MEEMA FAROUK Page 61 to 70

Daga baya kuma Uncle Hashim ɗin ya tashi ya fice a gidan; su kuma suka ci gaba da hira tare.
Zuwa dare bayan sun ci abinci ne MEEMA ta koma ɗaki, tayi wanka har ta saka kayan barcin ta riga da guntun wando baƙaƙe masu tsantsi, tana tufke gashin kanta wayan ta tayi kar’ar shigowar text message, sai da ta gama abin da take yi kafin ta taso a gaban mirror ɗin ta zauna a saman gadon tana ɗaukan wayan nata. Duba wa tayi ta ga text ne daga Umar Faruk, kasancewar dama ya saba mata a koda yaushe, tunda ya bata wayan ya soma kiran ta but bata taɓa ɗauka sun yi waya ba, tun sanda ta ɗauka ta ji muryan sa shikenan kuma ta dena ɗauka, shiyasa a koda yaushe yake mata text babu dare babu rana, sai dai ta buɗe ta duba but bata taɓa mishi reply ba. Yanzun ma koda ta gani karanta wa tayi ta mayar da wayan ta ajiye, sai ta kwanta tana aza kanta a saman pilow tare da matse wa, lumshe idanun ta tayi tayi shiru bata sake motsa wa ba, sosai ta faɗa duniyar tunani sai da wayan ta soma ring before ta buɗe idanun ta a kasalance. Sai da ta ɗauki two seconds before ta ɗauki wayan tana duba screen ɗin, ganin Numban Umar Faruk sai ta tsaya kawai tana kallon wayan, daga ƙarshe har ta katse bata ɗauka ba, baza ta iya ɗauka bane shiyasa koda ya sake kira bata yi peacking ba, tana ji har wayan ta gaji da ring ta dena, sai kuma wani sabon message ɗin ya shigo. Dole ta ɗauka jiki na rawa ta soma duba wa. Murmushi kaɗai ta saki tana ajiye wayan ta koma ta kwanta. Shiru tayi kawai tana sauraron bugun zuciyar ta, ta jima a wannan yanayin wanda ita kanta ta kasa gane abun da ke damun ta, daga ƙarshe kuma sai tayi addu’a ta gyara kwanciyar ta. Babu jimawa barci ya sure ta cike da mafarkai kala-kala.
Zuwan ta Abuja yasa ta samu sauƙi daga abun da ke damun ta, sosai zaman gidan yake mata daɗi kasancewar yanda Uncle Hashim ke kula da ita matuƙa, kuma da yanda suke gudanar da al’amuran su shi da Jalila komi birge ta yake yi
Jalila yanzu da kanta take jan MEEMAN suke fita yawo ko kuma wajen aikin ta, komi Idan zata yi sai tace, “MEEMA ta zo suyi tare.” Har ta girki tare suke shiga kichen
Duk da ita MEEMAN ba ƙaunar cooking take yi ba but ba ta mata musu haka take shiga suyi tare tana koya mata wasu abubuwan. Shiyasa da sannu da sannu komi ya soma bata sha’awa har idan Jalilan ba ta nan ita zata shiga tayi ta jagwalgwala girkin, ko ta girka abin da take so ta ci, idan be yi daɗi ba kuma ta zubar.
Zuwa yanzu Uncle Hashim ya sama mata wani aikin but a wani Company ne na jaridu, shiyasa itama yanzu bata da lokacin kanta ko yaushe tana wajen aiki, ita da kanta take tuƙa mota ɗaya daga cikin motocin Uncle Hashim ɗin, tunda shi ba ya hawa any time yana wajen aikin sa
Har yanzu kuma Umar Faruk yana bibiyan ta but bata taɓa ɗaukan wayan sa ba. Sai dai a ko yaushe idan yayi mata text tana buɗe wa ta karanta, har idan be mata ba tana jin babu daɗi, ta saba yanzu da kalaman sa shiyasa duk sanda bata ga text ɗin ba a ranan kuwa tana rasa sukunin ta ne, ta kasa gane kanta a game da shi tunda ta kasa yarda son shi take yi, wani ɓangare na zuciyar ta tana burin ace a koda yaushe ta kasance da shi but bata san meyasa ta kasa amincewa da soyayyar sa ba, shiyasa duk sanda tayi kamar zata amsa Calls ɗin sa ko kuma ta mayar masa da reply sai ta tuna yana da aure, hakan ke sawa take jin wani irin tuƙuƙi da baƙin ciki wanda har sai ta ji tamkar ta kira sa tayi masa gargaɗin, “ya rabu da ita.” But ba ta iyawa.
Time ɗin da suka yi Seven weeks da zuwan su ne sai ga shi ya dira a gidan. A lokacin ita tana wajen aikinta sai dawowa tayi ta ganshi kwatsam.
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_39*
Shigowar MEEMA falon babu inda idanun ta suka faɗa face cikin na Umar Farouk, hakan yasa ta kasa ci gaba da takowa illa kallon sa da take yi ta kasa ko ƙyafta idanu, mamakin ganin sa ne ya bayyana a kan fuskar ta
Yanda shima ya tsare ta da ido ya gaza ko kaudawa. Yana riƙe da Glass cup a hannun sa wanda Jalila ta zuba masa Holandia yana sha. Sanye yake da fararen kaya kamar yanda ya zame masa ɗabi’a, gezna ce me tsananin tsada wanda kana kallo zaka san ba ƙaramin kuɗi ne da ita ba, kansa ya murza hula wanda yayi dai-dai da kalan aikin kayan nasa, sai farin eyeglasses medical da ya saka wanda ya ƙara fito da ainihin kamalan sa da kwarjinin sa tare da haiban sa, kana kallon sa ka ga mutum me tsananin kamala, har wani ƙiba ya sake yi ya yi kumatu
Abin da MEEMA kenan ta hango daga gare shi
Yayinda shima ya hango sauyi sosai a wajen ta, duk da bata yi ƙiba ba but ta sake murmurewa sosai, sai haske da ta sake yi yayinda kyakykyawar fuskarta ta sake fayau da ita
A hankali ta taka ta soma tahowa cikin falon saboda gajiya da tayi da tsayuwar, tuni ta ɗauke kanta daga kallon shi zuciyar ta na sake bugawa da sauri-sauri a kuma wani yanayi
Kasancewar gidan babu kowa sai Jalilan, domin shi Uncle Hashim ɗin yana wajen aiki, while Habeeb kuma yana school be dawo ba
Fitowar Jalila daga kichen da hango MEEMAN yasa ta saki fara’a tana cewa, “MEEMA are you back?”
Kallon ta tayi sai ta gyaɗa mata kai
“Ok. Your guest has come. He’s been waiting for you to come.” Tafaɗa da fara’a
Ita kuma ta kasa yin magana illa sauke kai da tayi ƙasa
While shi kuma yana kallon ta har yanzu sai dai be ce komi ba
Ganin haka yasa Jalilan tace mata, “She went to the bathroom and got ready and came out to greeting.”
Hakan yasa ta wuce da sassarfa ta shige ɗakin ta
Sai a lokacin ya lumshe idanun sa yana buɗe wa tare da ajiye ɓoyayyen ajiyan zuciya
Inda ita kuma Jalila zama tayi a wajen suna taɓa hira. Daga ƙarshe sai ta tashi ta wuce kichen tunda girki ta ɗaura saboda shi, dawowar ta kenan daga aiki ya zo ga shi babu komi a gidan, dole ta tashi da sauri ta ɗaura girki.
MEEMA wacce ta shige ɗaki ta kasa aiwatar da komi illa zama da tayi ta tsirawa waje ɗaya idanu, duk ta rasa sukunin ta jikin ta gaba ɗaya babu ƙwari, sai da ta ɗau lokaci a haka kafin ta tashi ta soma rage kayan jikin ta, Toilet ta shiga tayi wanka ta shirya cikin riga da wando, pink color ɗin wando burgujeje daga sama har ƙasa, sai farar riga Robber me dogon hannu wanda tayi talking ta cikin wandon, kasancewar wandon Robber ne ya kama mata ƙugu ɓam, bata saka komi ba a fuskar ta ba illa veil da ta sanya tayi Rolling a kanta light pink
Jalila ce ta shigo ɗakin saboda jin ta shiru da tayi bata fito ba, don a lokacin har ta gama girki ta zuba mishi yana ci. Shigowar ta yasa tace mata, “She came out and left him waiting for her.”
Ɓata fuska ita kuma tayi da cewa, “So what’s going on from me? I think there is no connection between us.”