MEEMA FAROUK 1-END

MEEMA FAROUK Page 61 to 70

“Bismillah.” Yafaɗa yana mata wani kallo me shiga rai fuskar sa yalwace da fara’a

Ita kuwa tsaban farin cikin ganin wajen yanda ya burge ta har buɗe baki take yi, kallon sa take yi ba tare da ta furta komai ba

Sai ya gyaɗa mata kai yana sake nuna mata da hannayen sa yace, “sit Please.”

Zama tayi tana mayar da idanun ta a kan table ɗin

Sai shima ya zauna idanun sa a kanta yace, “Are you happy to see the place? I hope you are enjoying?”

Kanta ta gyaɗa masa sai tace, “na’am, I’m happy Love, But why did you prepare this for me?”

“I’m telling you it’s because you’re happy. I want to be alone in such a place. I’m impressed.”

“Me too.” Tafaɗa cikin farin ciki

Kallon ta kawai yake yi yana murmushi, kana kuma ya saka hannu ya ɗauki Cup ɗaya da ke kife a cikin ƙaramin Glass plate tare da ɗaukan ɗaya daga cikin drinks ɗin wanda ke a cikin wani irin dogon kwalba, ya tsiyaya a Cup ɗin kafin ya sake ɗaukar wani ya zuba, sai ya miƙa mata yana kashe mata idanu tare da murmushi yace, “take.”

Farin hannun ta ta saka a hankali ta amsa tana kallon sa itama

Shima ɗaukan nashi yayi kana ya matso dashi kusa da nata ya ɗan buga kaɗan before suka kai bakin su a tare. A taren kuma suka cire suna sakar wa juna murmushi, sai da ya ajiye nashi kafin ya gyara zaman sa yana kallon ta da cewa, “heartbeat I have a gift for you.”

Ɗan waro ido waje tayi still har yanzu fuskar ta yalwace da fara’a, sai kuma ta ɗan saki murmushi tana tokare haɓan ta da hannayen ta biyu da ta dunƙule, ta zuba masa idanu tana wani narke su cike da ƙaunar sa tace, “Will you give me a gift?”

“Yes, but close your eyes.”

“Ok.” Tafaɗa tana murmushi, sai kuma ta rufe idanuwan ba tare da ta cire hannayen ta daga haɓar nata ba

“Ok open.” Yafaɗa sanda ya gama zaro wani ɗan ƙaramin kit na Ring ya ciro shi

Ware idanun ta tayi a kansa sai kuma tabi Ring ɗin da kallo, ta kasa yin magana illa kallon sa da take yi

Sai ya sakar mata murmushi tare da cewa, “Bring your hand and I will put it on you.”

Hannun damar ta ta miƙa masa. Sai ya zira mata farin zoben wanda ya kasance na gold ne, a ɗan ƙaramin yatsanta ya zira mata kasancewar ɗan siriri ne me kwalliya a saman, sai ka kula sosai zaka hangi haruffan sunan su a jiki an saka *U&Z*

Janye hannun ta tayi ta kai dai-dai fuskar ta tana ƙarewa zoben kallo, a nan ne itama ta kula da harufan da ke cikin zoben, shiyasa ta furta, “woww!” Tana washe ƙananun haƙoran ta wanda dumples ɗin ta suka samu damar fito wa sosai da sosai suka sake ƙawata kyakykyawar fuskar nata

Shi kuwa murmushi kaɗai yake zuba wa yana sake tsare ta da idanu domin ba ƙaramin kyau ta sake masa ba a yanzu ɗin, soyayyar ta ne ke ƙara huda jinin jikin sa tana yawo a duk gaɓoɓin sa da ke aiki. “I hope he impresses you and does it for you?” He speaks still smiling

Kasa magana tayi illa kallon sa da take yi, sai kuma ta langaɓe kai kamar zata yi kuka tana sake narke murya da cewa, “I’m so happy with this gift of yours for Me. I can’t tell you how I feel in my heart! I love the Ring so much, thank you Love.”

Yanda idanun ta ke ƙyalli hakan ya gane hawaye ne a cikin idanun ta. Sai ya lumshe idanu yana sake buɗe wa a kanta yace, “Are you going to cry?”

Ware ido tayi sai ga hawayen sun soma ɗiga a kuncin ta, “I’m very happy! I can’t describe to you how I feel Love, I love you so much!”

“Let’s have some drinks and go. Don’t let Hajiya hear you shut up.” Yayi maganar sabida ya ɗauke mata hankali don ba ya son ganin hawayen nata, yanzu ba lokacin su bane lokacin farin ciki ne

Hakan yasa ta ɗauki Cup ɗin tana kaiwa bakin ta, sai dai idanun ta a kansa suke ta kasa ɗauke wa

Yanda suke sakar wa junan su kallo me ma’anoni daban-daban wanda su kaɗai ne suke iya fahimtar a halin da zuciyoyinsu suke ciki.

                Sai da suka gama sha sannan suka tashi suka bar wajen. Kai tsaye gida ya mayar da ita, sai da suka ɓata lokaci a waje suna sake soyewa kafin suka rabu, ta shiga gida shi ya ja motan nasa ya bar wajen

Koda ta shiga gidan akwai baƙi sosai, don yawanci ƙawayen Ummee suka zo

Shiyasa tana shigowa Ummee ta soma nuna musu, “ita ce ɗiyar ta.”

Hakan yasa suka gaisa suna ta yaba kyawun MEEMAN, sai janta da hira suke yi kowa na haba-haba da ita

Ita dai murmushi kaɗai take musu tana zaune a cikin su don sun hana ta tafiya. Sai daga baya ta samu ta silale ɗaki, a lokacin ne taji shigowar message wanda Umar Faruk ya tura mata na kalaman soyayya, murmushi kaɗai take zubawa tana karantawa, sai da ta gama sai ta mayar da idanunta a kan zoben hannun nata tana kallo still fuskarta ɗauke da murmushi, hannun ta kai bakinta ta sakar wa zoben kiss tana wani lumshe idanuwa, sai kuma ta kwanta tana ƙanƙame pilow still idanuwan ta a rufe, shauƙi da bege gami da soyayya ne ke tsumata wanda har ta kasa taɓuka komi tana nan kwance a wajen, sai kuma daga baya ta tashi zaune ta ɗauki wayan nata ta tura masa message ɗin itama kana ta tashi ta soma rage kayan jikin ta, saka towul tayi ta shiga Toilet tayi wanka ta fito ta sanya doguwar riga na atamfa me ruwan zuma da ratsin baƙi-baƙi da ja, ta yafa siririn gyale a kanta sannan ta fice Parlour tunda akwai sauran time ɗin sallan magriba.

     

          **********

            Ranan juma’a dubban jama’a suka shaida ɗaurin auren Ummee ita da mijin ta Alh. Shu’aibu Khabeer. A ranan aka wuce da ita Zaria, daga ƙawayen ta sai Zabba’u suka tafi, su ma a ranan zasu dawo tunda ba kwana zasu yi ba

Hajiya ta so MEEMA taje but ita taƙi, duk da har yanzu ba wai ta saki jikin ta da Ummeen bane amma dai ta sauka daga fushin da take mata sosai, tunda Uncle Hashim yana zaunar da ita yayi ta mata nasiha yana gaya mata girman uwa, ko me Uwa ta aikata wa ƴaƴan ta ba a fushi da ita. Kuma ta gane sosai yanzu sai dai rashin sakin jikin ta da ba ta yi da ita ne.

                 Koda aka gama bikin MEEMA bata koma Abuja ba sai da tayi sati ɗaya curr a garin, Jalila ce suka koma ita da Uncle Hashim a washe garin bikin. Ranan da zata koma Umar Faruk ya kai ta har can Abujan, sai da yayi kwana biyu a can don dama akwai aikin da ya kai shi

Bayan ya dawo ne ya je wa Momy da zancen auren sa da yake son ƙarawa, duk da be so ya taso da maganar a yanzu ba duba da rashin daɗewar auren sa da Luwaira, to amma ya kasa jurewa ne, fatan sa a yanzu kawai ya mallaki MEEMA ta zama tashi ta har abada, hakan zai saka hankalin sa ya kwanta shiyasa ya kasa jurewa ya sanar mata da zancen

Ita kuma sanda taji maganar hankalin ta ya tashi tunda bata san har yanzu yana da burin auren MEEMA ba. Sai dai ta kasa nuna hakan a fili illa nuna farin cikin ta da jin zancen da tayi a fuskar ta

Shi kansa har kunya ne ta kama shi saboda ganin yanda ta nuna farin cikin ta, sai ya ga tamkar be kyauta mata ba ace yana auren ɗiyar ta ko rufa wata takwas da aure basu yi ba ya kawo wani zancen, amma ya ya iya? Bazai haƙura da auren MEEMA ba, ita ce jinin jikin sa, ita ce farin cikin sa a yanzu, be da buri a yanzu sama da ya mallake ta, da ita yake kwana a koda yaushe, farin cikin sa da walwalan sa yana da nasaba da ita, ita ce cikamakon rayuwar sa a yanzu, be da wani abun bege sama da ita, ita kaɗai ce zata zamo cikon rayuwar sa kuma cikon farin cikin sa. Ya ji daɗin yanda Momy ta nuna damuwa da farin ciki da abinda yake so, shiyasa ya ji a zuciyar sa be da wata Uwa bayan ita, ya ƙara ganin girmanta sosai a zuciya, musamman da ta sanar masa, “a hanzarta a kai gaisuwa gidan su MEEMAN sabida a tsayar da ranan aure”. Wannan zancen ya fi komi saka shi farin ciki. Shiyasa koda ya tashi daga wajen ta sai ya wuce Part ɗin sa. Kasancewar yaran sa suna school a lokacin sai Luwaira kaɗai ya gani a parlour, bayan tayi masa sannu da zuwa ya amsa ta cike da fara’a yana zama a gefen ta tare da zame hulan kansa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button