MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 61 to 70

Ita kuma ta tashi ta kawo mishi ruwa ta zuba masa a glass Cup

Sai kallon ta yake yi a zuciyar sa yana tunanin yanda zata ji idan ya sanar mata zancen ƙara auren sa, shiyasa ya yanke shawaran barin zancen gwara Momy ta sanar mata domin bazai iya ganin damuwa a kan fuskar ta ba. Da ya sha ruwan ɗaukan hulan sa yayi yana miƙe wa tare da cewa, “muje ki haɗa min ruwan ka.”

“To.” Ta amsa mishi tana bin bayan sa har zuwa ɗakin sa. Ta shiga Toilet ɗin domin haɗa masa ruwan

Shi kuma ya zauna a gefen gado ya ajiye hulan yana zare agogon hannun sa, bayan ya gama ya miƙe ya soma ƙoƙarin cire rigan nasa. Sanda ya gama daga shi sai Singlet da dogon wandon jikin sa

A lokacin ne Luwaira ta fito daga Toilet ɗin ta gama haɗa masa ruwan. Zuwa tayi wajen sa tana kallon sa da cewa, “ranka ya daɗe ko zan taimaka maka?”

Murmushi yayi mata yana ɗan hura iska daga bakin sa, sai ya ɗan gyaɗa mata kai tare da kama hannun ta ɗaya da cewa, “kin dai ƙi sauya min sunan nan ko? Ba na son kina ce min ranka ya daɗe ɗin nan saboda ina jin wani iri. Ki samo suna me daɗi na soyayya ki riƙa faɗa min zan fi jin daɗin hakan.”

Murmushi tayi tana ɗan ɗauke idanun ta daga kallon cikin nasa idanun, domin ba ta son kallon cikin idanun nasa saboda yanda suke da matuƙar kwarjini da tada hankalin duk wani me ji da kanshi gami da ƙara saka Mutum shauƙi da tsananin begen shi. Hannun ta ta kai jikin sa tana shirin ɗaga Singlet ɗin nasa da cewa, “to na maida maka Yayana, hakan yayi?”

Shima hannun yasa yana taimaka mata da cewa, “no ban yarda ba, sunan baya ne ba na so, ki sake wani.” Yayi maganar a hankali a cikin wani irin yanayi idanun sa na yawo a kan fuskar ta

Bata kalle sa ba duk da ta san itan yake kallo, sai da ta gama cire masa Singlet ɗin tare da ɗaura sa a dantsen hannun ta tana shirin juyawa tace, “to zan canza maka, amma kafin nan ka shiga wankan idan ka fito sai in faɗa maka time ɗin nayi tunani nima.”

Hannun ta ya kamo ya dawo da ita gaban shi, yanda ya narke fuska kamar zai haɗiye ta don kallo ya matso da ita sosai ta yanda ta jingina da jikin sa, kana ya mayar da hannun sa ɗaya a ƙugunta yace, “tare zamu shiga, ke zaki yi min wankan ma.”

Waro ido tayi tana kallon sa a yanzu ɗin, sai dai bata yi magana ba illa murmushi me cike da kunya da ta saki

“Oya muje kiyi min wankan”. Ya sake rungumo ta a jikin sa ta yanda gaba ɗayan ta ta gama manne masa

Bata iya masa musu ba illa bin sa da tayi ganin ya nufi hanyar Toilet ɗin.

               Sai da suka yi wankan tare kafin suka fito. Be bar ta ta fice ba sai da ta shirya sa tayi masa komi, a lokacin wayan sa ta fara Ring, sai ya kalle ta yana faman taje suman kanshi yace, “miƙo min waya ta”.

Ajiye lotion ɗin dake hannun ta tana ƙoƙarin mutstsika masa a kai tayi, sai ta wuce gaban gadon tana sake gyara towul ɗin da ke ɗaure a jikin ta daga saman ƙirjin ta zuwa ƙasan gwiwowin ta, ɗaukan wayan tayi nan idanun ta suka faɗa kan sunan da ke kan screen ɗin wayan, inda taga an rubuta Heartbeat ɓaro-ɓaro, take a nan kuwa zuciyar ta tayi wani irin sarawa wanda ƙiris ya rage ta yar da wayan, sai kuma ta sake tallabowa tana jin komi na jikin ta ya dena aiki, can kuma sai ta soma rawan hannu sai dai bata yi wata-wata ba ta juya ta nufi inda yake da wayan ta miƙa masa jikin ta a matuƙar sanyaye, yayinda zuciyar ta ke luguden bugawa tana son hana bayyanuwar firgita gami da halin da take ciki

Shi kuwa da ya juya amsar wayan, yana amsa ya kalli screen ɗin wayan, ganin wacce ke kiran ne yasa ya mayar da idanun sa kan Luwaira, sai dai ta kasa bari su haɗa idanu amma hakan be sa ya kasa fahimtar a halin da take ciki ba, barin ma yanda ya ga fuskarta ta nuna, hakan yasa ya dakata daga ɗaukan wayan yayinda wayan ma ta tsinke a time ɗin. Sai wata kiran ta sake shigowa, kallon Luwairan yayi kamar zai yi magana, sai kuma ya tashi a wurin ya nufi gaban gadon sa, sai da ya zauna ya kalle ta daga inda take tsaye ko motsin kirki ta gaza yi kuma ta ƙi kallon sa, “ki je ki shirya na hutashshe ki.” Yayi maganar a cikin matuƙar sanyin muryan sa me daɗi

Ɗago kai tayi ta kalle shi zuciyar ta na ƙuna, sai dai a dole tayi ƙoƙarin danne abun da take ji illa gyaɗa masa kai da tayi ta juya ta fice

      

Sai da ya ga ta datse ƙofan kafin ya saki numfashi da ƙarfi yana yin peacking call ɗin.

                Ita kuma kanta tsaye ɗakinta ta ruga aguje tana sakin kuka, bata tsaya a ko ina ba sai a kan gadonta ta faɗa tana ci gaba da kukan sosai, zuciyarta ne ke tafarfasa sabida tuna sunan da ta gani, “to wace ce?” Tambayar da ke kai kawo a ranta kenan wadda ya hana ta sukuni yayinda kishi ke ƙara nunkuwa a zuciyarta. Babu shakka yarinyar da yake so ce ita ce har yanzu take bibiyan rayuwar sa, har yanzu suna tare basu rabu ba wanda ta ɗauka a tunanin ta sun daɗe da rabuwa ne, idan kuwa haka ne bata san inda zata saka ranta ba, muddin aka yi auren nan baza ta iya jurewa ba saboda tsantsan kishin da take ji a ranta, zata iya haukacewa, ada soyayyar da take mishi be kai yanda take ji a yanzu ba, zata iya yin komi domin ta raba shi da koma waye ne, baza ta iya barin shi ya auri Wata ba, hakan na nufin zata ci baya idan har ya auri wacce yake ƙauna? Ita kenan ba ƙaunarta yake yi ba har yanzu? kawai taimakon ta yayi. Yanda zuciyarta take kawo mata wannan hasashen ji take yi kamar zata mutu, har wani kama maƙogwaron ta take yi sabida zafin da take ji. Take kuma ta tashi tana share hawayen nata yayinda wasu suke gudun tseren fitowa daga cikin idanun, inda suka kaɗa suka yi jazur har wani kumbura suka soma yi, “Heartbeat.” Tafaɗa a maƙoshi tana jin kamar zata mutu, majina ta ja tana wurga idanunta a cikin ɗakin domin neman wayan ta, can ta hango shi a gaban dressing mirror ɗin ta sai ta tashi da azama ta ɗauko ta dawo ta zauna, wayan ta soma latsawa tana neman Numban Abida, baza ta iya jurewa ba gwara ta kira ta ta sanar mata a halin da take ciki, hakan shi ne kawai maslaha da abinda take ji, ta san ita zata bata shawarar abun da ya dace tayi, domin baza ta taɓa bari Wata ta shigo mata gida ba, Umar Faruk nata ne ita kaɗan ta, babu Wata mahalukiyar da ta isa ta mallake shi bayan ita, baza ta bar hakan ta kasance ba har abada.

_Enjoy your weekend FAN’S._

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button