya tashi ya ja mata kujeran kusa da shi yana mata murmushi da cewa, “have a seat Baby”.
Ko kallon sa bata yi ba ta samu wuri ta zauna
“Daughter, don’t go into the room. You sit here with your siblings, stay in them and talk to them ok?” Inji Abba yana kallon ta da murmushi
Jinjina kanta tayi kawai ba tare da tace uffan ba
Sajjad da ya ɗauki Plate zai yi serving ɗin ta yace, “What will you eat if I pour it on you?”
“Nothing”.
Abba said, “you mean you don’t eat anything?”
“I’ll have some tea.”
“Tea is not food Daughter. Carry and eat ok?”
Still kanta ta jinjina masa
Sai yace, “Sajjad serve her”.
“Ok Abba”. Shi ya zuba mata jollof rice ɗin tare da veggies ya tura mata a gaban ta
Bata ce komi ba ta ɗauki spoon ta soma ci kaɗan-kaɗan don ko kwatan cokalin ba ta iya cuko sa
Shiru wurin ya ɗauka kowa sai cin abincin sa yake yi, while Sajjad gaba ɗaya hankalin sa na kan MEEMA, sosai yanda take cin abincin nata ya ɗauki hankalin sa har yana manta wa da shima abincin yake ci
Sai da Murjana ta bugi cokalin sa sannan ya dawo hayyacin sa, “kai yaya ka mayar da hankali a kan abincin ka ba guduwa zata yi ba kuna tare”.
Hararan ta yayi yana langaɓe kai ya kalli Umma yace, “Umma ki ce mata ta fita harka ta yarinyan nan”.
Taɓe baki ita kuma tayi bata ce komi ba illa abincin ta da take kaiwa baki fuska babu walwala
Murjana tace, “Yaya ya kamata ka kaimu shopping da ita hakan zai saka mu sake shiga jikin ta, ko ya Abba?”
“Yes haka ne Murjana,” sai ya kalli MEEMAN yace, “Daughter, are you going shopping with your siblings and seeing the city.”
MEEMA da ta ɗago kai tana kallon sa kasa cewa komi tayi. Sai da ya sake maimaita mata sannan tace, “ok”. Ta mayar da hankalin ta kan abincin da take ta faman cakala. Ita ta soma tashi ta wuce ɗaki
Hakan yasa da sauri Murjana ta tashi ta bi bayan ta. Tana shiga ɗakin ta ganta a zaune sai tace, “get ready to go don’t Bro Sajjad hear us silently”.
Bata ce komi ba ta miƙe ta shiga Toilet ɗin, wanka tayi bayan ta fito sai Murjana ta shiga
MEEMA tayi shirin ta kamar ko yaushe yanda ta saba, bayan ta saka riga da wando sai ta ɗauki Abaya baƙa me kamar alkyabba ta sanya, ta yane kanta da farin gyale me Stones wanda ya ƙara fito da cuty face ɗin ta sosai ta ƙara yin fayau kasancewar babu abinda ta sanya, babu wani annuri a face ɗin ta haka suka fice a ɗakin ita da Murjana
Sajjad dake jiran su a Parlour tun fitowar su ya kasa ɗauke ido a kan MEEMA, gaskiya Allah yayi diri a nan wurin, yana rasa nutsuwar sa a duk sanda yayi tozali da ita ji yake yi kamar ya je ya haɗiye ta tsaban shauƙin da yake ji a kanta, har yana jin kamar bazai iya jure har nan da one month be mallake ta ba, be san ya zai yi da tarin buƙatuwar ta a zuciyar sa ba. Daƙyar ya iya control kansa suka fice a gidan bayan sun yiwa su Abba Good bye
Da suka fita MEEMA baya tayi ninyan shige wa sai Sajjad ɗin yace, “ta dawo gaba”.
Tsaya wa tayi tana kallon sa while tana sake haɗe kyakykyawar fuskar ta
Shi kuma murmushi yayi mata yana sake roƙon ta a kan, “She Return the front seat”.
Kasancewar Murjana tuni ta shige baya shiyasa ta buɗe gidan gaba ta shiga
A haka ya ja motan suka fice a gidan
Duk inda suka bi idanun MEEMA na kai, sai kallon yanayin garin take yi duk da ba wai farin ciki take ji a zuciyar ta ba
Hakan da Sajjad ɗin ya gani ne yasa yake mata bayanin duk inda suka wuce
Sai dai bata kula sa ba har suka kai wani ƙaton shop Mall suka fito. Tana biye da su duk inda suka sanya ƙafa har suka shiga ciki. Sai dai duk yanda suka yi da ita, “ta dauki abun da take so.” but ta ƙi ɗauka
Dole Sajjad da kansa ya dinga jidan mata abubuwan duk da ya ga yayi masa
Itama ta fannin Murjana duk abinda ta ɗauka tana daukar mata, domin tana ganin ta hakan ne zata sake shiga jikin ta sosai idan ta bata kayan a matsayin gift ɗin ta.
Har suka gama suka fito suka wuce wajen shan Ice cream, nan ma MEEMA ta ƙi taɓa duk abin da suka bata, ce musu tayi, “she does not want to drink anything.” Dole suka kyale ta sabida banza tayi da su daga baya
Murjana tace, “gaskiya Yaya kana da jan aiki a gaban ka wajen yarinyan nan, Allah ba na tunanin zata so ka ko kaɗan, kana gani fa abun da take yi ko magana wannan bata taɓa yin maka ba”.
Sajjad da kamar zai yi kuka yace, “Murjana nima ban san meyasa take min haka ba? Kina ganin akwai makusa a jiki na da har zata ƙi so na?”
Murmushin ƙeta tayi kafin tace, “babu Yaya sai dai kawai ina tunanin har yanzu bata saba da mu bane, tabbas akwai abun da ke ranta da har ta ƙi sakin jikin ta da mu, amma ina ga duk sanda ka aure ta sai yanda ka juya ta Yaya, nayi maka alƙawari sai ka juya ta kamar waina domin sai ta koma a tafin hannun ka, kawai ka bari lokaci yayi Yaya kai da kanka zaka sauke mata duk wani abun da ke kanta”.
Dariya yayi yana ɗan shafa tulin gashin kansa, sai ya kalli MEEMAN da hankalin ta ke kan waya amma tana sauraron abun da suke faɗi, sai dai kasancewar ba ta gane abun da suke cewa shiyasa bata san da ita suke yi ba. “Ƙanwata nima wannan lokacin nake jira, abu ɗaya ne yake hana Ni aikata abin da ke raina a halin yanzu a kanta, sabida kawai ina son mallakan ta that’s why komi nake yi a sannu, ai kamar yau ne wata ɗayan zai cika.” Sai ya ci je leɓe yana faɗin, “zata san waye Sajjad Aliyu Ahmad Riskuwa”.