MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

“Allah sarki ai kuwa kin kyauta…. Sannu da zuwa”
“Ina yini?” Hanan ta fada tana kallon ta,dan murmushi maamy tayi sannan ta amsa cikin fara’a,
“Lafiya lau…. Mun sameku lafiya?”
“Lafiya lau” Hanan ta amsa mata tana tattare kayanta tunda dama ta gama,sama ta haura domin kai kayan bayan sun gaisa da zaid, lokacin da take saukowa tana jiyo muryar Zaid yana cewa umma,
“Ai ni umma kasa gane Anty maamy nayi Yaya Khalil ma nasan dakyar idan zai ganeta dan tafi 4 years rabonta da kasar nan”
Dariya maamy tayi ta cire farin glass din dake idonta,
“Zaid kaima fa baka da dama”
Ita dai hanan samun wuri tayi ta zauna tana kallonsu da sauraren hirar da suke yi yayinda ita kuma Aryan yazo ya haye cinyarta. Kasancewar ga dakuna nan reras agidan daki guda aka warewa anty maamy ta shigar da kayanta lokacin anata kiraye kirayen sallar magriba,suma su Hanan basu zauna ba kowa dakinshi yawuce domin gabatar da salla shikuma Aryan suka fita tare da Zaid,
Hanan bata samu fitowa ba sai bayan sallar ishah saboda tana can dakinta tana chaten da su salaha tana tuttura musu abubuwan da ta gwaggwada na daga cikin wad’anda ta koya,bayan sallar ishah tafita domin cikinta yafara kiran ciroma,tana sanye da dark blue din doguwar riga yar kanti da hijab asama,falon babu kowa hatta umma bata fito ba,zama tayi kan dining bayan ta debi abincin da zata ci,tana tsaka da cin abincinta Zaid suka shigo shida Aryan,suna zama saiga umma itama tafito nan suka cigaba da hirar su suna cin abinci,
K’arfe 9 tabar falon takoma sashenta bata sake fitowa ba sai 11 saura lokacin Khalil yadawo suna can falonshi gaba dayansu harda umma,sashen nashi itama ta nufa jikinta na fitar da wani kamshi mai sanyi,cikin nutsuwa ta bude kofar falon ta shiga abinda idanuwanta suka gane mata shine yasanya ta taji jikinta yayi sanyi cikin rashin kwarin gwiwa ta juya zata koma………………………鉁嶐煆?
_Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:13 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*
*39*
***Muryar umma tajiyo tana kiranta lokacin da take kokarin komawa,
“Sa’adatu ina kuma zakije…..? Ki karaso mana ayi dake”
Babu musu tafasa fita ta shiga,kujera ta samu ta zauna tana kallon kowa, Khalil ne zaune kan doguwar kujera shida Aryan wanda ke bacci akusa dashi sai Anty maamy dake kujerar kusa dashi tana sanye cikin brown colour din doguwar riga sai Zaid dake kujerar kusa da ita amma shi gaba daya hankalinsa yana ga wayar dake hannunsa yana daddannawa ita kuma na zaune opposite dinsu tana kallonsu,akusa da umma Hanan ta zauna tana yiwa Khalil sannu da zuwa sannan tana sake kallon Anty maamy dan sai yanzu ne ma tayi mata kallon tsaf,doguwa ce sosai dan idanma Khalil zai fita tsayi to da kadan zai fita, fatarta mai haske ce sosai wadda hutu da jin dadi suka sake haskaka ta, siririya ce Sam bata da kiba amma fa kuma tana da masifar kyau kamar ita tayi kanta tana da diri da sura,
Hanan wani abu taji ya tsaya mata arai sakamakon murmushin da taga Khalil nayi lokacin da suke yin hira da Mami,
“Maamy uwar son girma…. Wai dan Allah har yanzu baki daina son girman nan ba? Lokacin da kina yarinya fa har kuka kike yi idan akace kece karama acikinmu….”
Wata dariya mai kayatarwa maamy tayi sannan cikin murmushi tace,
“Woohhh Khalil ka iya bada mutane wallahi,yanzu da girmana kake fada min haka agaban Zaid….. Kana gani na kusa diban surukai,sahla fa jss 3 take Jawad jss 2 faruk ne kadai a primary school”
“To kuma shine me? Kaji yarinyar nan da wata magana,to nida Khalid da ace da wuri mukayi aure da ba tuni mun aurar da ‘yaya ba…..”
“To wai Khalil da kai da Khalid din da me kuka fini? How many years kuka ban? Da me kwado yafi gaya ne wai?”
Dariya Khalil yayi yasake kishingida jikin kujera alamar yana jin dadin wannan hirar,
“Wai dan Allah shekararki nawa? Fada min”
“Am 39 by the way….”
“Lallai maamy kina da son shekaru,to yarinya ai ko mu bamuyi 39 ba 38 muke har yanzu…. Ke ai ba zaki fi 36 ba ko 35…”
“Haba haba Ibrahim….haba Ibrahim ya zaka fadi haka? Nice 35 ko 36? Gaskiya nafi haka”
“Au wai ko dan kinga kin hayayyafa kin tara yara shine kike karawa kanki shekaru? Saboda kinga su sahla sun fara girma ko…. To ai ba anan takeba”
Hanan kallonsu kawai take yi dan bata taba sanin cewa Khalil yana iya yin hira doguwa kamar wannan ba sai yau gaskiyar bahaushe da yace kowa da abokin zancensa,yau kam shi cikin nishadi yake da alama dan harda dariya yakeyi Hanan har tambayar kanta take yi wai dama mutumin nan yana hira? Kuma koda wasa bata taba bashi shekaru har 38 ba dan wallahi da za sata agaba ace ta kiyasta shekarunsa da ko tantama bata yi zatace 32 ko 33 domin jikinshi da fuskarshi duk basu nuna yafi hakanba,
“Wai ma yaushe muka daina tsallakar dake kwata ne maamy? Idan kin manta in tuna miki”
“Ibrahim kenan…. Ka manta lokacin da nake tare maka fada ko? Ka manta lokacin?”
Dariya Khalil yayi,
“Gaskiya maamy ki rage son girma dan wallahi duk shekarunki mu dai mun girme miki nida Khalid”
“Da shekara daya da rabin? Shekara daya da rabi ne fa Ibrahim”
“Zan fadawa Khalid ai duk abun da kika ce”
“Shima saida muka yi dashi ai zuwan nan da nayi gidanshi,ku son girma gareku bayan kuma tuni na kwace muku girman,yanzu dole ku bani girmana”
Murmushi Khalil yayi nan suka cigaba da hirar kuruciya har suka gangara suka koma ta duniya su Hanan dai na zaune suna jinsu saida dare ya raba sannan suka fara tafiya daya bayan daya,umma ce ta fara tafiya sannan Zaid,ita kam Hanan tana nan zaune koda za su kwana anan tayi alkawarin sai taga tafiyar maamy sannan zata tafi dan haka kawai taji bata jin dadin yanda Khalil yasake yabiye maamy suna hira duk da tasan yar uwarsa ce amma bata san ta ina suka haduba kuma da alama tare suka yi kuruciya suka tashi tare dan har hirar zuwa makaranta lokacin da suna kanana sukayi. Bayan fitar anty maamy itama tashi tayi ta dauki Aryan tafita sai da tafara kaishi dakinshi tukunna sannan ta wuce nata,bata san dalili ba amma baccinta kadan tayi ko me yasa oho kuma saida ma tajima kafin ta samu ya dauketa saboda tana ta tunane tunane marassa amfani zuciyarta sai faman sake baci take yi,
Washe gari haka ta tashi shima babu walwala ahaka ta shirya Aryan sannan takoma part dinta bayan yatafi makaranta,wanka itama tayi ta shirya cikin atamfa exclusive riga da skirt sannan tasha humrarta da sauran turarurruka masu dadi,fita tayi dan ta sauka k’asa tana fitowa ta hango anty maamy ta glass ta nufi part din Khalil, kamar ta bita amma sai ta nufi kasa tana duba agogon dake daure a hannunta karfe 9 saura wasu mintuna,
A babban falo ta iske umma da Zaid na kokarin yin breakfast Zaid rike da waya a hannunshi yana sakale da earpiece, gaisheta yayi duk da ahaife kamar zai girme mata amma dai yana bata girmanta,ruwan tea kawai ya hada da sauran kayan soye soyen da John yayi ya dauka yawuce dakinsa dake nan k’asa.