Al-Ajab

Miji ya kama matarsa na lalata da dan’uwansa a kan gadon aurensu

Wani dan kasuwa, Justine Onu, a ranar Litinin din nan ya bukaci wata kotu da ke Jikwoyi, Abuja, da ta raba aurensa da matarsa, Joyce, bisa cewa ya kama ta tana lalata da wani dan uwansa.

 

Mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa matarsa ​​ta kasance tana aikata sana’ar karuwanci ya kuma fada wa kotun cewa ya gaji da auren.

 

Sai dai wadda ake kara, Joyce, ta musanta dukkan zarge-zargen da mijinta ya yi a kanta.

 

Alkalin kotun, Labaran Gusau, ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba.

Kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su mungode!

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button