MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 61 to 70

Kai tsaye shi kuma supper market ya wuce ya yo wa MEEMA siyayyan kayan dubiya abubuwa da yawa, har waya sai da ya siyo mata don dai kawai ya faranta mata. Yana son su riƙa kasancewa a koda yaushe shiyasa ya ga ya dace shi ya fara mallaka mata wayan ko don hakan zai rage masa wahalan kasancewar su tare.

          ✳️✳️✳️✳️✳️

         MEEMA na zaune a ɗaki a lokacin sai ga Zabba’u ta zo kiran ta Umar Farouk na jiran ta. Jim tayi tana kallon ta bata amsa ta ba. Bata san kuma me zai ce mata ba, tunda yanzu yayi auren sa me zai nema a wajen ta? Mene ne dalilin zuwan sa wajen ta? Idan ma sabida soyayyar da yake mata ne ba ta jin zata iya zama da shi da wata, taya ma zata iya zama da kishiya alhalin ta tsani kishiya? baza ta iya ba sam, duk da zuciyar ta ba ta mata daɗi tana cikin ƙunci da jin zancen auren sa, amma ta ji daɗi da bata amince masa da soyayyar sa ba, ko ba komi bata amince ba bare yayi tunanin tana son sa ne, dole kuma zata faɗa mishi gaskiyar abin da ke ranta domin baza ta iya jure sintirin shi a wajen ta ba, zuciyar ta zata iya bugawa idan ta ci gaba da damuwa da shi. That’s why ta tashi ta fito daga ɗakin tayi Parlour, daga ita sai doguwar rigan atamfa me ruwan ƙwai, sai aka yi design ɗin sa da ja da fari, hakan yasa ya sake haska ta sosai kayan, ɗinkin yayi mata kyau sosai tunda akwai kwalliya da aka yi a gaban rigan da ƙyallen atamfar, sai gashin kanta da ta tufke a tsakiya ta ɗaura baƙin siririn gyale a kan ba tare da ta ɗaura ba

Daga shi sai yaran sa ne a parlour’n tunda duk sun gaisa da su Hajiya sun wuce ɗaki. Fitowar ta yasa suka haɗa idanu wanda ya bi ta da kallo kamar wacce yau ne ya soma ganin ta, be taɓa ganin ta da kayan hausawa ba sai yau shiyasa ba ƙaramin mugun kyau tayi masa ba, ji yake yi tamkar yau ya saba ganin ta, yayinda yake jin ƙaunar ta da begen ta na ƙara huda can cikin zuciyar sa

Ita kuwa tuni ta kawar da nata idanun daga kallon sa ta samu waje a ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna. Sosai take jin kaifafan idanun sa a kanta suna yawo wanda suke sake sagar mata da jiki tare da ƙara mata bugawar zuciya da rashin natsuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar kallon sa sabida yanda yake mata kwarjini shiyasa a yanzu ɗin ma bata sake ɗago kai ba bare ta kalle sa

Shi kuma yayi shiru ya kasa cewa komi. Sai kuma daga baya ya kalli yaran nasa waɗanda su ma sun mayar da hankali wajen MEEMA suna ta kallon ta kamar sun samu t.v. ce musu yayi, “su gaishe ta.”

Hakan yasa suka haɗa baki wajen furta, “ina wuni.”

Ita kuma a sa’ilin ne ta ɗaga kai tayi duba gare su. Guntun murmushi ta saki tare da amsa su da, “lafiya.” A cikin gurɓataccen Hausan ta, kasancewar yanzu zaman ta a cikin hausawan yasa ta soma iya guntayen words waɗanda basu da wahala kuma tana fahimtar su. Miƙa hannun ta tayi kuma alamun, “su zo wajen ta.”

Hakan yasa Yusra ta taso da sauri ta isa wajen ta

Hafsah kuwa ƙin zuwa tayi. Sai da shi yace mata da kanshi, “ta je.” Sannan ne ta nufe ta

Hannayen su ta riƙe yayinda har yanzu bata gusar da murmushin da ke fuskar ta ba ta soma tambayar su, “ya suke?” Da school ɗin su

Yusra ce kaɗai take amsa mata while Hafsah tuni ta samu waje ta zauna abun ta tana wani ɗaɗɗaure fuska. Dama ita ba ƙaunar Mutane take yi ba musamman waɗanda taga suna mu’amala da mahaifin ta, Yusra ce kawai idan ta je waje take iya sakin jikin ta tamkar ta sanka

Hakan yasa MEEMAN ta ɗauke ta ta azata a jikin ta

Yanda Umar Faruk ya ga ta nuna wa yaran sa kulawa sai ya saka shi farin ciki tsantsa, domin shi Mutum ne me son ya ga ana ƙaunar yaran sa. Sai kallon su yake yi da murmushi a face ɗin sa

Ita ce da ta ji shirun nasa yayi yawa sai tayi ƙarfin halin ɗago kai tana kallon sa, a hankali ta furta, “What are you going to do in my place?”

Shiru ya ɗan yi shima yana kallon ta, kana kuma ya buɗe baki yace, “I came to greet you in your body. I hope you are well?”

“Na’am.” Tafaɗa a takaice tana ɗauke kai

Hakan yasa suka sake yin shiru gaba ɗayan su

Can kuma da ya gaji don kansa ya buɗe baki yace, “I brought the phone to you so we can greet each other.” Sai ya kira sunan Yusra yace mata, “ta zo ta miƙa mata.”

Tasowa tayi da gudun ta ta amsa ta kai mata

Ba da son ranta ba sai don ganin idon yaran yasa ta amshi wayan tare da ce mishi, “shukran.”

Murmushi yayi kawai yana kallon ta. Ya rasa abun cewa dole yayi shiru, sauran kayan ma da ya zo dasu su Ummee ya ba. Wai, “na dubiya,” wayan ce kawai yayi ninyan miƙa mata da kansa

Ita MEEMA ta gaji da zaman su a haka shiyasa ta tashi tace mishi, “She’ll go inside.” Da haka ta shige abun ta ba tare da ta jira cewar sa ko wayan bata ɗauka ba, domin haushin kanta take ji a yanda ta kasa buɗe baki tayi masa magana, takan rasa meyasaka ba ta ƙaunar yin magana a gaban shi koda kuwa tana son furta wani abu a cikin ranta?

Shi kuwa kwata-kwata ransa babu daɗi da yanda ta nuna masa, musamman ƙin ɗaukar wayan da tayi ta wuce da shi hakan ke nuni da cewa bata yi farin ciki ba. Ɓoye damuwarsa kawai yayi ya saka Hafsah ta je ta faɗa wa mutanen gidan, “za su tafi”. Bayan yayi musu sallama suka fice tare da niƙi-niƙin kaya da su ma su Hafsan suka samu daga wajen su Hajiya da Ummee.

              Kai tsaye suna zuwa gida ɗakin sa ya shige ya bar su a falon ƙasa. A kan gado ya zube komi be iya cirewa ba illa takalman kafafun sa, lumshe idanun sa yayi yana mayar da ajiyan zuciya. Ya jima a haka kafin ya tashi tsaye jiki a mace ya wuce Toilet don ɗauro alwalan sallan asar.

             Luwaira sai da ta tambayi yaran inda suka je

Da sauri Hafsah ta faɗa mata, “ai wajen budurwan Dady suka je wai ya je duba lafiyan ta.” Ta ƙare maganar tana tura baki gaba

Yayinda Yusra kuma cikin murna tace, “Aunty wlh ga ta kyakykyawa, Dady ma yace mu ce mata Aunty, kuma ƴan gidan su ne suka bamu Waɗannan kayan.”

Yanda maganar nasu ta bigi zuciyar Luwaira hakan yasa ta kasa cewa komi illa kallon su da take yi. Kenan dai wajen yarinyar da yake so ɗin ya je? Har yanzu be rabu da ita ba? Wani irin ƙunci ne ya tabaibaye mata zuciya, tsam ta tashi zata wuce ɗaki ba tare da ta sake bi ta kansu ba

A lokacin ne Umar Faruk ya sauko daga saman yana saukar da hannayen rigan sa da ya naɗe wajen alwala, fuskar sa duk ruwa har saka hannu yayi ya sake sharce wa, idanun sa a kan Luwaira wacce ta tsaya ta kasa shigewa ɗaki tana sunkuyar da kanta ƙasa, sai da ya sauka Steps ɗin kafin yace, “ki tasa yaran nan mana kiyi musu alwala suyi Sallah, and ki dafa min ruwan lipton ina buƙata ki saka min na’a-na’an nan a ciki.”

“To.” Ta amsa mishi tana kallon sa a yanzu ɗin

Shi kuwa tuni ya wuce wajen su Hafsah yana cewa, “to ƴan mata na a tashi aje ayi sallah, ku bi Auntyn ku ɗaki tayi muku alwala.”

Amsa masa suka yi suna tashi da gudu suka yi ɗakin Luwairan

Ita kuwa tuni dama ta shige ta sanƙami wayan ta ta soma kiran layin Abida, don yanda take ji baza ta iya jira ba sai ta kwashe komi ta faɗa mata. Suna shigowa ɗakin kallon su tayi da ce ma Hafsah, “ke Hafsah ba kin iya alwalan ba?”

“Eh Aunty na iya.”

“To ku shiga Toilet ɗin kuyi ina zuwa, but ban ce kuyi min ɓarnar ruwa ba don na san halin ku musamman ma ke Yusra, ban son rashin ji.”

Duk gyaɗa mata kai suka yi suka wuce cikin Toilet ɗin nata

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button