MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 61 to 70

“Don’t say that MEEMA, this man loves you so much, he came from somewhere to you why would you do that to him?” Cewar Jalila da ta riƙe mata hannu

“Aunty he didn’t come for me, he come to Uncle.” Tafaɗa tana tura baki

“No, he didn’t tell me that, he came to you, but please accept him with open arms. Let’s go.” Ta ja ta suka fice. Har kujeran kusa da shi ta kai MEEMAN ta zaunar da ita sannan ta kalli Umar Faruk ɗin tana murmushi tace, “Ni bari in shiga ciki.”

“Ok.” Yafaɗa shima yana yalwata fuskar sa da murmushin. A lokacin har ya tsakura abincin ma ya gama

Tafiya tayi ta bar su ta shiga ɗaki

Shi kuma sai ya mayar da kallon sa kan MEEMA wacce ta haɗe hannayen ta waje ɗaya ta ɗaura su a saman gwiwowin ƙafafuwan ta, fuskar ta na kallon gefe ta wani haɗe rai tare da turɓune fuska. Sosai tayi masa kyau a shigan nata wanda har ya kasa ɗauke kai a kanta, tasbihi kawai yake yi a cikin ransa. Ya ɗau seconni yana kallon ta kafin ya ja numfashi da faɗin, “You Are not happy for my coming?”

Ɗago manyan idanun ta tayi ta zuba su a kansa, sai dai bata ce komi ba ta sake ɗauke kai

Sai yace, “Did I offend you MEEMA? Tell me what I did to you, I followed you to let me know what I did to you, why don’t you pick up my phone when I call?”

Shiru tayi tana mirza yatsun ta

“Zulaiha.”

Jin yanda ya kira sunan ta ne yasa ta sake ɗaga kai a karo na biyu ta kalle sa. A wannan lokacin bata iya kawar da kanta ba domin tayi ƙoƙarin ganin ta kalle sa sosai kamar yanda ta arawa kanta jarumta, shiyasa take bin shi da kallo ba tare da walwala a fuskar ta ba

Hakan yasa shi kuma jikin sa yayi sanyi, sai yace, “You don’t like me? Tell me please why don’t you love me?”

Lumshe idanu tayi ta buɗe, abun da take ji a zuciyar ta yana sake ƙuntata mata zuciya hakan yasa ta kasa yin magana, kuma ba ta jin zata iya yin magana ɗin, shiyasa ta ɗauke kai kawai, sosai zuciyar ta ke shiga ƙunci duk sa’ilin da ta tuna yana da wata mata, ta kan ji kamar ta amshi soyayyar shi sai dai hakan ke hana ta ba shi amsa, baza ta iya cewa ba ta ƙaunar sa ba sannan baza ta iya cewa ta amince da shi ba

Umar Faruk wanda ya gaji da shirun nata wanda har ya ji zuciyar sa tayi masa zafi. Shiyasa ya kalle ta yace, “You can go.”

Jin abun da yace sai ta sake kallon sa. Yanda ya kawar da kansa yasa ta ɗan tsira mishi ido, bata ce komi ba kuma ta tashi ta wuce ɗaki

Shi kuma da kallo ya bi ta har ta shige, sai ya ja numfashi yana jin zuciyar sa na sake zafi, hannun sa yasa a fuskar sa yana mayar da ajiyan zuciya a hankali, shi mutum ne mara son damuwa abu kaɗan ke ɗaga masa hankali. Daƙyar ya iya daurewa ya ɓoye halin da yake ciki. Koda Jalila ta fito sai yayi mata sallama a kan, “zai wuce, zai wuce ta wajen Uncle Hashim sai su gaisa daga can”.

            Ita kanta MEEMA ta san bata kyauta mishi ba, but bata san meyasa ba ta ƙaunar buɗe baki a gaban sa tayi magana ba, duk dai tana kishi ne saboda auren shi shiyasa ta gummaci tayi banza da shi, amma kuma zuwan da yayi har ya tafi da yanda ta nuna masa ya tsaya mata a rai, shiyasa ta kasa sukuni, walwalan ta gaba ɗaya ta rasa a ranan. Har dare yayi tana jiran text ɗin sa but babu, shiyasa can tsakar dare da zuciyarta ta kasa sukuni haka ta tashi ta ɗauki wayan ta, ta jima tana tunanin abin da zata aiwatar daga ƙarshe kawai ta bi umarnin zuciyar ta. Text message ta tura masa na gaisuwa da kuma komawar sa gida lafiya. Daga ƙarshe sai ta kashe wayan ta kwanta tana ƙanƙame pilow, daƙyar barci ya sure ta a wannan daren saboda a halin da take ciki.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

                *AFTER SIX MONTHS*

          Abubuwa da dama sun faru a cikin waɗannan watannin, ciki kuwa har da nasaran da Umar Faruk yayi a kan MEEMA, a yanzu haka ta amshi soyayyar sa inda suke gudanar da ƙaunar junan su kamar zasu cinye juna

Da taimakon Uncle Hashim da ya jajirce wajen nuna mata dacewar su da yanda yake nuna mata muhimmancin Umar Faruk a rayuwar ta, hakan yasa har yayi galaba a kanta

Yanzu ta rigada ta sallama zuciyar ta a kanshi, tana ganin shi ne zai zamo Abokin rayuwar ta, shi ta zaɓa ya zame mata farin cikin rayuwa, tana matuƙar son shi yanzu wanda ko kwatankwacin sa bata yiwa Ishaq ba, don tuni yanzu ta haƙura da Ishaq tunda Uncle Hashim ya sanar mata, “bazai taɓa biyo ta nan ba”.

              Yanzu haka Ummee ta samu mijin aure har an tsayar da rana. Wani hamshaƙin me kuɗi ta samu a nan Kaduna, sai dai yana aiki a can Zaria ne shiyasa a can zasu zauna da ita, but uwar ƴaƴan shi kuma tana Kaduna ne

Yanzu haka saura kwana uku bikin shiyasa MEEMA da Jalila da Habeeb suka shirya suka wuce Kaduna

Kasancewar shi Uncle Hashim yana Legos a halin yanzu wajen aiki, kusan two weeks yayi a can sai ranar ɗaurin auren zai leƙo.

         Sun isa Kaduna da magriba, su Hajiya sun yi murna da ganin su musamman ma MEEMA wacce dama tunda ta tafi bata taɓa zuwa ba sai yau.

          Washe gari sai ga Laɗifa ta zo gidan. Lokacin ma MEEMA na barci sai ita ne ta tashe ta, suka rungume juna cike da farin ciki a fuskar su

Laɗifa tace, “I’m glad to meet you again. I’m missing you. You left us.”

Murmushi ita kuma tayi tace, “No, I’m not leaving you. You’re in my heart, and we’re making a phone call.”

“But I want you to come back and live here. I’d rather enjoy that.”

“Ok zan dawo idan kina so.” Tayi maganar a cikin gwarancin Hausan ta wanda har yanzu ya kasa kama bakin ta

Waro ido Laɗifa tayi cike da farin ciki tace, “oh my MEEMA kin iya Hausa? Wow I’m happy wlh.”

Dariya ita kuma tayi wanda ba kasafai take yin shi ba, sosai kuwa ya yiwa fuskar ta kyau matuƙa, hannayen ta ta riƙe tana kallon ta tace, “I am learning with my Aunt, but Hausa akwai wahala.” Ta ƙare maganar tana ɓata fuska

Laɗifa dake dariya tace, “kuma tayi miki kyau wlh, but zamu sha dariya fa, wannan Hausa sai kace kina larabci, bari in kira Idris muji Idan Yana Kira.”

Murmushi tayi kawai don ba wai duka maganar nata ta gama gane wa ba, har yanzu hausa wahala yake bata sosai, idan ta iya wani abun kuma sai tazo koyan wani sai ta manta wancan, shiyasa a kullum ƙorafin ta wajen Jalila, “Hausa da wahala.”

Bayan Laɗifan ta gama wayan ta kalle ta tace, “Should we go to their house because it’s there.”

Shiru tayi sai kuma ta ɗaga kafaɗan ta da faɗin, “why not.”

Daga nan sai ta tashi ta shiga wanka ta fito ta shirya

Ita kuma Laɗifan tuni ta fice Parlour wajen su Hajiya

Bayan ta gama shiryawa cikin bak’ar material ɗinkin riga da skert, an yi zanen flowers da Orange color, ya ɗauki skin ɗin ta sosai kayan ya sake mata kyau ainun, bata saka ɗan kwali ba sai ta tufke gashin ta a ƙeya, sannan sai ta saka siririn farin gyale me kwalliyan Stones ɗan ƙarami, iyakan kanta ya rufe mata ya sauka a kafaɗan ta, flet shoes ta saka fari da agogon hannun ta ma fari, sai ta ɗauki wayan ta ta fito. A falo ta tarar da su. wajen Hajiya ta nufa ta rungume ta tana sakar mata peak a kumatu, kana tace, “good morning my grandma.”

Sai da ta shafo fuskar ta kafin ta amsa ta cike da fara’a

Daga nan suka gaisa da Zabba’u wacce dama su biyu ne a parlour’n sai Laɗifa da ke zaune

“Grandma we will go to their house Idris.”

“But you didn’t do Breakfast?”

Shafa cikin ta tayi da faɗin, “I’m not hungry.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button