MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

Murmushi yayi ya dan kalleta bayan ya rausayar da kanshi gefe daya,
“To ko dai ban samu karbuwa bane?”
Murmushi tayi wanda har fararen hakoranta suka bayyana,
“Hmmmm….. Anya kuwa ban yimaka tsufa ba?”
Harararta yayi hararar dake cike da ma’anoni daban daban,
“Nawa kike da har zaki yimin tsufa,nine ma dai nake tunanin kamar zan iya yimiki tsufa”
Wannan karon dariya tayi sannan ta kalleshi,
“Kai ai har yanzu kamar yaro ne,ban san menene sirrin ba amma baka canjawa”
Murmushi yayi yana wasa da agogon hannunshi,
“Maamy kenan…. Ai kin fini kuruciya,wai dan Allah yaran nan waye zai zaci naki ne? Saifa wanda yasani”
Dariya tayi suka cigaba da koda juna daga bisani ya kalleta,
“Me kike so inbaki a matsayin sadaki…?”
Dan jimm tayi alamar tunani,zuwa can ta kalleshi,
“Ring…”
“Na gold ko na azurfa?”
“Diamond gold”
“Angama ranki yadade,kamar nan da yaushe kika shirya yin auren ne?”
“Ka bari zamuyi wannan maganar daga baya”
Misalin karfe 11 suka koma gida, Hanan tun 10 take jiran dawowarsa taci gayu cikin English wears riga da skirt,kamar wacce akace ta sauka kasa tana saukowa suna shigowa,tsayawa tayi tana kallonsu maamy sanye cikin bakar doguwar riga mai adon stones ja ajiki ta yafa jan mayafi marar nauyi,shi kuma Khalil kananan kaya ne ajikinsa jeans da riga long slif mai dogon hannu da p cap duk bakake,kafarsa sanye da bakin combos,sosai yayi kyau abunka da farin mutum cikin bakin Kaya……………………….鉁嶐煆?
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
Share this
[ad_2]