MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

“Sannu da zuwa” ta fada tana sunkuyar da kanta kasa,
“Yawwa….”
Tsaye suka yi awurin cirko cirko shi dai bai shiga cikiba haka kuma bai koma waje ba,
“Ki shirya jibi zaki je ganin gida……”
Da mamakinsa sai yaga ta dago fuskarta cike da farin ciki ta kalleshi,
“Nagode”
Baice komai ba yajuya yatafi nan tabishi da kallo yauma dai fararen kayanne na gado farar riga t shirt mai gajeren hannu da farin wando,cike da murna taje ta fada saman gado ta rungume pillow cike da farin ciki ranar dai tsabar murna bacci kadan tayi,washe gari kuma ta fara hada kayanta akwati guda kamar wacce zata yi watanni ko shekara,ranar wuni tayi tana fara’a kamar anyi mata albishir da kujerar hajji,
Washe gari da safe bayan Aryan yatafi makaranta itama suka kama hanyar kanon dabo,karfe 11 da kusan rabi suka isa kano ai Hanan kamar zata tashi sama haka take ji dan tsananin farin ciki,
Lokacin da suka je gidansu kaya taga ana ta fitowa dasu ana shigarwa,kayan abinci ne,atamfofi bandir bandir da shaddodi na maza, “wadannan kuma na menene?” Ta tambayi kanta dan Khalil bai fada mata ba,
Da tsallenta da gudunta ta shiga gidan taje ta rungume mamaye tana murna,shamsu dake tsaye shikam matsawa yayi yana fadin,
“A’a karki kada ni ki jamin zama wuri daya”
Bakinta yau yaki rufuwa kuma ta kasa zama wuri daya ta shiga nan ta fita nan haka ta rinka yi saboda bakuwa ta zama agidan,har Abba yadawo bata samu zama ba sai lokacin ne suka zauna,
“Uwar masu gida ina kuma kika baro dan naki Sulaimanu?”
Dariya tayi aranta tana cewa Allah sarki Aryan,
“Abba suna nan lafiya duk suna gaisheku”
Har dare bata san ma’anar wadannan kayan da tazo dasu ba,text tayiwa Khalil tana tambayar shi wad’annan kayan da ya hadota dasu na menene? Sai lokacin ya tuna ashefa baiyi mata bayani ba shi yasaba duk lokacin da Ramlat zata je gida yana yimata tsaraba wadda zata kaiwa yan uwa da abokan arziki, reply ya mayar mata dashi,
_Tsaraba_
Shine kadai abinda ya rubuta,tambayarsa ta sake yi wai to kwana nawa zatayi nan ya dawo mata da reply wai sati daya marairaicewa tayi kamar yana ganinta wai dan Allah tayi sati biyu shi kuma yace A’a,damunsa Aryan yayita yi shi kuma wai zaiyi waya da mommy,saida ya kira masa ita sannan yabarshi,tashi yayi ya wuce bedroom dinshi.
Tana kwance suna shan hirar yaushe gamo da mamaye tana ta zuba shagwaba wai mamaye bata je gidanta ba, gashi ankusa shekara tana cikin yin wannan mitar kira yashigo cikin wayarta nan ta dauka tun kafin tayi magana taji muryar Aryan,
“Hello mommy….”
Murmushi tayi ta amsa masa ko gaisheta baiyi ba yasoma bata labari yadawo daga makaranta umma tabashi abinci yaci kuma yaje islamiyya,uncle yadawo daga office ya kawo masa shawarma da tsire,labarai dai kala kala,
“Ina uncle din yake?”
“Yana daki yace kar na dameshi da surutu”
Dariya tayi saboda abisa dukkan alamu kam Khalil ba mai son hayaniya bane sai wacce ta zama dole shiyasa take mamakin yanda yake yi da bakin matasa a office duk lokacin da suka kawo masa ziyara kila wannan dalilinne yasa baya rabuwa da ciwon kai kullum cikinsa yake,
Sun jima suna waya da Aryan har saida Khalil yafito nan tajiyo muryar shi yana tambayar Aryan wai har yanzu basu gama hirar da mommyn ba?lumshe idanuwa tayi tana murmushi sakamakon jin muryar sa da tayi tasan yanzu yana can sanye da farar t shirt da bakin wando ko fari tunda shigar tashi kenan kullum babu sauyi, sallama sukayi da Aryan ta kashe wayar.
Sabo turken wawa bata taba sanin cewa tayi mugun sabo da gadonta ba sai yau domin kasa bacci tayi sai juye juye kadai taketa faman yi tana tuno abun kaunarta, fuskarsa, muryar shi da dukkan yanda yake gudanar da komai nashi cikin jan aji da nutsuwa, murmushi tayi ta rungume pillow ahankali cikin rada ta furta “I love you minister”……………………鉁嶐煆?
*Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*37*
***Baccin yau tayi shi ne cike da nutsuwa,kewa da kuma shauki,hakanne ma yazama silar faruwar wani mafarki mai dadi acikin baccinta,
Khalil ta gani zaune akan wasu duwatsu agaban bakin wani tafkeken kogi,shi kansa ruwan yana da daukar hankalin duk wani ma’abocin kallonsa ko kuma wanda yasamu kansa a wurin. K’ananan duwatsu yake ta dauka yana cillawa cikin ruwan,yana sanye da farar t shirt da bakin trouser fuskarshi boye cikin bakin gilashin da ya karbeshi yayi masa kyau ainun,ita kuma tana zaune gefe daya can nesa dashi itama sanye cikin farar doguwar riga amma kuma tana ta kuka tsawon lokaci shi kuma yaki ya ko kulata bare ya bata hakuri,
Tsawon wani lokaci bai juya ya ko kalleta ba sai tajiyo wata kara daga bayanta kafin ta juya tuni yayi kukan kura yayi tsalle yazo ya fizgota jikinshi ya rungume yana kakkareta alamar baya son wani abu ya sameta ko ya tabata,zuwa cann bayan dan wani lokaci ya dago kanta yana kallon kwayar idonta sai dai ita bata iya ganin nashi idon sakamakon bakin gilashin dake sanye a fuskar tashi,cikin muryar shi mai taushi da dadin saurare yace,
“Sa’adah…… Kin zaci bana sonki ko?….. Gashi ke kuma kina sona…. Shi so sirri ne dake boye cikin zuciya…… Wani mutumin yana mutukar kaunar ka amma yakan boye hakan acikin ransa batare da ya bayyana maka ba…..”
Sakinta taga yayi ya durkusa akan gwiwowinsa irin yanda indiyawa keyi hannunshi guda daya yakai ya kamo nata yayi kissing dinshi sannan ya bude baki cikin salo mai burgewa yace,
“Nima ina sonki……! I love you sa’adah……”
Wata iskace mai karfi da dadi ta taso wacce ke barazanar yin awon gaba da ita cak taji ya dagata yasata cikin jikinsa ya lullube ta da yalwataccen kirjinsa,
Juyi kawai take yi daga kwancen da take saboda har lokacin cikin mafarki take tana rungume a kirjinsa suna juyawa iska na kadasu tana shakar kamshin jikinsa mai saukar da nutsuwa,
“Hanan….. Hanan….”
Ahankali ta bude idonta nan taga mamaye tsaye da carbi a hannunta gari har yayi haske alamar ta makara,
“Wai kinyi sallah ma kuwa?”
Girgiza kai tayi ta sauka daga kan gadon tana jin wani sabon shaukin kaunarsa acikin zuciyarta. Kamar mahauciya ko sabon kamu haka ta zama ranar domin wuni tayi tana murmushi bata da aiki sai murmushi ita kadai,da zarar ta tuno wannan mafarkin da tayi sai murmushi ya kufce mata haka tayi ta fama tana buri tare da fatan mafarkin ya zama gaske,
Yauma sunyi waya da Aryan kuma sun jima yana yimata surutu dan har da sanar da ita wai Daddy bashi da lafiya yana yin ciwon ido dayake yau khalil da ciwon ido ya tashi gaba daya idanuwan sunyi jajur kuma suna yimasa radadi ga dan kunbura da sukayi,
Bayan sun gama waya da Aryan sun gaisa da umma barira ta katse wayar tana tunanin taya yadace ta duba Khalil? Shin kiransa zatayi ko text massage zata tura masa? Ita fa gaba daya Khalil dinne kunyarsa take ji idan ta tuna irin diban albarkar da tayi masa abaya, shiyasa ba kyau saurin yanke hukunci ita dai gashi yanzu zuciya ta kaita ta barota aruwa,shiru tayi tana nazari to idan ta kirashi me zata ce masa? Kawai gara tayi text din zaifi sauki dama dadin text massage kenan zaka iya fadawa mutum abinda kake so wanda bazaka iya fada ba idan waya kuke, shawarar zuciyarta tabi ta tura masa massage din.