MEEMA FAROUK Page 21 to 30

Fashe wa tayi da kuka tana girgiza mata kai tace, “My father is dead. He is dead.. He is dead.” Yanda kukan ya ci ƙarfin ta ta kasa ƙarisa zancen nata dole tayi shiru tana sake rungume ta a wannan lokacin tana kuka sosai
Salati kawai Hajiya take yi tana bubbuga bayan ta. Sun jima a haka kafin ta ɗago ta taci gaba da rarrashin ta, sannan ta kalli Zabba’u da har yanzu tana wurin tana ta kallon su, tace da ita, “ki kawo mata ruwa ta sha sannan ki kira min Zulaiha a ɗaki”.
“To Hajiya”. Ta amsa ta tana wuce wa wurin Fridge ɗin da sauri
Ita kuma Hajiya hannu ta sanya tana share mata hawayen fuskar ta tana ci gaba da rarrashin ta, sannan ta ɗago ta ta zaunar da ita kan sofa dake jingine da wheelchair ɗin ta. Da Zabba’u ta kawo ruwan ita da kanta ta amsa ta bata ta sha tana sake shafa mata fuska cike da rarrashi
Zabba’u da ta wuce kiran Ummee bata kai ga hawa benen ba ita Ummeen ta fito daga saman zata sauko, kyawu da zubi da tsari gami da haɗuwa da tsaban iya kwalliya shi zaka soma gani a tattare da ita, a kallon farko baza ka taɓa ce mata ta haura shekaru arba’in ba, but tsaban kyawun jikin ta da ɗaukan wanka irin nata sai kayi tunanin ƴar shakara talatin ne, sam bata da jikin manyanta. Tana sanye da lesi me uban tsada da tsantsan kyawu, gaba ɗaya hannayen ta da wuyan ta duk ta zuba sarƙa da awarwaron Gwal sai walwali suke yi, fuskar nan nata ya ɗau Powder duk da ba kwalliya ne a fuskar ba, yanda take tafiya zaka tabbatar da babban mace ce me aji sosai. Tun daga saman benen idanun ta suka sauka a kan MEEMA, sai dai bata gasgata itan bace kasancewar ba ta ganin fuskar ta sosai. Hakan yasa ta ɗan ƙara sauri wajen sauko wa tana son ƙaryata idanun ta. Sai dai bata gama ƙarisowa ba suka haɗa ido da MEEMAN wanda a lokaci ɗaya ta tsaya cak daga inda take tsaye.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT* ????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_19*
Wasu sabbin hawaye ne suka wanke mata fuska saboda arba da tayi da fuskar mahaifiyar ta a yau, kimanin shekaru biyar da watanni kenan rabon da ta sake tozali da ita. yanda idanuwan ta suke mata zafi ne yasa ta mayar da idanun nata ta rufe ruf tana sauke numfashi daƙyar
While itama Ummee tuni hawayen ne suka cika mata idanu, sai dai ta kasa samun ƙwarin gwiwan da zata iya tunkaran MEEMAN a halin yanzu, gaba ɗaya ta kasa motsa wa a inda take
Inda Hajiya tace da ita, “ki ƙariso mana kin tsaya a wurin, ko zuwan nata ma baki yi murna da shi bane?”
Girgiza kanta ta soma yi still hawaye na zuba a face ɗin ta, sai a lokacin ta samu damar taka wa ta iso gaban MEEMAN zata sanya hannu ta taɓa ta tare da furta, “My daughter…”
Saurin janye jikin ta tayi tana tashi da sauri, ido cikin ido take kallon ta cike da wani irin yanayi da fushi a tattare da ita tace, “Don’t touch me again! I am not your daughter because I will never be your daughter.” Sai ta juya ga Hajiya cike da rawan murya a wannan lokacin tace, “She is not my mother. If she touches me again I will leave this house. I will enter the world wherever I am and, I will not stay here.”
Gaba ɗayan su shiru suka yi suna sauraron kukan ta da a yanzu take yi da ƙarfi wanda ke fita da ɓacin rai da tuƙuƙin baƙin cikin da ya kasance da ita tsawon shekaru
Hajiya ce tayi ƙarfin halin kiran sunan Zabba’u tana bata umarnin, “ta kai MEEMAN ɗakin kusa da nata”.
Hakan yasa ta iso da sauri ta ja Trolley ɗin bayan ta ɗauki ƙaramin
Hajiya ta yiwa MEEMAN bayanin, “she follow her.”
Bata ce komi ba ta bi bayan Zabba’un har ɗakin da zata kaita, a downstairs ne ɗakin bayan ka wuce dogon corridor zaka hangi ɗakuna guda biyar a jere, ɗaya daga ciki ta shigar da MEEMAN. Dayake ɗakin babu datti tunda a koda yaushe ana gyara wa, tana ajiye mata jakan ta ta fito ta bar ta.
********
“To kin gani abun da nake gudan miki kenan tuntuni Zulaiha, son zuciya da ruɗin ƙawaye yasa kin aikata mummunan aikin da zai ja miki dana-sani a rayuwa, yanzu ke baki ji kunya ba da kiran ta da kika yi a matsayin ɗiyar ki? Kin san kina son ta meyasa kika yanke wannan hukuncin? Dama na sha sanar miki akwai ranan da zaki yi nadama, tunda kika tafi kika bar su baki sake waiwayan su ba, sannan ni ba ƙafa ba bare in je in ga lafiyan su, wanda kuma zai je ɗin yanzu kusan shekaru shida kenan basu dawo ba, bamu da tabbacin yana raye a halin yanzu ko ba ya raye, wata huɗu kenan da wayan Hashim ba ta shiga, ba don haka ba da shi ne zai riƙa zuwa yana duba mana a halin da suke ciki. Ni na tabbata Faruk ya tafi da baƙin cikin ki a zuciya domin kin cutar da shi sosai, ya koma ga Allah ya bar ki a duniyar da kike ganin ya fi miki shi, mutum me ƙaunar ki amma kika kasa zama ki tallafi rayuwar sa da ɗiyar sa, wannan wani irin zuciya ce da ke Zulaiha? Anya kina da ɓurɓushin imani?”
“Wlh Hajiya nayi matuƙar nadaman abin da na aikata, na san zuciya ta bata yi min adalci ba da har na yanke hukuncin barin su, amma wlh ina matuƙar nadama da abun da nayi musamman ma a yau…” Kukan da ya ci ƙarfin ta yasa a dole tayi shiru
Hajiya tace, “hmm kaɗan ma kika gani, yanzu ga shi kin koya wa ɗiyar ki tsanar ki a zuciya, ba na tunanin a yanzu kina da wani sauran mutunci a idanun ta, wacce ta tafi ta bar ƴar ta tsawon lokaci babu waiwaya ai ba na tunanin akwai wani sauran soyayya, gwara ma ki tashi min a nan tun kafin raina ya ɓaci, kuma ban amince ki takura mata ba domin muddin ta bar gidan nan a sanadin ki wlh sai nayi mummunan saɓa miki Zulaiha”. Daga haka Hajiyan ta kwaɗa wa Zabba’u kira. Tana zuwa tace mata, “ta mayar da ita ɗaki.”
Haka ta ja ta suka wuce ɗakin Hajiyar suka bar Ummee a wurin tana ta faman share hawaye. Zuciyar ta sosai take mata tuƙuƙi da baƙin ciki sabida fama abun da ke cikin ta. Ta jima a wurin ta rasa me ke mata daɗi, daga ƙarshe ta tashi ta wuce ɗakin da aka sauke MEEMAN
Tunda ta shiga ɗakin MEEMA ta sauke ido a kanta sai tayi saurin kawar da su tana sake haɗe rai sosai
Ita kuma a hankali ta taka izuwa bakin gadon da take zaune, kasa zama tayi illa tsaya wa da tayi tana kallon ta yayinda idanuwan ta har yanzu suna da danshin hawaye. A hankali ta soma magana a cikin harshen turanci. “I know I was wrong with you and your father, and I do not know how to apologize to you. I was a mother who loved herself more than anyone else. I followed the deceptions and advice of my friends. I made a big mistake that I now know…” sai tayi shiru sabida kukan da ya taho mata sosai a yanzu ɗin. Daƙyar ta iya buɗe baki da zummar taci gaba
Sai MEEMAN ta dakatar da ita wajen ɗaga mata hannu da cewa, “enough..! I do not want to hear your words in my ears, you are a tyrant in my place, you do not love me and you do not love my Abee, if you had faith you would never do that to us, how can I call you mother? Do you think that is appropriate? Tell me, do you think that is appropriate?” Ta ƙare zancen da wani irin ihu tana kuka sosai. Sai kuma ta haɗe hannayen ta wuri ɗaya tana haɗa su da fuskar ta tace, “please leave this place before my heart beats, I do not love you and I don’t want to see you around me!”