MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

Washe gari haka ta tashi sukuku danma dai online classes dinsu na dan debe mata kewa domin abubuwan da take koya a group din Allah yayi yawa dasu ko a fannin girke girke ta koyi girki kala kala wadanda ba zasu lissafu ba ita kuma dama Allah ya dora mata jarabar son girki dan sam bata ganin wahalar sa amma abun haushi tun da tazo gidan Khalil iya farfesu kawai ta taba girkawa komai kuku ke dafa musu,wuni tayi adaki tana tsara abubuwan da zata bada a sissiyo mata domin hada turaren wanka da humrah wadanda hajja hasinah ta koyar musu,ita nata take son tayi daban mai kamshi na musamman wanda duk wanda yaji zai so,
Zuwa yamma ta bawa Emah driver yatafi kasuwa domin harhado mata kayan,daga nan falon kasa ta zauna wurin umma barira dake zaune tana sakar maficin roba anan take jin wai Khalil yau minna yatafi gaisuwa,dan tabe baki tayi cike da bacin rai amma bata nunuwa umma ba.
Zuwa dare Khalil yadawo kuma yau da wuri yadawo sakamakon takurawar da idonshi yayi masa wani irin radadi da zugi yake yimasa ta ciki,
Yana zaune falonsa jikinsa sanye da jallabiya umma barira da Aryan da Hanan suka shiga domin dubashi,waya suka iske shi yana yi yana cewa,
“Khalid kace mata nifa bana cin mike….. Ehhh…to shikenan muna zuba ido….ok thank you”
Jin sunan wanda ya ambata yasake tabbatar musu cewa da Khalid yake yin waya nan Aryan ya tubure yahau rigimar shi sai anbashi yayi magana dasu Nawwar,mika masa wayar Khalil yayi sannan ya maida hankalinsa ga su Hanan wadanda ke zaune ita umma tana saman kujera ita kuma Hanan tana k’asa kan Rug. Da umma suka fara gaisawa tana tambayar ya idon nashi saboda yau da sassafe yafita, tissue ya yaga yana dan goge idon nashi sannan ya dagosu jajur yana kallon umma ita kuma Hanan tana kallonsa tana ganin yanda idanuwanshi suka yi ja,
“Wallahi umma idonne ma ya takura min nadawo gida amma ban gama aikiba a office kawai dai tahowa nayi…. Ina saka masa magani amma kamar bana sakawa”
“Ai likitan ido ya kamata ka gani mu’azzam…”
“Ai shi nagani umma, Dr Al’amin ne ma ya hada ni dashi…”
Sai da Hanan tajira suka gama da umma sannan ta gaishe shi,sau daya kurum ya kalleta daga nan bai kara ba sun dan jima wurinsa suna hira da umma sannan suka fita,
Washe gari da burin yin aiki ta tashi tana son hada humrah da turaren wanka kuma cikin nasara ta yisu kamar dama can tajima tana yi,gaba daya sashenta gaurayewa yayi da kamshi kamar me ita kanta kamshin take yi saboda kayan hadin da tayi amfani dasu masu kyau ne da tsada sannan ta dan kakkara da wasu turarukan wanda ma hajja hasinah bata saka musu suba, lokacin da ta kammala saida ta yiyyi wa kayan hotuna sannan ta turawa hajja hasinah,kowa na gidan saida ta diba masa ta saka masa acikin toilet daga Aryan har umma har Khalil shi amma Khalil a toilet dinshi na falo ta ajiye masa dan ba taba shiga master bedroom dinshi ma tayiba har yau bata san kalar bedroom dinsa ba ita kuma humrar dama kanta ta hadawa shiyasa bata bawa kowa ba,ji tayi idanuwanta suna yi mata kekayi nan ta sosa kamar kuma dama jira suke suka fara yimata radadi sai kuma hawaye kafin dare itama tuni har ido ya ruruce yahau ciwo ya kada yayi jajur, lokacin da umma tagani cewa tayi to awurin Khalil ta dauka sai akira mata likita itama yadubata, itama tasan awurin nashi ta dauka dama tun lokacin da sukaje falonsa ta kalli kwayar idanuwanshi tafara jin nata kwayar idon suna dan tsikarinta kadan,
Har 12 dare bata yi bacci ba sakamakon ciwon da idanuwanta keyi ganin babu haza yasata yimasa text wai bata da lafiya ciwon ido ke damunta ko zai taimaka ya Kira mata Dr? Reply taga yayi mata da wai tazo,
Tashi tayi ta sauka daga kan gadon ta saka hijabinta da silifas tafita,yana kishingide akan kujera kafarshi daya saman center table yana kallon CNN ta bude kofar ta shiga bakinta dauke da sallama, idanuwanshi akan TV ya amsa batare da ya kalleta ba. Wuri ta samu ta zauna can nesa dashi sosai amma duk da haka sai da hancinsa ya jiyo masa masifaffen kamshin humrar dake tashi jikinta,shiru yayi ya dan lumshe idanuwanshi na dan wani lokaci sannan ya kalleta da lumsassun idanuwanshi wadanda suka kara yin jaa,saurin kawar idonta tayi daga kanshi dan tunda ta zauna take kallonsa kamar zata cinyeshi,
” Me kika ce….?” Taji ya tambayeta bayan ya dauke idonshi daga kanta,
“Idanuwana ke ciwo…” Tabashi amsa tana wasa da bakin hijab din jikinta,
“Me yasamu idon?” Ya sake tambaya,
“Awurinka na dauka…”
Jin abinda tace yasashi daga ido ya kalleta,
“Awurina kuma?”
“Uhmmmm”
Shiru yayi na dan wasu mintuna sannan cikin rashin daga murya taji yace,
“Shiga bedroom dina zaki ga magani ki dauko….”
Har ta mike bata san me ya tuna ba taji yayi saurin cewa,
“Zauna kawai bari in dauko..”
Daga haka yatashi yawuce cikin bedroom dinshi nan tabishi da kallo farar t shirt ce jikinsa da farin wando wanda da kadan yawuce gwiwarsa shima fa ta lura idan yasamu dama akwai gayu idan zai fita ne kullum cikin manyan kaya,
Koda yashiga cikin dakin sai da yatsaya gaban bedside drawer dinshi wanda ke dauke da hoton Aryan da hoton Ramlat cikin wasu frame kanana guda biyu masu kyau,ya dan jima yana duban hoton kamar mai son gano wani abu aciki sannan ya dauki maganin yafita,
Tana zaune inda yatafi ya barta zama yayi saman kujerar da yake zaune tun farko, sannan ya dora mata maganin kan center table din gabanshi,
“Zo ki dauka”
Anutse ta tashi tazo ta dauka tana kallonsa alamun neman karin bayani,
“Ki disa a idon naki idan zaki kwanta”
“To kai kuma fa?” Ta fada muryarta na rawa kamar wacce ke jin tsoron fada,
“Ba matsala kije dashi”
“Nagode,sai da safe”
Kai kurum ya daga mata ta juya ta fita tana jinjina rashin son magana irin na wannan bawan Allah dan idan yana yinta kamar anyi masa dole.
Kamar ciwon idon nasu layi yake bi washe gari shima Aryan yatashi da shi duk idanuwan nashi a like haka suka yita fama har tsawon sati biyu umma ce kadai bata yi wannan ciwon idon nasu ba,
Abangaren abubuwan da take koyo kuwa yanzu tasake bada himma sosai kuma alhamdulillah ta koyi abubuwa masu yawa kuma tana ma kan koyo wani abun burgewa ma shine ta kan jajurce wurin gwada dukkan abun da aka koyar dasu,
Yauma kamar kullum tana zaune falon kasa itada umma kowa yana aikinsa maganin zaman banza,ita umma tana karasa mificin da take sakawa ita kuma Hanan tana sabulun gyaran jiki wanda hajja hasinah ta koyar dasu cikin satin nan,muryar Aryan tajiyo yana ta zuba surutun nashi ko shida waye oho,
“Kinji d’an naki can ko wa ya samo yabaro karatun islamiyyar tashi kuma?” Umma ta fada tana kokarin bantarar goronta,kafin Hanan tayi magana tuni anbude kofa, dukkansu ita da umma d’aga ido sukayi suka mayar da hankalinsu kan wad’anda ke shigowa,Zaid ne rike da trolley yana janta Aryan na biye dashi shida wata kyakkyawar matashiyar mata sai zuba mata surutu yake yi,
Ganinsu yasa umma fadada fara’arta tana fadin lale marhabun da mutanen gombe,itama Hanan ba abarta abaya ba wurin yimusu barka da zuwa,
Kujera duk suka samu suka zazzauna ana kokarin gaisawa,jin muryar matar yasa Hanan dan sake kallonta lokacin da taji umma tace,
“Maamy mutanen London….. Saukar yaushe?”
“Ai zan kai 3 weeks da dawowa…. Koda yaushe Khalil na mitar wai bana zumunci naki zumunci shiyasa shima ya shareni ko Aryan baya kai min to yanzu gani nazo har gida…..”