Uncategorized

MEEMA FAROUK Page 21 to 30

             Da safe bayan ta gama shirya wa ta fito ta sami me napep ya kaita tasha inda zata samu motan Kaduna. Wannan karon ma drop ta ɗauka suka wuce Kaduna, wajen goshin magriba suka isa.

           A cikin G.R.A Ummeen ta take zaune ita da Mahaifiyar ta da ƙanin ta, shi yanzu ƙanin nata ya koma Abuja da zama da shi da Matar sa da ɗan su guda ɗaya, wajen shekaru shidda kenan da aka tura sa yaƙi ya tafi ya bar matar tasa a can Abujan kasancewar tana aiki shiyasa bata dawo nan Kaduna ba, sannan kuma ɗan su na school wannan dalilin ne ya zaunar da su can, sai dai jefi-jefi tana zuwa Kadunan ta gaishe su. Yanzu haka mahaifiyar Ummee me suna Hajiya Halima suna kiran ta da Hajiya, tana cikin halin rashin lafiya na hawan jini wanda yasa har ta rasa ƙafafuwan ta tana zaune a wheelchair ne. Mahaifin su Ummeen shi ya daɗe da rasuwa, su biyu Hajiya ta haifa daga ita sai ƙanin ta Captain Hashim. Kuma mahaifin su dai-dai gwargwado ya bar musu dukiya me ɗumbin yawa, don gidan su babban gida ne me hawa biyu. Part ɗin Hashim da matar sa daban duk a ciki idan ya zo hutu suna sauka a nan, sannan sai na Hajiya sai kuma inda Ummee ke zaune a halin yanzu, tana aiki ne a wani Company tun dawowar ta daga Riyadh.

                Kwatancen da MEEMA ta yiwa Me motan be sha wahala ba wajen tambayar mutanen garin, tunda sun rigada sun shiga G.R.A ɗin, duk da MEEMA bata taɓa zuwa ba amma ta riƙe sunan gidan su Ummeen nata sosai tunda ba wani ɓoyayye bane, har Numban gidan sai da Abee ya sanar mata da zai rasu hakan yasa nan da nan suka gano gidan.

          Bayan ta sauka ta sallami me motan ta ɗauki kayan ta ta taka a hankali zuwa bakin Gate ɗin. Ta jima a wurin tana ta kallon ƙofar gidan ta kasa buga wa, lokaci ɗaya idanun ta suka cika da hawaye yayinda zaciyar ta ta soma zugi tsaban ƙuncin da ya ziyarce ta a halin Yanzu ɗin. Ba komi ya haifar mata da hakan ba sai tuna wa da tayi a yau zata haɗu da mahaifiyar ta wacce ta guje su a cikin rayuwar su gaba ɗaya, kuma bata taɓa tunanin ta neme su ba har ga shi Abee ɗin ta ya bar duniya da baƙin cikin ta, ta kasa gane wani irin abu ne Abee ya aikata mata da har ta zaɓi tayi masa wannan mummunan hukuncin? Baƙin ciki da ƙuncin da take ji a wannan lokacin tamkar yanzu ne Ummeen ta tafi ta bar su, sanadin ta sun rasa farin cikin su wanda hakan yasa ta rasa mafi soyuwa a rayuwar ta wato Abee ɗin ta. Sai kawai ta fashe da kuka sosai har bata iya ganin komi tsaban yanda hawayen suke kwaranya a face ɗin ta. Hannu ta sanya ta dinga share wa yayinda wani tuƙuƙin baƙin ciki ke kai komo a maƙogwaron ta. Ta kasa ɗaga ƙafafu ta isa bakin Gate ɗin bare ta buga. Tana nan tsaye wadda ta fi mintuna talatin a wurin har an kira sallan magriba ana shirin shiga

A lokacin ne aka buɗe Gate ɗin gidan wanda me gadi ne da shi da masu hidiman gidan su biyu suka fito zasu wuce masallaci. Da kallo suka bi ta ganin ta da suka yi a wannan yanayin kuma a jikin gidan su. Sai dai babu wanda ya samu halin yin magana illa idanu da suke bin ta da shi kamar wacce basu taɓa ganin halitta makamanciyar nata ba, gaba ɗaya a cikin zuciyoyin su mamakin ganin Balarabiya a bakin ƙofar gidan suke yi. A haka har suka wuce ta suna waigen ta

While MEEMA tunda tayi musu kallo ɗaya taci gaba da share hawayen ta kafin ta ja ƙafafu a hankali ta isa ƙaramin ƙofan ta tura ta shige. Kallon gidan take faman yi tana tafiya a hankali har ta isa ƙofar da zata shiga gidan, a nan ma ta ɓata lokaci kafin ta sanya hannun ta dake faman rawa ta soma Nocking. Kasancewar a hankali take Nocking ɗin shiyasa sai da ta ɗau lokaci tana yi kafin a zo a buɗe mata

Wata mata ce me jiki don a ƙalla zata kai shekaru arba’in, wanda daga gani ƴar aikin gidan ce. Tunda ta ɗaura ido a kan MEEMAN ta tsaya kallon ta, sai da ta gama ƙare mata kallon kafin tace, “baiwar Allah daga ina?”

Ita MEEMA yanda bakin ta yayi mata nauyi shiyasa ta kasa yin magana illa zuba mata idon itama da tayi tana bin ta da kallo. Koda tayi mata maganar bata fahimci abun da tace ba amma hakan yasa ta buɗe baki a hankali tace, “May I come in?”

Jin tayi turanci kuma bata gane ba kasancewar yanda take furta words ɗin sai Matar ta sake cewa, “to Ni gaskiya ba na jin ki ina zuwa”. Sai ta juya ciki tana ce ma Hajiya dake zaune a kan wheelchair ɗin ta, “wata budurwa ce ta zo Hajiya, amma gaskiya ba na jin yaren nata, turanci ne ko wani yaren ne oho don maganar nata wani iri wlh, Idan kika ganta kamar ba ƴar nan bace, sanye da kayan Larabawa ta zo”.

Hajiya dariya tayi da cewa, “Kai Zabba’u kin cika Zabbo ta, wlh kin ci sunan ki. Idan ban dake memakon ki zauna kina min kwatancen ta ai gwara ki ce mata ta shigo kin bar ta a waje kuma”.

“To kuma fa haka ne Hajiya, to amma kin san yanda duniya babu gaskiya shiyasa gwara in soma sanar muku don wlh ban yarda da ita ba Ni daga kallon ta, sak bata yi kama da ƴar nan ba, yaren nata ma fa ban fahimci me tace ba don ba turanci bane ai da zan gane ko ya ya ne tunda ina jin kaɗan-kaɗan.”

“Ki dai zauna kiyi ta rattaba zance da Allah kin bar baiwar Allah a waje”. Hajiya tafaɗa tana jan guntun tsaki

Hakan yasa Zabba’un ta wuce da sauri bayan ta ce, “to kiyi haƙuri Hajiya kar ranki ya ɓaci, bari in CE ta shigo to”. Tana zuwa bakin ƙofan tace da MEEMA, “shigo baiwar Allah”.

MEEMA da bata fahimci me tace ba ko motsi bata yi ba sai kallon ta da take yi

Sai Zabba’un ta sake maimaita mata da gwarancin turancin ta tana sanar mata, “ta shigo ciki”.

A hankali ta taka ta shiga ciki idanun ta suna faɗa wa kan Hajiya wanda itama ta kafe ƙofar da kallo

Da sauri ta furta, “Zulaiha ke ce?”

Har gaban ta ta tako ta tsaya ba tare da ta furta komi ba illa son hana fitowar hawayen ta da suke maƙale a kwarmin idanun ta

“Ya ki Jika ta, taho.. taho wuri na”. Hajiya ta furta cike da rawan baki tsaban murnar ganin MEEMAN

Yanda take ya fico ta da hannun ta ne yasa ta isa gare ta a hankali tana duƙa wa a gaban ta

Hannayen ta ta kama cike da farin ciki kamar zata yi kuka tace, “Will I ever see you again? How did you get here? Who brought you? Where is your father?”

Bata iya amsa mata ko kalma ɗaya ba duk da a ranta ta ɗan ji sanyi da yanayin karɓar da tayi mata, sannan kuma farin cikin da ta ga ya bayyana a fuskar ta yasa ta gane tana murna da zuwan ta. Shiyasa ta matsa sosai ta rungume ta hawayen idanun ta suna sauka kamar an kunna su

Sosai itama Hajiyan ta sake ƙanƙame ta a lokacin tana kuka da sambatu

Ita dai Zabba’u baki ta kama kawai tana kallon su. A lokaci ɗaya kuma sai ƙwaƙwalwan ta ta bata ƙila yarinyan Ummee ce, domin ta san da cewar tana da ɗiya kasancewar wani lokacin tana yawan jin suna ambatar ta, sai dai a zahiri bata taɓa ganin ta koda a hoto ne duk da ta daɗe a gidan tun kafin Ummee ta dawo Nigeria, shiyasa tayi tunanin ita ce ɗiyar Ummee duk da ba wai kama suke yi ba, amma Idan ka kalle ta tabbas zaka gane jinin ta ne.

         Sun jima a haka kafin Hajiyan ta sake ɗago ta tana me riƙe mata hannu da cewa, “Zulaiha, will we see you again? Your mother do not came to check on you, and I was sick and had legs, and your uncle was not in the country to go and check on you and your father, I hope he feels better?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button