MEEMA FAROUK Page 21 to 30

Dariya suke yi su duka
While Zabba’u tana faɗin, “ai yau har gidan su Umman taku sai na je kai gulman ku.”
“Kin gani ko Hajiya? To ki faɗa mata ba faɗa muka yi ba.”
“Ƙyale ta Idrisu na, duk wanda yace zai gan mu a rana ai zai ruɓe ne, Ni da miji na ai ba ma ɓaci. Yanzu dai kira Zulaihan a waya tana sama ne.”
Wayan sa ya ɗauka yana latsa wa yana ci gaba da bai wa Zabba’u amsa wacce ta sako shi a gaba sai ba’a take mishi. Bayan ta ɗau wayan ne ya sanar mata, “ya zo.”
Ba’a jima ba kuwa sai ga ta ta sauko. Ta zauna a kan sofan tana amsa gaisuwar sa, kana ta ƙara da faɗin, “Idris aiki zaka samo wa yarinya ta MEEMA a wajen aikin ku, Ina fata za’a samu?”
“Eh Aunty za’a iya samu insha Allahu, idan ma hakan ya gagara zan yi ƙoƙari ko a ina ne in samo mata, amma Aunty Kar dai ace yarinyan ki ta Riyadh ita ce ta zo?”
“Eh ita ce.” Ta ba shi amsa tana murmushi
“Wow! Gaskiya zan so in ganta, kin san na daɗe da jin labarin ta wajen Hajiya sai dai baki taɓa zuwa da ita nan ba.”
“To ai yanzu sai ka gaji da ganin ta kuwa Mijin, tunda muna nan da ita ta dawo gaba ɗaya.” Cewar Hajiya tana dariya
“Allah Hajiya ta?”
“Ƙwarai kuwa Mijin. Yanzun nan ma ta tashi ta shiga ɗaki.”
“To in dai haka ne insha Allahu I will try my best to get her a job. But I need her documents so I can go with them.”
Ummee da sauri ta kalli Zabba’u tace, “ki kira ta sai ki faɗa mata ta kawo takardun nata.”
Tashi Zabba’un tayi ta wuce ɗakin MEEMA. Bata jima ba ta dawo ta sanar musu, “ga ta nan zuwa”.
Ba’a jima ba MEEMA ta fito riƙe da documents ɗin a hannun ta ta taka a hankali zuwa wurin su
Hajiya na murmusa wa tace, “to ka ganta nan Idris, Jika ta kenan.”
Idris da ke faman kallon MEEMAN miƙe wa tsaye yayi fuskar sa yalwace da fara’a yace, “gaskiya tana da kyau Hajiya, Allah ya baki jika kyakykyawa. Anya Hajiya ba daga can ƙasar kika sanyo ta da naki ba?” Sai kuma ya kama haɓa yana sake ƙare wa MEEMAN kallo da cewa, “Hajiya Ni fa ban yarda ba, kwata-kwata ban ga tayi kama da ke bane ai.”
Dariya suke yi duk kan su sabida abin da ya faɗa
While Hajiya tace, “ai yaro duk kyawun nan da ka gani kaɗan ne da wanda nayi a zamanin da nayi ƴan matanci na, wannan ai bata kai Ni kyau ba.”
“Nima haka na gani ki bar sa kawai Hajiya don ya ga kin taƙwarƙwashe ne shiyasa yake faɗan haka.” Inji Zabba’u tana dariya
They all laughed. while MEEMA na tsaye tana kallon su bata ce uffan ba tunda ba jin su take yi ba
Idris yace, “ƴar uwan tawa ba ta magana ne Hajiya naga tayi shiru ko fara’a ba ta yi?”
Zabba’u tayi tsagal ɗin cewa, “ba ta jin ka ne shiyasa, baka yi mata da Yaren da zata gane bane.”
“Kina nufin larabci?” Yafaɗa yana ƙwalalo ido. “To ai Ni ban iya ba.”
Ummee tace, “kayi mata da turanci.”
Murmushi yayi ya kalli MEEMAN da cewa, “sorry sister. My name is Idris. Our house is looking at this house, we are staying outside Hajiya, I am happy to meet you.”
Guntun murmushi tayi masa da cewa, “me too.”
“Ok Bring the documents.” Yafaɗa yana miƙa mata hannu
Handing him the fetus without saying anything again she turned and walked away
Hajiya tace, “to sai ka ƙoƙarta Idrisu na.”
“Kar ki damu Hajiya ta baki da matsala. Ni zan tafi don akwai inda Abba ya aike Ni dama. Zuwa gobe ko jibi zaku ji me ke akwai in Allah ya yarda.”
Daga nan sallama suka yi ya fice ya bar su. Su kuma suka ci gaba da ɗan taɓa hira, inda Zabba’u ta wuce kichen domin ci gaba da aikin ta.
Ba’a rufa kwana biyu ba Idris ya dawo gidan ya shaida musu, “an dace da samun aikin MEEMA”.
Zuwa Monday suka soma fita aikin tunda a wurin aikin su ta samu, tare suke fita da Idris kasancewar sa me son Wasa da barkwanci a cikin ƙanƙanin lokaci suka soma saba wa, idan ya shirya sai ya zo gidan su tafi tare
Tunda ta fara fita aikin ta sake sakin jiki sosai, abubuwan da ta gani a wurin aikin nasu da kuma yanda ake gudanar da al’amura gunun sha’awa a wurin ta. Musamman yanda mutane suke son mu’amala da ita domin sosai tayi farin jini a wurin jama’a, kowa MEEMA kowa MEEMA sai hakan yake sanya ta farin ciki da nishaɗi, duk da ba kowa take kula wa ba iyakan gaisuwa sai kuma abun da ya kaita tunda ko yaushe suna tare da Idris, ga kuma cousin ɗin shi Laɗifa komi tare suke yi, ita take jan MEEMA a jiki tana koya mata wasu abubuwan musamman idan bata fahimta ba kasancewar yanayin mu’amalar mu ta nan bata san da su ba, ga kuma rashin iya Hausa da har yanzu ko Eh ta gaza fahimta.
Musamman Ummee ta siyo mata mota sabuwa fil domin ta riƙa zirga-zirga da ita na yau da kullum zuwa wajen aiki, amma ta ƙi amsa
Hajiya da kanta ta kira ta, ta miƙa mata keey ɗin motan daƙyar ta amsa. Sai dai bata taɓa hawa ba kullum Idris take bi tunda sun zama tamkar friends ne a cikin ɗan ƙanƙanin lokacin da be gaza wata ɗaya da haɗuwar su ba. Wani lokacin ma har gidan su take shiga wajen Umman sa, kasancewar gidan akwai yara shiyasa zaman gidan yake mata daɗi, kowa so yake yi ya ja ta a jiki saboda farin jinin ta. Shiyasa a ɗan ƙanƙanin lokaci ta saki jikin ta ta soma saba wa da sabon rayuwar ta, a hankali ta soma manta duk wani rayuwar ƙunci da tayi na tsawon shekaru, duk da har yanzu ta kasa manta wa da Abee ɗin ta duk idan ta tuna sa tana zubar da hawaye sosai, sai ta riƙa jin tsanar Ummeen ta yana sake zama sabo a zuciyar ta, tana jin tamkar baza ta taɓa yafe mata ba. Ita ce silan komai.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*FAƊAKARWA*
“`Manzon Allah yayi mana bayani cewa, “Bambancin da yake tsakanin mumini da kafiri shi ne rashin yin Sallah.” Busaida ya ruwaito wani hadisin mai kama da wannan inda ya ce, “na ji Manzon Allah yana cewa,” “haƙƙin da ya bambanta mu da su shi ne salla. Duk wanda yayi watsi da ita ya zama kafiri.”
Shi kuwa Abdullahi Ibnu Umar ya ce ne wata rana Annabi yayi magana a kan Sallah yace, “Ga wanda yake tsayar da sallah, takan zame masa haske, shaida da kuma tsira a ranar lahira. Wanda ba ya tsayar da ita kuwa, gare shi babu haske, babu shaida, babu tsira, kuma a ranar lahira za a haɗa shi da Ƙaruna da Fir’auna da Ubayyu ibnu Khalaf.”
Da hadisai da ayoyin Alkur’ani duka suna nuna irin munin zunubin da yake rataya da ƙin yin salla, suna kuma nuna matsayin mai yin hakan duniya da lahira. Dokar musulunci dai tana yin gargaɗi ne ga mabiya addinin cewa su riƙe shi da gaskiya ta yin Sallah, babban jigon Islama kuma aikin addini mafi girman daraja. Ashe ba abin mamaki ne ba mu ji cewa duk wanda ya guje mata ya kafirta, ya kauce ma hanya miƙaƙƙiya. Alƙur’ani kam na kiran irin wannan mutum mai zunubi wanda aka tanadar wa wutar jahannama, mai ƙona komai, mai cinye Mutane da tsananin zafin ta. Kyakykyawan sakamako ga wanda ya bijire. Ubangiji ba ya zaluntar kowa. Allah yasa mu dace yasa mu gama da duniya lafiya.“`