Uncategorized

MEEMA FAROUK Page 21 to 30

“Daughter…”

“Please out”. Tafaɗa cikin tsawa yayinda take kallon ta a wannan lokacin ido cikin ido hawaye na zuban mata

Shiru Ummeen tayi ta kasa motsa wa, sai kuma a hankali ta juya ta fice har tana sake waigo ta

Ita kuwa tuni ta kifa kanta a saman gadon ta soma rusa kuka sosai, ji take yi kamar ta haɗiye zuciya ta mutu tsaban baƙin ciki, why Ummee zata yi mata haka? Anya ita uwa ce a gare ta da har ta zaɓi rabuwa da su? Ba ta tunanin akwai wata uwa makamanciyar nata uwar, shin wani hujja ne da take da shi da har zata tsallake tabar su alhalin suna matuƙar buƙatar ta? Tana ga rashin lafiyan Abee ɗin ta ba hujja bace da zata aikata musu haka, abun da take gani kawai Ummeen ta bata da imani, rashin imanin ta ne yasa ta aikata musu wannan abun, to, don me itama zata ɗauke ta a matsayin uwa? No hakan bazai taɓa yiwuwa ba domin tun sanda ta tsallake ta bar su itama ta cire ta daga zuciyar ta, a yanzu ita ba mahaifiyar ta bace, bata da kowa a yanzu sai ita kaɗai, a ko yaushe kuma hakan zata riƙa ɗauka… ta jima a nan zaune tana ta sharɓan kuka wanda har kanta ya soma mata zugin ciwo kafin ta shafa wa kanta lafiya ta haƙura, kiran sallan da ta ji ana yi shi ya ankarar da ita bata yi sallolin dake kanta ba, don haka ta tashi ta shiga Toilet ta ɗauro alwala ta ciri hijabin ta ta soma rama sallolin ta

Tana cikin yi ne Zabba’u ta shigo ɗakin, ganin tana sallah sai ta juya, babu jima wa kuma sai ta dawo da ƙaton faranti a hannun ta ta ajiye mata ta fice

Ita kuma ta jima tana sallan, sai da ta haɗa da shafa’i da wutri sannan ta sallame sallan, ta zauna yin addu’o’i na tsawon lokaci kafin ta shafa, yunwan dake addabar ta shi ya sanya ta jawo farantin ta zuba abincin dake cikin coolar a cikin ƙaramin Plate, haka tayi ta tusa abincin a baki ba don yana mata daɗi ba, duk tsawon lokacin da ta ɗauka tana cin abincin ko rabin Plate ɗin bata yi ba ta ture ta tashi tsaye. Wanka ta shiga tayi kafin ta sanya kayan barcin ta tabi lafiyar gado. A lokacin wajen ƙarfe 11:30pm. Na dare ne, sosai tunani suka bijiro mata a zuciya wadda yasa ta kasa barcin sai daƙyar ya sure ta daga baya. Tunda ta tashi da asuba tayi sallah ta sake komawa kasancewar akwai barcin sosai a idanun ta, bata farka ba har sai sha biyu saura domin Hajiya ta hana a taso ta har sai idan ita ce ta tashi, ta san tabbas akwai gajiya a tattare da ita. Koda ta tashi sai da tayi wanka ta shirya a cikin riga da skert na wani jan yadi me flowers da aka yi da kalan maroon color. Rigan tana da igiya ta baya wanda ta ɗaure shi, sai kuma gaban rigan a buɗe yake sai dai an saka raga-raga kalan maroon, shi kuma skert ɗin ya buɗe sosai tun daga saman ƙugun ta har ƙasa, sun mata cif sun fito mata da kyakykyawar surar jikin ta da Allah ya bata, while ta tufke gashin ta a ƙeya ta sanya ɗan kwalin kayan tayi Rolling da shi wanda ya saukar mata iya kafaɗun ta, exactly ta fito a tsantsan Balarabiyar ta. Koda ta gama shirya wa bata fita ba sai tayi zaman ta a kan gado, wayan ta dake kashe tun daren jiya ta ɗauka ta kunna, da saƙonni ta soma cin karo wanda ta fahimci Sajjad ne ya turo mata, domin kasancewar shi ya bata Simcard ɗin that’s why ya mallaki Numban, a ko yaushe yana kiran ta but tunda ta san shi ne bata sake ɗauka ba, yanzu ɗin ma bata duba ko ɗaya ba illa zare layin da tayi ta karya shi biyu ta jefar. Miƙe wa tayi ta bar wayan a wurin ta zira room slippers ɗin ta da ta ciro su daga Trolley ɗinta ta fita. Ta cikin corridorn da ta san an biyo da ita ta nan ta fita sai ga ta a tsararren parlour’n gidan

A lokacin Hajiya na zaune a Kan wheel chair ɗin ta tana karanta littafin Hisnul Muslim sanye da eyeglasses. Ganin ta yasa ta tsayar da karatun nata tana me yalwata fuskarta da murmushi tare da yiwa MEEMAN alamu da hannun ta alamun ta ƙariso gare ta

A hankali ta taka izuwa wurin ta yayinda ta ɗan saki fuskarta kaɗan. Hannun Hajiyan da ta miƙa mata ta kama tare da ɗan ranƙwafa wa kaɗan ta sumbaci hannun cikin sassanyan muryan ta da a yanzu be fita ko kaɗan ta gaishe ta

Sai da ta riƙo mata kafaɗun ta ta zaunar da ita a saman kujera kafin ta amsa ta cikin tsantsan fara’an da dole zaka gane tana a cikin farin ciki sosai, kana ta tambaye ta yanda ta kwana?

A taƙaice ta bata amsa tana kallon ta

Murya Hajiyan ta ɗaga ta kirayi Zabba’u

Babu jima wa kuwa sai ga ta ta bayyana a gaban Hajiyan, cikin washe baki ta kalli MEEMAN tace, “Barka da safiya ƴar nan”.

Kasancewar da hausa tayi bata amsa ta ba

Sai Hajiya tace, “ki riƙa mata magana da turanci ne saboda ba ta jin Hausa. Tukunna ki je ki haɗo mata Breakfast ɗin ta ki kawo mata nan sai ku gaisa daga baya”.

“To Hajiya”. Ta amsa cikin sauri tana juya wa

Ita kuma Hajiya ta kalli MEEMAN tace, “Now she’ll bring you your Breakfast. Hope you stay home?”

Guntun murmushi ta saki tana jinjina mata kai

“Calm down, ok? Whatever you are want ask me directly, insha’Allah you will never touch Zulaiha. I am always with you.”

Still kanta ta sake ɗaga mata a lokacin idanun ta suna me ciko wa da hawaye

Murmushi Hajiyan tayi mata, kana kuma ta mayar da kallon ta kan Zabba’u da ta kawo Breakfast ɗin a saman faranti. Still she keeps her eyes on MEEMA asking her, “what she wants?”

“Tea alone is enough”. Tafaɗa a hankali cikin muryan ta da har yanzu be washe ba sakamakon kukan da ta sha jiya

Saka Zabba’u tayi ta haɗa mata tea ɗin. Bayan ta gama ta amsa da kanta ta miƙa mata

Ita kuma Zabba’un zama tayi kana ta kalli MEEMAN da har ta soma kai Cup tea ɗin bakin ta, cikin turancin ta na ƴan koyo tace, “Good morning and hope you are fine? Hope you enjoyed the stay?”

Kasancewar har yanzu Cup ɗin na bakin ta, kallon Zabba’un kawai take yi tare da gyaɗa mata kai kawai ta ci gaba da shan tea ɗin

Sai ita Zabba’un ta kalli Hajiya tana muskuta zaman ta tace, “Hajiya wai yanzu ita ɗin dai yarinyan Hajiya Zulaiha ce kenan?”

“Ƙwarai kuwa. Baki ga sun yi kama bane?”

“Eh na gani wlh, ai ban yi tunanin ta kai girman haka ba, Masha Allah gaskiya tana da kyau matuƙa tamkar dai ƴar can ƙasan wlh”. Ta ƙare maganar tana washe baki

Ita dai Hajiya bata ce komi ba illa ɗaukan Hisnul Muslim ɗin dake jikin ta taci gaba da karanta wa

“Hajiya nace ba. Amma tana da aure ko?”

Ɗago wa Hajiyan tayi tana kallon ta da cewa, “ke dai Zabba’u kina da son tsegumi wlh, idan tana da aure ai zaki sani tunda tare muke da ke tsawon shekaru a gidan nan, a baya nasha sanar miki labarin su tun Zulaiha na can, sannan kuma koda ta dawo baki taɓa jin mun ce miki tayi aure ba”.

“Haka ne Hajiya. To kiyi haƙuri”.

“Idan ban yi haƙuri da ke ba ya zan yi ne Zabba’u? ki tashi dai yanzu ki je ki ɗaura mana sanwan abinci kina gani rana tayi amma kin zauna tsegumi”.

Tana washe baki tace, “Hajiya ai na ɗaura miyan har ya kusa soyuwa zan sauke, dama farar shinkafar kaɗai ya rage in girka”.

Bata ce mata komi ba ta juya ga kallon MEEMA da har yanzu tana kafe da Cup tea ɗin a bakin ta. Tace da ita, “What do you want to eat?”

Sai a lokacin ta cire Cup ɗin a lokacin ta shanye tass duk da kuwa zafin shi, domin ita ta fi son ta ji tea da zafi-zafin sa, kuma ta shanye sa a hakan ya fi mata a ko yaushe. Ce mata tayi, “She doesn’t need anything, that’s enough.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button