MEEMA FAROUK Page 61 to 70

“No, you can’t go out without breakfast. Go and do whatever.”
Hakan yasa ta wuce kan dainning ɗin ba tare da ta sake cewa uffan ba
Zabba’u tace, “ke ma Laɗifa kin ƙi cin komi haka ake yi?”
Murmushi tayi da faɗin, “Baaba ba na jin yunwa wlh, sai da na cika ciki na kafin na fito”.
Daga nan hiran su suka ci gaba da yi inda ita Laɗifan ta tashi ta wuce wajen MEEMA da ke kan dainning
Bayan ta gama suka fita tare suka yi gidan su Idris. A can suka wuni har da Idris ɗin tunda yana gida, daga ƙarshe ma sai suka fice gaba ɗayan su wai zasu je zaga gari. Idris ne me tuƙin. Bayan sun gama yawon sai suka dira kuma a gidan su Laɗifa
Suna can ne Umar Faruk ya kira MEEMA yana tambayar ta, “inda take zai zo wajen ta?”
Shi ne tayi masa kwatancen inda take
Yace, “ga shi nan”.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
A fannin Luwaira har yanzu bata san yana tare da MEEMA ba, duk a tunanin ta yanzu ba sa tare, ta kwantar da hankalin ta yanzu gaba ɗaya ta cire wata MEEMA a rai tunda tana samun kulawa ɗari bisa ɗari a wajen sa, ba ta rasa komi abun da take buƙata. Umar Farouk mutum ne shi wanda ya iya soyayya ko kaɗan ba ya tauye mata haƙƙin ta a matsayin ta na matar sa, dai-dai gwargwado yana bata farin ciki da ƙarfin iyawan sa, shima yana jin daɗin zama da ita tunda tana ƙaunar sa sannan tana nunawa yaran sa ƙauna, abun da ya fi so kenan ya ga an damu da yaran sa
Har Momy itama tayi tunanin ya rabu da zancen MEEMA tunda be sake tayar da maganar ba. Abun da ke damun ta yanzu shi ne rashin samun cikin Luwaira har yanzu shiru ko ɓatan wata bata taɓa yi ba
Bata san cewa ita Luwairan magani take sha ba don hana ɗaukan ciki, a bisa shawaran Abida wacce ta sanar mata da komi kasancewar yanzu babu ɓoye-ɓoye a tsakanin su, ita ta bata shawaran, “kar ta sake tace zata ɗauki ciki, muddin ta ɗauka kuwa su Momy zasu cika burin su a kan Umar Faruk, zata rasa shi a nan gaba, sabida idan ta haifu su kuma a nan ne zasu aiwatar da ƙudirin su a kansa, idan kuma bata haihu ba zasu yi ta jelan jira har sanda zata samu ciki ta haihu kafin su kashe sa.”
Ita kuma Luwaira ba ta son a raba ta da mijin ta, ƙaunar da take mishi baza ta bari tana ji tana gani Mahaifiyarta ta aiwatar da abun da take so ba, shiyasa taga ya dace ta bi wannan hanyar. A halin yanzu har ta gama karatun ta kasancewar dama suna zangon ƙarshe ne. Ta mayar da hankalin ta yanzu kan mijin ta tana kyautata mishi da iyawan ta domin kawai ta ga ta sake shiga zuciyar sa ainun.
Inda shi kuma Umar Faruk ɗin ya jingirta da auren MEEMA ne ba don komi ba sai don ganin auren su da Luwaira be wani daɗe ba, idan har yace zai taso da maganar auren su da wani idon zai kalli Momy? Ace yana auren ɗiyar ta sannan ko shekara bata rufa ba yazo musu da zancen sake aure, shiyasa ya bari zuwa nan da kamar sun yi shekara ɗaya sai ya taso zancen
Duk da Uncle Hashim yana ta faɗa masa, “gwara ayi a huta hakan zai fi.”
But yanzu sun yanke shawaran nan da one month zai tura a nema masa auren ta, tunda zancen auren Ummee ya taso shiyasa suka ce a bari zuwa an yi nata ya wuce
Itama MEEMAN ta amince tunda ta ƙosa ta aure shi, a yanda take ji yanzu ba ta ƙaunar ko sati ne ta ƙara a gida, ƙaunar da take mishi ya rigada ya tabaibaye ta wanda tana jin baza ta iya rayuwa babu shi ba, shi kaɗai yanzu take kallo a zuciyar ta. Babu wani saurayi ko namjin da ke burge ta sama da shi. Soyayya me tsafta sosai suke gudanar wa wanda burin ko wannen su yaga ya mallaki ɗan uwan sa.
_Mu je zuwa. Yanzu za’a fara._
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_40*
A tsanake yake shirin sa duk da yana sauri ne, ya shirya a cikin shadda gezna maroon color me tsada sosai, sai yayi using da Black shoes and wrist watch, ya saka ƙuben hula da ya dace da aikin kayan sa, yanda ya kofa hulan ne yasa ake iya hango kwantaccen baƙin gashin kansa daga ƙeya, ta zauna masa hulan ɗass ta sake fito da ainihin kamalan sa da tsantsan kwarjinin da Allah ya ba shi, sai ya saka eyeglasses medical sannan ya feshe jikin sa da turarukan sa masu shegen ƙamshi da saka zuciya natsuwa. Ya kalli kansa a madubi sai ya saki murmushin sa me kyau yana sake shafa kyakykyawar fuskar sa. Wayoyin sa ya kwasa ya zuba a cikin aljihun rigan sa kana ya ɗauki keeys ɗin mota ya fice
Luwaira wacce ke zaune a katafaren parlour’n ƙasa ita da su Yusra suna kallo, ta ci kwalliya a cikin ƙananan kaya fuskar nan ta sha kwalliya tana ta faman taunan chewing gum, jefi-jefi take sauraron Yusra wacce take mata surutu gaba ɗaya ta ishe ta; tana sauraron ta ne kawai ba don tana so ba. Tunda Umar Faruk ya doso Steps ɗin ƙamshin turaren sa yayi mata maraba a cikin hanci, shiyasa ta lumshe idanuwanta tana ƙara zuƙo shi sosai tare da buɗa hancin. A take ta buɗe idanun nata ta sauke a kansa
A lokacin ya rigada ya sauko daga Steps ɗin idanun sa shima a kanta, yayinda fuskar nan tasa me kamala take fitar da annuri kamar yadda ta saba. “My babies.” Yafaɗa sanda ya isa wajen idanun sa a yanzu a kan yaran nasa
Da gudu Yusra ta soma tashi ta nufe sa tana kiran sunan sa
Itama sai Hafsan ta tashi ta nufe sa duk ya rungume su
Luwaira wacce ta kasa motsi sai a lokacin ne ta miƙe zuciyar ta cike da bege gami da ƙaunar sa itama ta ƙarisa wajen sa. Cikin murmushi tace, “ranka ya daɗe sai ina kuma?”
Murmushi yayi mata yace, “zan fita ne akwai inda zan je. But har yanzu lessing teacher ɗin su be zo bane?”
“Eh be zo ba. Amma na san maybe zai zo tunda yanzu 4 tayi.”
Numfashi ya ja kana ya kalli yaran yace, “ok babies ku sake Ni zan tafi, me kuke so in siyo muku?”
Nan ko waccen su ta soma sanar mishi da abin da take so
Shi kuma murmushi yayi yana shafa kansu, sai kuma ya mayar da idanun sa a kan Luwaira wacce itama fuskar ta yalwace take da murmushin. yace, “ke fa baki faɗa min abin da kike so ba? Ko kar in siyo miki komi?”
Still murmushi tayi tana ɗan kawar da kai, cikin kunya tace, “nima ka siyo min abin da suke so saboda bani da zaɓi”.
“To shikenan. Take care, bari in wuce.” Daga haka ya bi yaran ya sakar musu peak a kumatu su ma suka yi masa. Har ya juya zai tafi kuma sai ya jiyo ga Luwairan yana kallon ta
Yanda ya zuba mata fararen idanunsa ne yasa ta ɗauke nata idanun
“Ke baza kiyi min naki kiss ɗin bane?” Yayi maganar a hankali
Murmushi tayi tana kallon su Yusra waɗanda suka zuba musu idanu
“Oya Common.” Yayi maganar yana riƙe mata hannun ta tare da jawo ta jikinsa suka haɗe
Hakan yasa ta ɗago kai cike da kunya tayi mishi kiss ɗin a kumatu
Shafa wajen yayi kawai ya sakar mata smile sannan yayi mata nashi a goshi ya sake ta ya juya ya fice coz a ƙage yake ya fice
Ita kuma tabi bayan sa da kallo cike da zallan farin ciki da ƙaunar sa. Sai da ta gama tsayuwar ta a wajen kafin ta juya zuwa ɗakin ta