MEEMA FAROUK Page 21 to 30

“No, Zulaiha, tell me something to be cook for you, because you will not sit still and eat nothing but tea.”
She Said, “I will eat whatever is prepared.”
“To maza tashi ki girka ki kawo mata”. Inji Hajiyar tana kallon Zabba’un
“An gama Hajiya.” Ita kuma tafaɗa tana tashi ta wuce
Hajia Looking her said, “I am still not tired of being sorry with you for not coming to see you. Please be patient. Your uncle is not in the country that’s why he did not come to you, but forgive us.”
Hannu MEEMAN ta sanya ta riƙo nata, fuskar ta a sake sosai a yanzu ɗin tace, “Don’t worry my grandmother because you are not criminal. Ummee is a criminal and I am the only one who is angry with her. ”
Hajiya tace, “But do not be angry with her because she is your mother, bind yourself to hide what you feel about her in your heart, don’t forget she’s a mother to you, no matter what she does to you, you should not hate her.”
Girgiza kanta MEEMA ta soma yi hawayen idanun ta da suka taru suka soma zubo wa, cikin amon muryan ta me kama da ɓacin rai tace, “No, I will never forgive her for taking me not her daughter, I will never see her as my mother, I have long removed her as my mother. Please grandma I don’t like talking about her”.
“Well. Since you said I will never speak to you again.” Ta ƙare maganar da shafa mata kai tana mata murmushi.
Lokacin ne Ummee ta sauko daga sama a cikin shigan ta kamar yanda ta saba, yau ma tayi kwalliya da baƙin less me kyan gaske, duk ta saka sarƙa da awarwaro a hannayen ta, duk da a yanzu ɗin damuwa ce cinkushe a fuskar ta, ga shi idanuwan ta sun yi ja sun kumbura sosai. Koda ta iso gaishe da Hajiya tayi tana samun wuri ta zauna a kan sofan da ke kallon wanda MEEMA ke zaune
Hajiya amsa mata tayi tana kallon ta da cewa, “wai yau baza ki je aiki bane sai yanzu kika fito?”
“Eh Hajiya yau bazan iya fita ba”.
“To me ya sami idanun ki suka yi ja haka? Kar dai ace tunanin MEEMA kike yi?”
MEEMA da kanta ke sunkuye tun zuwan Ummeen sai ta ɗago kai ta kalli Hajiyan jin ta kira sunan ta, duk da bata fahimci me suke cewa ba ta gane da ita ake yi
Ita kuma Hajiya murmushi tayi mata tana dafa hannun ta, sai kuma ta mayar da kallon ta ga Ummee da ta ƙura wa MEEMAN ido, tace da ita, “tun wuri ki dena saka wa kanki damuwa tunda komi da ke faruwa ke kika jawa kanki, son zuciyar ki yasa kika aikata hakan, kin baro Ƴar ki da mijin ki kin taho nan, to, meye na saka wa rai damuwa? Abinda kike so fa kika aikata, kuma duk rarrashi da ban bakin da nayi miki domin ki koma amma kika ƙi bin shawara ta”.
“Hajiya ba haka bane wlh nayi nadama tun ba yanzu ba, abun da na aikata yana damu na a zuciya na rasa yanda zan yi in koma, ban san ya Faruk zai kalle Ni ba shiyasa na kasa koma wa, baƙin ciki na yanzu ya koma ga mahaliccin mu ban nemi afuwar sa ba Hajiya, ya zan yi da raina?”. Ta ƙare maganar cikin muryan kuka
Tsam MEEMA ta tashi zata wuce ɗaki
Hakan yasa Hajiya ta dakatar da ita tana tambayar ta, “where to go?”.
“There is something I have to do.”. Daga haka ta wuce ba tare da ta jira cewar ta ba
“Yanzu ya ya zan yi Hajiya ɗiya ta ta dawo tana ƙauna ta? Bazan iya jure halin da take ciki ba, Ina son ganin farin ciki a fuskar ta, ina son ta ɗauke Ni a matsayin mahaifiyar ta me ƙaunar ta. Nayi kuskure sosai ban san ya zan yi in dawo da farin cikin da ta rasa ba, na san MEEMA ta kasance a cikin baƙin ciki na tsawon lokaci, nayi ƙoƙarin neman ta a waya a baya but wayoyin su duk ba sa shiga.”
“To ai haƙuri zaki yi tunda ke kika jawa kanki, a sannu wata rana zata gane idan kika fahimtar da ita, Ni dai ban ce ki riƙa damun ta ba na gaya miki domin idan har ta bar gidan nan sai dai ke ma ki bi ta.”
Shiru kawai Ummee tayi yayinda hawaye ke zuba a saman fuskar ta, hannu ta sanya tana share wa zuciyar ta na mata zafi da raɗaɗi
“Ki je ki karya ga Breakfast ɗin ki can a dainning Zabba’u ta shirya miki”. Hajiyan tafaɗa tana kallon ta
Bata ce komi ba ta tashi ta wuce kan dainning ɗin.
******
Shigan MEEMA ɗakin kwanciya tayi a saman gadon tana hawaye, danne kanta tayi a ƙasan pilow ta saki kuka me tsuma rai, ta jima tana kukan kafin ta tsagaita tana tashi zaune ta sanya hannayen ta tana share hawayen. Sai ta miƙe ta nufi jakar ta ta ciro computern ta ta soma aiki a ciki
Bata jima da fara wa ba Zabba’u ta shigo ɗakin da sallama
A ciki-ciki ta amsa mata bayan ta ɗago ta kalle ta sau ɗaya ta mayar da kanta
Cikin washe baki Zabba’u tace,
“good job. Hajiya says let me call you cooking is complete.”
Gyaɗa kanta tayi ba tare da ta furta komi ba ta mayar da hankalin ta ga computern
Ita kuma Zabba’u ta fice
Kamar mintuna goma kafin ta rufe ta tashi ta fita.
*WhatsApp only*
07065334256
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_20*
Tafiyan MEEMA ya ja tashin hankali matsananciya a wajen su Uncle Ali. Musamman ma Sajjad domin hauka tuburan ya nuna musu a kan, “sai sun nemo mishi ita duk inda ta shiga.” Kuka sosai yake yi duk ya hargitsa musu gida, su kansu sun kasa zama suyi tunanin mafita illa rarrashin sa da suke yi a kan, “ya kwantar da hankalin sa zasu nemo ta duk inda ta shiga.”
Mutanen da suka soma taruwa sai dai suka tafi a washe garin ranan tunda an nemi Amarya an rasa. Wasu har tsegumi suke yi da dalilin tafiyan nata
Su kuma tun suna ɗaukan abin da Sajjad yake yi a matsayin na ɗan lokaci dole zai haƙura; sai kawai zazzaɓi ya kama sa, sosai yake jin jiki wanda a koda yaushe sai dai yayi ta musu sambatu, “shi fa a nemo masa Zulaiha, bazai iya rayuwa babu ita ba.” Hakan yasa suka wuce da shi asibiti tunda abun nasa sai gaba yake yi.
Uncle Ali da Uncle Zubairu sun rasa inda za su fara zuwa su neme ta, hankalin su a matuƙar tashe yake sabida rashin amsar komi daga wurin ta, tabbas suna tunanin ta gane auren da zasu yi mata ne ta gudu, kuma ko kusa basu yi tunanin zata iya zuwa wajen Ummeen ta ba kasancewar ita Ummee ta bar su tun ba yanzu ba, ba sa tunanin cikin sauƙi zata je can. Shiyasa suka yanke shawarar zuwa Riyadh ɗin su duba ta
Umma duk ta tashi hankalin ta itama sai kuka take yi, a yanda ta ga Sajjad ya ƙi haƙura da zancen MEEMAN yasa itama take kuka da faɗin, “a nemo ta duk inda ta shiga don ɗan ta bazai mutu a kanta ba, a nemo ta a ɗaura mishi aure da ita idan har ɗan ta zai samu lafiya.”
Uncle Zubairu shi ya je har Riyadh ɗin amma masu aikin gidan suka ce, “bata zo ba”. Kwanan sa biyu a can yana zaman jiran ko zata zo amma babu ita babu alamar ta, dole ya dawo gida ya sanar wa da Uncle Ali. Hankalin su ya sake tashi sosai, sai dai babu yanda suka iya dole suka mayar da hankali wajen samun lafiyan Sajjad tunda har yanzu ya ƙi dangana shi a dole sai an nemo ta. Har ya samu sauƙi sun koma gida ya tayar da hankalin sa, “shi da kansa zai je neman ta a Riyadh ɗin.” Ba don sun so ba suka bar sa ya soma shirye-shiryen tafiya. A ransa ya ƙudura aniyar, “muddin be ganta ba bazai dawo gidan ba, dole tare za su dawo, a ko ina take a faɗin duniyar nan sai ya nemo ta, ba shi da matar aure sama da ita, yana matuƙar ƙaunar ta bazai taɓa barin ta ba”.