MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

Khalil yana zaune kan gadonsa da laptop a cinyarshi gefe daya kuma Aryan ne shima yayi matashin kai da kafarshi idanuwanshi sanye da farin glass sakonta ya shigo bai samu damar budewa ba saboda yana aikine mai muhimmanci,sai bayan da ya gama ya dauki Aryan yaje ya kwantar dashi a dakinsa ya shiga kitchen ya hado coffee mai zafi sannan ya koma bangaren sa, glass din idonshi yacire saboda dama saboda hasken system din shiyasa yasaka,wayar ya dauka yana zaune kan sofa yana kurbar coffee dinshi bude sakon yayi nan yaga daga Hanan ne wani dan kyakkyawan greeting card pic yagani mai kyau mai dauke da flowers jajaye ajiki sannan anyi rubutu kamar haka,
_If these flowers were wishes, then my wish for you is to get well soon._
Shiru yayi kamar wanda yake kokarin gano wani abu daga jikin sakon zuwa can yasaki ajiyar zuciya sannan yatura mata da reply, _Thanks_,bata damuba saboda dama tasan halinsa sakonshi bai wuce ok, alright, thanks etc.
***
Cike da mamaki sumayya ke kallon mujahid tun bayan da suka kamo hanyar kanon dabo tumbin giwa koda me kazo anfika, Wai yau itace mujahid yaje tahowa da ita takanas har garin katsina,hannu takai kan radio din cikin motar zata kunna,
“Karki kunna min….”
Fasa kunnawa tayi ta kawar da kanta tana hararar gefe,
“Ke haka akeyi sai ki wani taho gida ki nemi wurin zama ki shantake….. Kinma manta da mutane gaba daya”
Sai lokacin ta kalleshi tana kokarin turo masa baki,
“Suwaye mutanen? Mami ce kuma kullum muna gaisawa ta waya”
“Ohh mami kadai kika sani? Idan kika kara turo min bakin nan sai kinga yanda zanyi dake….”
Bata kara magana ba taja mayafi ta rufe fuskarta zatayi bacci,
“Karki yarda kiyi min bacci a mota,ki bude idonki kar ki jamin ace satoki nayi….”
Gaba daya ita mamaki mujahid ke bata wai shine yaketa takalarta da janta da surutu haka mujahid din da ada ko magana tayi masa sai ya gadama yake amsawa idan kuma bai gadama ba harara ce ke rabasu amma wai yau shine keta janta haka,har suka je kano yana janta da magana,agaban wani dan karamin restaurant ya tsaya ya fita yana cewa ta jirashi idan kuma tafito ta bata to babu ruwanshi, murmushi tayi ta dauke kanta bayan wasu yan mintuna yadawo dauke da wata yar kyakkyawar leda wadda aka zubo masa snacks aciki harda drinks guda biyu,
“Amshi kici yar kauye dake kawai….”
“Yan kauye dai”
“Keda wa?” Ya bukata yana kokarin yiwa motar key,
“Nida kai tunda duk tushenmu daya…”
Murmushi yayi ya harareta, “ke dai yarinya”
Lumshe idanuwanta tayi ta jingina da jikin kujera tana yiwa Allah godiya acikin ranta da yakawo mata wannan rana cikin sauki batare da tasha doguwar wahala ba.
***
Kullum sai sunyi waya da Aryan da umma barira haka shima Khalil tana kokarin tura masa massage tana tambayar idanunshi domin har yanzu bai samu lafiya ba sai dai da sauki za ace,
Acikin gidajen dangi da yan uwa da sauran abokan arziki babu inda bata je ba kuma duk inda taje sai takai turamen atamfofi da shadda ita kanta tana jin farin ciki da dadin abinda tayi domin ta dadadawa mutane da yawa ta hanyar basu wannan shaddar da atamfar,gidan anty salaha kuwa kwana biyu tayi acan anty salaha sai mitar uwar ramar da tayi take tayi tana cewa taki ta kwantar da hankalinta ta zauna lafiya agidan mijinta tayi kiba bayan bata rasa komai na jin dadin rayuwa ba idan kuma saboda tsufan minister ne take sawa ranta damuwa ai akwai matan da suka auri mijin da yafi nata tsufa, murmushi Hanan tayi sannan tace,
“Ai anty bama tsoho bane wallahi,matashi ne mai jini ajika son kowa kin wadda ta rasa…. Bari ki ganshi fa”
Hotunanshi da tayi saving a Instagram ta budewa anty salaha ta mika mata wayar tafara gani daya bayan daya,
“Ikon Allah…. Hanan yar baiwa…. Ke yanzu dama wannan balaraben ne mijin naki? Allah mai yadda yaso…. Hanan ki godewa Allah”
Haka anty salaha keta faman santin Khalil ai da taga pic din Aryan sai ta sake rudewa tana cewa sai kace jinin larabawa? Ita dai hanan dariya take yi saboda itama farkon ganinsu tayi wannan santin da rudewar amma ta boyewa anty salaha halin da take ciki na tsananin son Khalil wanda shikuma abisa dukkan alamu bai ma san tanayi ba. Satinta daya agida PA yaje ya daukota kamar yadda Khalil ya fada mata,harda kukanta itada mamaye ita tanayi mamaye nayi, tsakanin d’a da mahaifi,
K’arfe biyar na yamma suka shiga garin Abuja lokacin anyi ruwa an dauke amma garin awadace yake da ni’ima mai yalwa ga iska mai dadi tana kadawa, lumshe ido tayi ta bude lokacin da suka shiga unguwar su tana zaune ta kame a owners corner,unguwar shiru babu hayaniyar komai ga shuke shuke sunyi shar shar luf luf dasu, tangamemen gidansu suka shiga har bakin kofar shiga PA yakaita yayi parking, tunda Aryan ya hangota yabaro malamin islamiyyarshi yataho yana yimata oyoyo karatun da bai koma ba kenan,murna da umma barira da Aryan kamar sayi me saboda gidan duk sororo yayi musu lokacin da bata nan itama umma ba abokin zance sai kayan kallo da radio,har dare suna tare a dakin umma ga tsarabar da ta kawo musu nan iri iri da na ciye ciye da kayan amfanin gida,
Bayan sallar ishah tafito daga wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci blue colour,yau jin kanta take yi wata iska na shigarta sakamakon kitson da tayi kafin ta taho dan rabonta da kitso tun kafin bikinta dan tunda tazo Abuja ba ayi mata kitso ba ita dai umma ita keyi mata tunda ta dan iya, Aryan ne yashigo rike da balloon yana son hurawa ya kasa yabata wai ta hura masa awurin Daddy ya karbo,karba tayi ta kama hannunsa suka koma kasa wurin umma,itace har 12 saura adakin umma suna hira daga k’arshe tayiwa umma sallama ta tashi dama tun dazu takai Aryan dakinshi,
Tun da ta shawo kwana iskar dake kadawa tafara kawo mata kamshinsa cikin hancinta ai kuwa tana taka kafar bene tajiyo takunshi shikuma yana kokarin saukowa,sai da ta lumshe idanuwanta sannan ta budesu daidai lokacin ta hangoshi yana sanye da farar t shirt da bakin dogon wando hannunshi rike da dan karamin coffee flask yana kurba idanuwanshi sanye da bakin glass………………………鉁嶐煆?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM – Ummi Tandama: 38
***Ahankali take hawa steps din shikuma yana saukowa cikin kwarjini da cikar haiba,yana kara dosota kamshinsa na kara kusanto ta kasala na kara lullubeta,
Dan sunkuyar da kanta tayi lokacin da suka zo kusa da juna,
“Ina yini uncle?” Ta fada muryar ta na dan sassarkewa wanda ita kanta ba zatace ga dalili ba kawai dai abinda ta sani shine kusan duk lokacin da zata ganshi to sai ta tsinci kanta cikin wannan halin koma fiye da haka domin nutsuwarta tafiya take tabarta har sai baya nan sannan take dawowa gareta,
“Lafiya lau…. Ya mutanen gida?” Ya amsa yana cigaba da tafiyarsa batare da ya tsaya ba,
“Suna lafiya,ya jiki?”
“Alhamdulillahi….” Yabata amsa lokacin har ya dan gota ta,
“Allah ya kara sauki” Ta sake fada duk da bata da tabbaccin ko zai jiyo abinda ta fada,ahankali taci gaba da tafiya cikin ranta tana jin wani abu yana tsirgawa cikin magudanar jininta,kamar wannan shigar da yayi sak ita taganshi da ita cikin mafarkin da tayi kwanaki biyar da suka wuce,
Bedroom dinta ta shiga ta sulale gefen gado asanyaye ta kwanta tana jin damuwa na lullube farin cikin da take tare dashi yanzu,da ace Khalil na sonta ko yana jin wani abu agame da ita da yanzu suna can tare amma sai dai kash ba itace a gaban sa ba abisa dukkan alamu.