MEEMA FAROUK Page 61 to 70

Su kuwa su Yusra tuni sun wuce kan kujera sun zauna sun mayar da hankalin su a kan kallon su.
*********
Fitan Umar Faruk Part ɗin Momy ya je ya gaishe ta sannan ya wuce compound ɗin gidan. Koda securities ɗin sa suka nemi bin sa dakatar da su yayi, ya shiga ɗaya daga cikin motan nasa wanda ta kasance fara ce ya bar gidan. Sai da ya tsaya a masjid ɗin kan layin yayi Sallah. Kai tsaye sai ya wuce address ɗin gidan su Laɗifa. Yana zuwa bakin ƙofan gidan su bayan yayi parcking sai ya ɗauki wayan sa ya kira Numban MEEMA
Kamar mintuna goma da tsayuwar sa sai gasu sun fito ita da Laɗifan, kasancewar shi Idris tuni ya tafi tunda MEEMAN ta faɗa masa, “za’a zo a ɗauke ta.” Sai da ya gama mata tsiya da tsokanar ta kafin ya wuce a cewar sa, “yana da wurin zuwa dama”.
Umar Faruk wanda ke cikin mota idanun sa ƙyar a kan MEEMA, har suka iso wajen yana kallon ta, sai da ya lumshe idanun sa ya ya wani ja gauron numfashi kafin ya saka hannu ya buɗe ƙofar motan ya fito still idanun sa a kan MEEMA yayinda fuskar sa ke fitar da annuri
Laɗifa ita ta fara gaishe shi cikin girmamawa
Ya amsa ta yana murmushi da cewa, “kina lafiya?”
“Lfy kalau Sir.”
Still murmushi yayi da cewa, “baza ki fasa kira na da Sir ɗin nan ba? Da alamu kina so muyi faɗa ko? Heartbeat you are listening her?” Ya ƙare maganar yana mayar da idanun sa kan MEEMA tare da sakar mata wani irin kallo wanda yasa ta kawar da kanta tana kaɗa manyan idanuwan ta
Dariya ita kuma Laɗifa tayi ba tare da tace komi ba
“Ok tunda baza tayi magana ba, mu zamu tafi. Ki gaishe min da mutanen gidan idan kin shiga.” Sai ya saka hannu cikin aljihun rigan sa, ya ɗan laluba kuma sai ya buɗe motan da cewa, “wait kar ki tafi.” Yayi maganar saboda ganin Laɗifan tana yiwa MEEMA sallama zata wuce. Motan ya koma ya ɗauko bandir ɗin ƴan dubu-dubu da shi kansa be san nawa bane, ya miƙa mata yana cewa, “ga shi ko sai ki siya kayan kwalliya.”
Hannu ta saka ta amsa tana masa godiya
Yace, “a’a babu godiya tsakanin mu Laɗifa. Kuyi sallama ina mota.” Sannan ya shige cikin motan
Laɗifa hannun MEEMA ta kama tana kallon ta da murmushi tace, “Ni bari in shiga ciki in barki da masoyin ki, until we make a phone call.”
Gyaɗa mata kai tayi ba tare da ta furta komi ba. Sannan suka zaga tare Laɗifan ta buɗe mata ƙofan ta shiga ta rufe mata tana ɗaga musu hannu. Sai da motan ta tafi kafin itama ta shige cikin gidan su
Umar Farouk wanda ke murza motan a hankali ya juyo yana kallon ta da cewa, “heartbeat are you quiet or is something bothering you?”
Girgiza kanta tayi sai kuma ta juyo tana kallon sa itama. Murmushi ta sakar masa da cewa, “Nothing’s bothering me.”
“Ok now. Where are we going?”
Ɗan kawar da idanun ta tayi tana juya su da turo baki gaba, “We are going home.”
“No, there’s a place for me to go. I’m waiting for that day.”
“Where are we going?” She said looked at him
Murmushi yayi mata yace, “ki bari idan mun je zaki gani, I’m going to surprise you.”
Kanta kawai ta ajiye a jikin kujeran ba tare da ta furta komi ba
Sai ya kira sunan ta da cewa, “heartbeat ko ba kya so?”
Idanunta ta zuba mishi, sai ta sakar mishi murmushin ta me kyau tana kaɗa manyan idanun ta tace, “whatever you want I want, or I say let’s go and follow you.”
Lumshe idanun shi yayi yana buɗe wa tare da sake tamke sitiyarin motan. Cikin amon muryan sa me sanyi yace, “If you look at me like that, you’re making me lose my temper heartbeat.”
Dariya tayi wanda yasa dumples ɗin ta suka bayyana
“I love You! I love You so Much my heartbeat!” Yayi maganar yana sake kallon cikin idanun ta cikin narkewar soyayyarta
Ita kuma ta kasa jure kallon nasa shiyasa ta ɗauke kai zuwa kan titi tana zuba murmushi wanda ke bayyana tsantsan farin cikin da take ciki
Shi kuma numfashi ya ja kawai yana ci gaba da tuƙin sa, inda idanun sa shima ke kan titi, but jefi-jefi yake waigo da idanun sa gare ta yana sakar mata murmushi. Can kuma sai yace, “heartbeat I long to get married, buri na a yanzu kawai in mallake ki in huta da zuciyata.”
Ɗan kallon sa tayi kafin ta ɗauke kai tace, “I don’t understand. What happened to your heart?”
“Oh you don’t know?” Yayi maganar still yana ware idanu a kanta
Tura baki tayi da faɗin, “Yes I don’t know.”
“Ok soyayyar ki take wahalar da Ni a zuciya ta.” Sai ya kama setting zuciyar sa da cewa, “I feel like I’m going to die because of your love, MEEMA I’m not tired of expressing to you how much I love you, i love You with all my heart!”
Cike da farin ciki take kallon sa. Cikin so da ƙauna ta langaɓe kanta tana sake narke idanu tace, “me too love! I love you so much in my heart, I love you so much and so much!”
“Kar ki saka in Yi hatsari Heartbeat ki rage min irin Wannan kallon.”
Kasancewar bata fahimci inda ya dosa ba sai ta ware idanunta sosai a kansa da cewa, “whattt..?”
“I mean the look on your face will make me take an accident, stop kinga I’m driving.”
Murmushi tayi kawai tana sauke kai gefe.
Wani wajen shaƙatawa ya wuce da su inda masoya da ƴaƴan masu kuɗi suke zuwa wajen, wajen na manyan Mutane ne sosai don ba a samun ƙananun talakawa a wajen. Parcking yayi a haraban wajen kafin ya ɗauki wayan sa ya soma dealing number
MEEMA wacce take kallon sa lumshe idanuwan ta kawai tayi tana sake realising a kan kujeran da take
Shima kallon ta yake yi but a lokacin ya ɗaura waya a kunnen sa yana magana. Zuwa can kuma ya cire wayan yana tsare ta da idanu, cikin murmushin sa da ke masa kyau matuƙa ya kirayi sunan ta
Hakan yasa ta buɗe manyan idanun ta a kanshi, sai itama ta sakar masa murmushi tana sake ɗauke kai saboda yanda take ji a jikin ta da kallon nasa
“Don’t get tired. Give me some time. There’s someone I’m waiting for.”
Kanta ta jinjina kawai tana ɗan sakin numfashi
Shi kuma sai ya saka hannu ya buɗe motan ya zura ƙafafuwan sa a waje, wayan sa a hannu yana duba wa sai kuma ya fice hango wani receptionist ya taho wurin
Koda ya ƙariso cikin girmamawa ya soma gaishe shi domin alamu ya nuna sun san juna
Dayake shi Umar Faruk yana yawan ziyartan wajen domin wajen zuwan sa ne, musamman idan yana buƙatar keɓewa. Bayan sun gaisa magana suka yi kafin shi ya juya shi kuma ya shiga cikin motan. Sai yace, “heartbeat.”
“Uhm.” Tafaɗa tana buɗe idanu tare da zuba masa su
“Are you tired?”
Murmushi tayi kafin ta girgiza masa kai, sai kuma tace, “But what are we going to do here?”
“Surprised. I’ll let you know.” Yayi maganar yana mata murmushi. Sai kuma wayan sa ta soma Ring, hakan yasa ya ɗauka yana karawa a kunne, “ok”. Kaɗai ya furta kana ya cire wayan yana kallon ta. “Let’s go.”
Murmushi tayi kana ta saka hannu ta buɗe motan ta fita
Shima fitan yayi yana gyarawa eyeglasses ɗin sa zama, sai ya rufe motan kana suka taka a tare zuwa ciki. Kai tsaye wani rumfa suka nufa inda babu kowa a wajen don sun wuce Mutanen da ke can haraban wajen tsilli-tsilli
Yanda suke tafiya zaka san cewa tabbas lover’s couple ne, domin ba ƙaramin dacewa suka yi da juna ba, a hankali suke takawa har sanda suka isa rumfar, inda wajen an ƙawata shi da fitilu masu haske kala-kala, yayinda table ɗaya kuma aka fi ƙawata shi da flowers, ga kuma expensive drinks duk an cika table ɗin