Uncategorized

MEEMA FAROUK Page 21 to 30

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

            Zaman da MEEMA tayi a gidan ta samu kwanciyar hankali sosai, duk abin da take so Hajiya tana mata, tare suke zama suyi ta hira har da Zabba’u don yanzu ta saba da ita kasancewar ta akwai surutu da shiga abun da babu ruwan ta, yanda take shige wa MEEMAN ne dole ta saki jiki da ita, sai dai matsalan ko kaɗan ta ƙi bai wa Ummee dama wajen ganin ta wanke kanta daga laifukan da tayi mata, ko magana ba ta mata koda suna zaune wuri ɗaya, tun Ummee na damuwa sosai a yanzu har ta saba da halin MEEMAN, itama a hankali yanzu take ɗan shiga sha’anin ta duk da ba kula ta take yi ba, amma wani abun sai ta riƙa mata ko don ta faranta mata, musamman girkin da ta san tana matuƙar so irin ciman Larabawa, haka zata zaƙe tayi mata but ko kula wa ba tayi, Hajiya ke sanya ta taci wani lokacin shiyasa take ɗan ci idan ta ga dama. 

           Yau ma suna zaune da Hajiyan, Zabba’u na gefe tana musu surutu Hajiya na amsa ta, ita kuma MEEMAN tana zaune tana kallon su wani lokacin idan suka sako ta a zancen su tana tsulma musu baki

Dayake Ummee na wajen aikinta bata dawo ba

Duban Zabba’u Hajiya tayi da cewa, “yauwa Zabba’u kira min drever zan aike sa, zai siyo wa MEEMA layin waya ne ta ce min  tana buƙata.”

“To Hajiya bari in je.” Tayi maganar tana tashi da sauri ta fita

MEEMA da ke kallon su sai tace, “grandma I also want to learn Hausa because I want to know what you are saying”.

Dariya Hajiya tayi da cewa, “Are you tired of hearing us talk? Don’t you understand?”

Ita kuma sai tayi murmushi tana jinjina mata kai, sai kuma ta ƙara da cewa, “yet I want to be able to.”

“Ai kuwa zaki koya, da sannu ai zaki saba dama”.

“You say what?”

Hajiya smiled and said, “I said you will learn slowly.”

MEEMA smiled at her looking at her

“But I think your stay there makes you very anxious. what i was thinking why not get a job you going out, It will help you a lot and you will forget about any worries.”

“Na’am grandma. I need a job, I want to start working.” She spoke excitedly

Hajiya itama murmushi tayi da cewa, “If that makes you happy, you will be offered a job”.

               Zabba’u da Ummee ne suka shigo a tare

Hajiya ta amsa musu sallaman tana kallon su

“Sannu da gida Hajiya.” Inji Ummeen tana zama a kan sofa

“Yauwa an dawo?”

“Eh.”

Zabba’u da itama ta zauna take faɗin, “Hajiya wai ya fita zuwa shago yanzu zai dawo, na bar wa me gadi sallahu idan ya dawo ya faɗa masa kina neman sa.”

“Tom shikenan.” Cewar Hajiyan kafin ta mayar da kallon ta kan Ummee dake yunƙurin tashi tace, “zauna zamu yi magana”.

Koma wa tayi ta zauna tana kallon ta

“MEEMA tace tana son Fara aiki kinga ke ya kamata ki nema mata abun da ya kamata tayi”.

“To Hajiya sai in nema mata a wurin aikin mu hakan zai fi mu riƙa zuwa tare.” Inji Ummeen tana kallon MEEMA da murmushi

Hajiyan kallon MEEMA tayi tana sanar mata da abun da Ummee tace

Fuskar ta babu walwala ta dubi Hajiyan tace, “Laá. I do not like.”

They were silent

Sai kuma Hajiyan tace, “But you said you needed it, or did you break it?”

Kafin tayi magana sai Ummee tace, “a’a Hajiya ina ga ba ta son yi a inda nake yi ne, kuma dama mass.com ta karanta Ni ce dai nake son tayi aiki a companin da nake aiki hakan zai sa ko yaushe muna tare, amma tunda ba ta so sai in Yi ma Idris magana ya samo mata a wajen aikin su na gidan t.v hakan zai fi.”

Hannun MEEMAN Hajiya ta riƙe tana kallon ta tace, “well. Now you’re going to get a job somewhere, did you?”

Kanta kawai ta ɗaga har yanzu kyakykyawar fuskar ta a turɓune

Ita kuma Ummee tashi tayi ta haura sama

While su kuma suka ci gaba da taɓa hira ban da MEEMA da ke latse-latse a cikin wayan ta

Nocking ɗin da aka yi ne yasa suka yi shiru suna ba da iznin shigo wa

Drever ne ya shigo da sallama a bakin sa, ya isa wajen su ya durƙusa yana cewa, “Hajiya gani an ce kina nema na”.

“Eh Salihi. Layin waya zaka siyo wa Jika ta.”

“To Hajiya”.

“Yauwa Zabba’u ɗauko mishi 2k a ɗaki na ya je da shi.”

Amsa mata tayi tana tashi ta wuce

Drever’n yace, “amma Hajiya wani iri ne zan siyo?”

Kallon MEEMA tayi da cewa, “What brand do you want with the Simcard?”

Sai a lokacin ta ɗago da idanun ta daga duba wayan da take yi, “MTN.” Ta furta a taƙaice

“To kaji. Mtn take so ka siyo mata.”

“To Hajiya.”

Koda Zabba’u ta kawo kuɗin ta miƙa masa ya fice. Ita kuma tace, “Hajiya bari in shiga kichen in ɗaura mana abinci. Ko zaki taya Ni ne MEEMA?” Ta ƙare maganar da kallon ta tana washe baki

Jin ta kira sunan ta yasa MEEMAN ta kalle ta ba tare da ta furta komi ba

Hajiya tace, “kin yi mata Hausa taya zata san me kika faɗa mata?”

“Oh wlh manta wa nake yi Hajiya.” Sai ta maimaita mata da turancin

Girgiza kanta MEEMA tayi tace, “laá I can’t.”

“But you should always learn that it will benefit you even at your husband’s house.”

Murmushi kaɗai MEEMA tayi bata ce komi ba ta mayar da hankalin ta kan wayan ta

Ita kuma Zabba’un sai da ta gama zuba surutun ta da Hajiya duk dai a kan MEEMAN kafin ta wuce kichen ɗin

Hajiya ta kaɗa kai da cewa, “Zabba’u baki da dama ke dai, a nan kika fi auki wajen surutu, ayi mutum kullum ba ya gajiya kin girma baki san kin girma ba.”

Ɗago kai MEEMA tayi ta kalle ta tace, “grandma you do it for me?”

Tace, “No, I’m not doing it. I’m doing Zabba’u. She’s worried about you coming. She’s going to teach you how to cook.”

“I can’t grandma.” She spoke in a calm voice

“Then if you want she can teach you, because you should learn. If you get married who will go and teach you?”

Shiru MEEMA tayi and she drops head down

“If you have time, she will teach you ok?”

Gyaɗa kanta tayi kawai. Sai kuma ta miƙe tana kallon Hajiyan da cewa, “I’ll go into the room and lie down.”

Hajiya amsa mata tayi ita kuma ta wuce zuwa ɗaki.

        Tafiyan ta babu jima wa wani saurayi wanda bazai fi sa’ar MEEMAN ba ya shigo da sallama ciki

Hajiya ta amsa mishi tana masa lale da faɗin, “idon ka kenan Idrisu?”

Dariya yake yi ya ƙariso ya zauna yana cewa, “Allah ya bar mu da Hajiyar mu. Kin ci zamanin ki kina cin tamu, tsohuwa me ran ƙarfe an buga an bar ki, na same ki lafiya?.”

“Ai bazan amsa ba tunda sai yanzu ka san da Ni, gaba ɗaya ka manta da Ni sai yau zan ga ƙafafuwan ka a gida na.”

“Woo! Hajiya kina da ƙorafi ne na rantse da Allah, ban da abun ki duka-duka yaushe ne na ɗauke ƙafafu na a gidan nan? Kin san kuma aiki na ne ba ya bari na in shigo amma da sai kin gaji da gani na.” Yafaɗa still yana dariya

Hajiya tace, “babu wani nan, da ace ban san daɗin bakin ka bane.”

“Tukunna dai Hajiya inyaso daga baya sai mu ci gaba da taƙaddamar tamu, ina Aunty ita take nema na?.”

“To ka ji batu ashe sai da aka neme ka ka shigo?”

Dariya yayi da cewa, “Hajiya tawa ke dai so kike yi ki laƙaba min laifi, kowa ya san ina mugun ƙaunar ki, ko su Umma sun san cewa ina na fito wurin ki ne, ina zan tafi wurin ki ne, amma kike faɗan haka; idan wani ya ji ai sai yayi mana dariya Allah kuwa.”

“Ni zan fara yin dariyan kuwa. Dama ai ba yau kuka saba ba, sunan dai kuna miji da mata ne.” Cewar Zabba’u da fitowar ta kenan daga kichen ta tsinkayi maganar nasa

“To kin gani ko Hajiya ta? Ai dama nace miki akwai ƴan saka eyes wlh, kin ga ɗaya ta ɓullo. Bamu san kuma nawa za su ƙaru ba a nan gaba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button