MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 61 to 70

Ita kuma ta mayar da hankalin ta kan wayan ta.

               ✳️✳️✳️✳️✳️

       Tunda MEEMA ta shige ɗaki kuka kawai ta saka saboda yanda take jin ƙunci da wani abu ya tokare mata a wuya, duk yanda ta so ta jure ta kasa. Ta rasa me ke damun ta domin har yanzu ta kasa gane kishi ne ke ɗawainiya da ita. Har yanzu fargaba da tsoron abun da Sajjad yayi mata yana tare da ita, shiyasa hakan ke tasirantan zuciyarta take jin babu wani namiji da zata iya yarda da shi a halin yanzu, tana cikin tsoro sosai, but sai dai Umar Farouk ya tsaya mata a rai matuƙa. A ranan haka ta saka su Hajiya gaba da rigiman ta wai, “dole sai sun mayar da ita Riyadh, baza ta iya zama a nan ba zata iya mutuwa, ta tsani Nigeria ba ta son zama.” Haka take ta musu kuka duk ta rikita su, sun kasa gane me ke damun ta don da farko sun yi tunanin wani abun ne Umar Faruk yayi mata, sai ce musu tayi, “ita a’a ba ta son Zama a nan ne kawai.”

Ƙarshe dai sai da Uncle Hashim ya dawo ya rarrashe ta kafin ta samu tayi shiru, shima sai da yayi mata alƙawarin, “zai komar da ita.”

Hajiya tace, “me zai hana idan zaka koma Abuja kawai ka wuce da ita can, na san can zai fi mata nan tunda ƙila abubuwan da Sajjad ya yi mata ne har yanzu yake ɗaga mata hankali, ya kamata ta koma can da zama hakan zai fi mata.”

Uncle Hashim yace, “to Hajiya, amma sai mun gama da case ɗin nan don ba na son idan na tafi na sake dawowa, daƙyar aka bani hutun sati biyun nan da na ɗauka shima daƙyar sai da na basu ƙwararan hujjoji”.

              Daga haka suka bar zancen a kan MEEMA zata bi Uncle Hashim can Abuja

Itama ta amince domin dama ba ta son zaman ta a nan ne ba don komi ba sai don Umar Faruk, tana jin idan har ta ci gaba da saka shi a idanun ta ƙarshe zuciyarta ce zata buga, baza ta iya jura ba, baza ta iya juran halin da take ji a zuciyar ta a game da shi ba.

             Bayan kwana biyu da faruwar abun wanda yayi dai-dai da saura kwana huɗu a shiga kotu, sai dai labari suka ji Sajjad ya mutu

Tashin hankali da ba’a saka mishi rana, rikici fa ya ɓarke a tsakanin su Uncle Hashim da su Kawu Ali

Domin shi Kawu Ali ya hau ya dira yace, “wlh bazai yarda ba shima sai ya maka su a kotu domin MEEMA ita ta kashe mishi Yaro, bazai taɓa yarda ba sai ya bi kadin ɗan sa.”

Rigima aka yi ta yi daga ƙarshe ya maka su shima a kotun. A kwana huɗun da ya rage yanzu za’a shiga kotu

Su Umma sun sha kuka har sun gode wa Allah, ɗan su ɗaya tal ya mutu a kan wata, babu zagin da MEEMA bata sha ba a wajen dangin su, tuni labari ya bazu kowa ya san MEEMA ƴar wajen Faruk ita ce ta kashe Sajjad, wasu suna, “Allah wadai da ita.” Wasu kuma suna cewa, “su ma Allah ya ƙara da suka amshe ta har suka ajiye ta a gidan su, ga shi nan ta zame musu ƙarfen ƙafa ta kashe musu yaro be ji ba be gani ba.” Yayinda wasu kuma suke faɗin, “ai baza su yarda ba dole sai an kashe ta itama.” Shiyasa suka ji daɗin shiga kotun da za’a yi domin a hukunta ta, ko kaɗan ba sa ganin laifin da shi ya aikata mata.

     

???????????? 

*MEEMA FAROUK*

                     ????????????

*NA_NAFISA ISMA’IL*

*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????‍

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????

“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

               *SADAUKARWA*

_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._

*TARIHIN FARILTA SALLAH*

        “`An farilta sallolin nan biyar ne gabanin ƙaura, watau hijira, da shekara ɗaya da rabi. Sallah ce kaɗai ibadar da aka farilta ta a sama a daren Isra’e, kamar dai yadda aka ruwaito a hadisin nan na Anas. Da farko an umurce shi da Sallah guda hamsin ne; da sannu aka dinga rage su har suka zama biyar a bisa roƙon da shi Manzon ya yi wa Ubangijin sa. Da suka zama biyar, sai Allah ya ce masa su biyar ɗin nan, dai-dai suke da hamsin.

   Malamai da yawa sun yi bayanin yadda sallar ma’aikin Allah, mai tsira da aminci, take gabanin Isra’en.

Wasu malaman sun ce, “Gabanin Isra’e, babu wata sallah wadda aka farilta sai sallar dare (Ƙiyamul lail) wadda aka umurci ma’aiki da yin ta ba da iyakataccen lokaci ko adadi ba, kamar yadda yake a suratul Muzzammil, ayoyi huɗu na farko:

    “Ya wanda ya lulluɓe! Ka tsayu domin yin Sallah a cikin dare (duka) face kaɗan, rabin sa, ko ka rage abu kaɗan daga gare shi, ko ka ƙara kansa…        Ma’aikin Allah ya kasance yana yin sallar a kashi biyu cikin uku na dare ko a rabin sa ko kuma sulusin sa. Musulmi suka dinga yi tare da shi kamar shekara guda har suka gaji; daga nan sai Allah ya shafe ta don jin ƙan su.

       An ruwaito cewa sallar da Musulmi suke yi gabanin tafiyar dare suna yin ta ne kafin faɗuwar rana da kafin ketowarta kamar yadda yake a sallah littafin Almanhalil Azb. Gabanin ƙaurar Annabi zuwa Madina raka’o’in sallah bibbiyu ne, bayan ƙaura ne suka zama hurhuɗu, illa magriba da ta kasance raka’a uku, ita kuma sallar subahi ta tsaya a kan biyu saboda dogon karatun da ake yi cikin ta. Buhari da Ahmad sun ruwaito daga Nana A’ishah cewa, “an farilta sallah raka’a bibbiyu, bayan ƙaura ne aka mai da ita raka’a hurhuɗu, amma an bar sallar tafiya a kan raka’a ne bibbiyu, sai sallar magriba ita ko da ma raka’a uku-uku ce.”

        Allah ya sa mu dace.“`

                       *NO_38*

              A ranar da aka shiga kotu abun da aka soma tuhumar Sajjad da shi; laifin kidnapping, sannan auren dole da ya yiwa MEEMA ba tare da amincewar ta ba; ya zamar da ita Matar sa ta ƙarfi da ya ji, laifin drugs abused, yayi amfani da ƙarfin sa wajen ɗura mata magunguna waɗanda suka gusar mata da hankali har hakan ya kusa sanadiyar taɓa mata ƙwaƙwalwa, sannan kuma ya yi mata abortion wanda hakan yasa ba don tana da rai kusa ba da tuni an rasa ta. Waɗannan laifukan da aka lissafo a kan Sajjad su ne yasa Alƙali ya yanke hukunci nan take ya wanke MEEMA da laifin ita ce ta kashe shi, tayi hakan ne kawai domin ƙwatan kanta wanda ko waye ma a madadin ta hakan ne ya kamata yayi, don haka bata da laifi ko kaɗan tunda shi ne ya cutar da ita, azumi ne zata yi wanda kuma wannan tsakanin ta da Ubangiji ne

Sanda Alƙali ya buga guduma ya tashi ya fice sosai zuciyoyin su Kawu Ali ke tafarfasa, ba haka suka so ba amma basu da yanda za suyi, suna ji suna gani an kasa hukunta MEEMA a bisa kashe musu ɗa da tayi

Yayinda Mutane su ma suke ganin laifin Sajjad ɗin da irin ta’addancin da yayi, sun yi tur da Allah wadai da shi duk da babu shi a raye, haka yake ta shan zagi nan da nan labarin ya bazu a ko ina, kama tun daga gidajen talabijin da gidajen rediyo da jaridu duk labarin ya bazu, ko wani kafa ka kunna zancen kawai ake yi ana tur da Maza irin su.

                  To farin ciki dai a wajen su Uncle Hashim ba a magana tunda komi yanzu ya kau sai murna, sun koma gida cike da farin ciki inda kowa hankalin sa ya kwanta har ita MEEMAN wacce ta ɗaga hankalin ta gaba ɗaya sai kuka take yi, a tunanin ta ko za’a kama ta da laifin kisan kai ne

Yanzu haka kuma shirye-shiryen wuce wa Abuja suke yi ita da Uncle Hashim

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button