MEEMA FAROUK Page 61 to 70

Sanda ya sanar wa da Umar Faruk hankalin sa yayi ƙololuwar tashi, be shirya yin nesa da ita ba sabida ƙaunar da yake mata, yana ganin kamar idan tayi nesa da shi zai rasa ta. Duk ya tashi hankalin sa har yana cewa Uncle Hashim ɗin, “Dude yanzu shikenan bazan aure ta ba why zaka tafi da ita bayan ka san ina son ta? Idan tayi nesa da ni hakan zai saka na rasa ta gaba ɗaya?”
Murmushi Uncle Hashim ɗin yayi zuciyar sa cike da mamakin abokin nasa, sosai yake mamakin yanda yake kasa ɓoye soyayyar MEEMA har hakan ke son cutar da shi, hakan yasa yace mishi, “ka kwantar da hankalin ka idan har muna raye MEEMA Matar ka ce, ba wai tafiyar da zamu yi shi ne ka rasa ta ba, idan Allah ya yarda kai ne Mijin ta domin zan fi kowa farin ciki da hakan, ace yau daughter ta aure wanda ke matuƙar son ta ai Ni abin murna ne a wajena, Please be a man mutumi na ban son ka nuna ragwanta daga ƙarshe kuma ka ja ta raina mu, sai kace wani yaro?”
Murmushin da be shirya ba ya saki yayinda yake kallon sa, cike da sanyin murya irin nasa yace, “baza ka gane bane Dude, amma zancen raini kuma ai ya kau tunda har nake ƙaunar daughtern ka.”
“Haka ne. To dai ka zama na Mijin kai ma ka ja ajin ka, itama daughter tana son ka fa ba Wai kai kaɗai ne kake kiɗan ka kake rawanka ba, ka bata lokaci na san komi zai wuce da yardan Allah.”
Cike da fara’a a fuskar sa yace,
“Are you really or kidding me? Are you sure she loves me?”
“Yes she loves you.”
Lumshe idanuwan sa yayi cike da farin ciki ya kasa cewa komi
Sai Uncle Hashim ya dagi kafaɗun sa yana dariya da cewa, “ka zurma da yawa Mutumi na, Allah ya baka daughter na zaku dace sosai.”
“Ameen Ameen.” Yafaɗa yana shafa kansa, sai kuma yace, “when are you going?”
“Tomorrow insha Allah.”
“Ok Allah ya kai mu, zan zo muyi sallama.”
Da haka suka rabu kasancewar dama Uncle Hashim ɗin ne ya je ya same shi a Office ɗin sa.
Koda goben tayi a lokacin da zasu tafi sai ga Umar Faruk ya zo gidan. Shi ne ma ya ɗauke su ya kai su airport kasancewar ta jirgi zasu bi. Duk yanda ya so suyi magana da MEEMA hakan ya faskara
Domin ita ko kallon sa ba ta son yi, tunda ya zo gidan sai ta ɗauke walwalan ta take ta faman fushi, ko magana ta ƙi yi har suka wuce. Haka ma a cikin motan tunda ta shiga baya ta mayar da hankalin ta a kan wayan da ya siyan mata tunda yanzu da shi take using sakamakon nata tun sanda Sajjad ya amsa ba’a san inda yake ba ma, bata sake ɗago kai ba har suka kai
Shi kuma suna ta hira da Uncle Hashim kasancewar shi ke tuƙa motan, Uncle Hashim kuma na gefen sa, but hankalin sa na a kanta yana ta kallonta ta mirror ko zata ɗago kai, sai dai hakan ya gagara
Koda suka kai shi Uncle Hashim ɗin tuni ya fice yana amsa call
Hakan ya ba shi damar saka luck koda ta zo buɗe wa sai ta kasa
Dalilin da yasa ta ɗaga manyan idanuwan ta ta sauke a kanshi kenan tana kallon sa fuska babu fara’a. Yanda suka haɗa idanu ta cikin mirror ɗin ne sai tayi saurin ɗauke kai saboda wani irin faɗuwa da gaban ta yayi, yayinda ta ji wani abu ya tsarga mata tun daga tafin ƙafafuwan ta har a cikin kwanyan ta, dole ta lumshe idanuwan tana wani ƙanƙame jiki sakamakon tashi da tsigan jikin ta tayi
Shima lumshe idanun yayi kafin kuma ya juyo sosai yana fuskantar ta, tsawon soconni biyu ya ɗauka befor ya buɗe baki ya kira sunan ta, “ZULAIHA.”
take a nan ta ɗaga kai ta sake duban sa saboda yanda ta ji sunan ya shige ta sosai. Ido cikin ido suka kalli juna sai ta sake ɗauke kai saboda ta kasa jurewa da abubuwan da take ji na sauyi daga jikin ta
“Why are you going to leave me?”
Tambayar ta zo mata a bazata shiyasa ta sake ɗaga kai ta ɗan tsira masa ido kaɗan before ta sake ɗauke kai, hannayenta ta haɗe waje ɗaya tana jin zuciyar ta na sake gudu, sosai a yanzu ɗin ta soma rasa nutsuwar ta kasancewar su waje ɗaya
Numfashi shi kuma ya ja yana ci gaba da kallon ta ko ƙyafta idanu ba ya yi, a duk second soyayyar ta na ƙara huda magudanan jinin sa yana sake linƙaya; ta yanda yake jin tamkar yayi ta kurma ihu sabida azaban son ta, yana jin kuma kamar ya jawo ta ya mayar da ita cikin sa ta zama mallakin sa na har abada daga yanzu ɗin, sai dai babu hali. Sake jan wani ajiyan zuciyar yayi tamkar dai ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka, ya sake kafe ta da ido cikin cool voice ɗin sa yace, “I will miss you when you leave, I love you and I love you so much! I hope you continue to remember Me when you leave?”
Shiru ne ya biyo bayan zancen nasa, sai dai ita tuni ta sake kai kanta ƙasa tana sake haɗe hannayen ta waje ɗaya waɗanda suka soma tsatstsafo da gumi, ta soma gajiya da yanayin da take ji a tare da ita shiyasa ba tare da ta kalle sa ba tace, “I’m leaving… Open the door for me.”
Yanda sassanyan muryan nata ya daki kunnen sa ne yasa shi mayar da idanun sa ya rufe. Take kuma ya buɗe yana kallon ta be ce komi ba, sai can kuma ya danna luck ɗin ya buɗe mata yana me sake gyara zaman sa sosai
Ita kuma tuni ta buɗe ƙofan ta fice har tana rawan jiki, daƙyar ta aro jarumta wajen daidaita tafiyan nata wanda hakan ya sake mayar da ita tamkar tana yanga ko ba ta son taka ƙasan
Shima tuni ya fito ya harɗe hananyen sa a ƙirji yana bin ta da kallo. Har ta ƙarisa wajen Uncle Hashim be ɗauke ido a kanta ba
Sai daga baya da Uncle Hashim ɗin ya gama wayan ne ya taho wajen sa daga nan suka sake sallama. Sai suka wuce tare shi da MEEMAN kasancewar har an fara shiga jirgi, tana jan akwatin ta shima tare da nashi a hannu suka tafi
Umar Farouk sai da ya ga tafiyan nasu kafin ya hau mota ya tafi shima, zuciyar sa duk babu daɗi don shi gani yake yi tamkar ba ta son shi, and kuma Hashim yana faɗa masa, “tana son shi”. a haka ya koma gida cike da tunani kala-kala a ransa da kuma yanda zai jawo hankalin ta a wajensa, gaskiya bazai iya haƙura da ita ba dole ne ya san abun yi.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Sun isa Abuja By three. Drever’n Uncle Hashim shi ya zo ya ɗauke su zuwa barikin sojoji
Bayan sun isa gida Jalila da Habeeb suka fito tarban su
Da gudu Habeeb ya je ya rungumi MEEMA yana faɗin, “Aunty Oyoyo.”
Murmushi tayi cike da farin ciki a fuskar ta ta sake ƙanƙame shi
Jalila wacce ta amshi Trollyn mijin ta tana murmushi ta kalli MEEMAN da cewa, “Today you are at our house. Welcome.”
“Thanks Aunty.” Tafaɗa itama still tana murmushin
Cikin gidan suka wuce, inda gaba ɗayan su suka zube a saman sofa. Daga baya kuma Jalila ta tashi ta kawo musu drinks duk ta zuba ta basu. Bayan sun huta sai ta raka MEEMA ɗakin da zata zauna
Wanka ta soma shiga tayi kasancewar ta kwaso gajiya, sai ta ɗaura alwala tunda four ta kusa. Sallah tayi ta saka doguwar riga me sauƙin nauyi green color kafin ta fita Parlour. Jalila kaɗai ta tarar tunda su sun fita masjid
Nan Jalilan tace mata, “ga abinci nan a saman dainning.”
Zuwa tayi ta zauna tayi serving kanta ta soma ci kasancewar da yunwa dama a tattare da ita
Ita kuma Jalilan kichen ta wuce ta ci gaba da aikin ta
Babu jimawa su Uncle Hashim suka dawo daga masallacin. Shima kan dainning ɗin ya nufa ya zauna. Suna cin abincin suna taɓa hira, daga ƙarshe bayan sun gama suka koma Parlour
A nan ne Jalila itama ta fito ta zauna aka ci gaba da yi da ita