Uncategorized

MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

Kallon umma barira Hanan tayi bayan Zaid yatashi,

“Umma ina kwana? Ya gajiyar zama wuri daya?”

“Alhamdulillahi Sa’adatu,ya akaji da dawainiyar gida da kulawa da Sulaimanu?”

Murmushi Hanan tayi amma batace komai ba, hira suka cigaba dayi ita da umma jifa jifa har sukaji alamun saukowar Khalil,tare suka jero shida anty maamy wacce ke sanye da doguwar riga ta bacci ta yafa babban mayafi shi kam farin tsadadden boyel ne ajikinsa wanda yasake fito dashi dass kuma ya amsheshi,

Tun kafin ya karaso kamshinsa yafara karasowa, Hanan tun bayan kallo daya da tayi musu bata kara sake kallon su ba,tana ji suna gaisawa da umma yana sanar mata da wai Legos zaije amma by flight kuma insha Allah ayau zai dawo,

“Ranka yadade wannan charger din abar min mana sai ka nemo wata….” Anty maamy tafada tana daga charger din dake hannunta,

“Kinma isa….. Aro nabaki kina gamawa ki mayar min”

“Dan Allah ka nemo wata Ibrahim..”

“A’a indai bada a nemo miki,amma nidai ki mayar min”

“To babu matsala…., Allah yatsare saika dawo”

Har tajuya zata tafi ta sake dawowa,

“Am Khalil dan Allah acikin motocin gidan nan za a ara min daya inaso zan fita anjima….zanje gidan wata friend dita”

“Babu matsala ki fadawa Zaid sai ya d’auko miki….”

Daga haka yafita itama ta wuce daki, Hanan dai sama sama ta yi breakfast dinnan ta tashi ta koma part dinta wanda ita kanta bata san abinda ke damunta ba,

Tunda ta kule acikin part dinta bata fito ba sai la’asar iya umma kadai ce agidan da ta tambayi umma su Zaid fa sai tace ai tun dawowar Aryan suka fita su uku har Aryan din da anty maamy saboda dama yau babu islamiyya tunda alhamis ce,bata kara magana ba taje ta zubo sakwara da miyar egusi ta dawo ta zauna,

“Wai umma meye dangantakar Abban Aryan da anty maamy?”

“Kakanninsu daya,da uban maamy da uban Khalil ai uwa daya uba daya suke…. Dukkaninsu ‘yayan moddibo ne,Asalinsu, Ibrahim moddibo haifafen garin Billiri ne dake nan gombe sana’arshi a wannan zamani kiwo domin Allah ya hore masa dabbobi masu tarin yawa kusan yana daya daga cikin mutanen da ake lissafawa wadanda keda tarin arziki a wannan karnin domin yana da yawan shanu,tumaki, da kuma jakuna,matarsa daya maryo da yara hudu Sulaiman shine dan fari sai Idris dake bi masa sannan sai mariya sai kuma karamarsu muzayya,

Duk cikar gombe da batsewarta babu wanda bai san moddibo ba domin mutum ne sananne kuma malami domin lokacin da yaransa suka fara girma yabaro Billiri yadawo cikin garin gombe da zama nan yasake bude tsangayarsa inda almajirai ke taruwa suna karatu,anan ‘yayansa duka suka yi karatu na allo da na zamani amma na allon yafi yawa dan iya Idris ne kadai yasamu nasarar yin karatun boko mai yawa amma yayansa Sulaimanu shi iyakacinsa primary,

Anan cikin gombe duk sukayi aure shi Sulaimanu yar gidan sarauta ya aura yar sarki gaba da baya wacce take sonsa dalilin zuwa fada da suke yi tare da mahaifin sa moddibo saboda aminin sarki ne a wancan lokaci dan shine limamin gidan sarki ma ko ina sarki zaije suna tare to kinji inda ita zaituna suka hadu da Sulaimanu mahaifin mijinki har akayi aure kuma aka samesu su biyar da saude dashi ibrahim mijinki da Lubnah da Humaida da kuma zaidu mai sunan kakan hajiya zaituna wato sarki zaidu na uku,Shi kuwa Idris can yawon karatunsa a k’asar borno ya samo tasa matar labibah wacce ta kasance shuwah wanda ana kyautata zaton ma asalinsu larabawan sudan ne zama yakawo su nan k’asar maiduguri suka zo suka zauna,bayan andaura musu aure nan gombe suka dawo suma suka zauna ga dakin zaituna ga na labibah kowacce tana zaune da mijinta lafiya,kuma yanda kan mazajensu yake ahade haka suma suka hada kansu kin san zama irin na da ya banbanta da na yanzu,ita zaituna duk da kasancewar ta yar sarki jikar sarki bata dauki girman kai ta dorawa kanta ba tare suke yin girki da sauran aikin gida ita da labibah har Allah yabawa kowaccensu rabo bayan zaituna ta yaye babbar yarta ta farko saude na biyunne sukayi rainon ciki lokaci daya dan kusan tare suka haihu tsiran na kwana biyar ne kowaccensu ta haifi danta namiji kuma duk aka saka musu sunan moddibo wato ibrahim amma shi Khalil da yake shine babba shi sai moddibo yasa masa Khalil shikuma dayan Khalid to tare suka taso suka yi wasan kasa suka yi komai da kika sani tare shekararsu daya da watanni biyar labibah ta haifi maamy to itace aka sakawa sunan maryo mahaifiyar su Sulaimanu shine suke kiranta da maamy,itama acikinsu Khalil ta taso tare suka tashi har girma,to da yake kin san shi Idris yayi karatun zamani babu laifi to shine yashiga siyasa ka’in da na’in kuma da Allah ya dafa masa sai yasamu karbuwa,jinin moddibo akwai albarka kowa yana son Idris dan har mukamin governor yarike kuma shine yajawo Khalil ajikinsa yadorashi shima aharkar siyasar duk da shi Khalil din bawai dan yana da sha’awar hakanba dan har commissioner na yada labarai yayi masa lokacin mulkinsa shekararsa hudu yana rike da commissioner na yada labarai matasa da wasanni saboda abinda yakaranta kenan a makaranta,to lokacin da aka gyara kundin tsarin mulki akace anbawa yan k’asa da shekara 40 damar rike mukamin ministoci saboda suma yara zasu iya a lokacin Alhaji Idris yatura Khalil kuma da yake Allah ya tsaga da rabonsa kin ganshi nan sai yasamu dan yanzu akalla ba a kasaru ba mun shafe fiye da shekara biyu a nan kadanne bai karasa uku ba,maamy yar uwarsa ce sosai yaranta uku amma yanzu babu auren dan tafi shekara uku ma bata tare da mijinta, zawarci take yi…..”

Ajiyar zuciya Hanan ta sauke bayan umma ta kammala bata tarihin su Khalil,to ita yanzu me yadace tayi? Ta ina yadace tafara? Wanne mataki yakamata ta dauka……………………….??鉁嶐煆?

*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎

8/14/20, 10:14 AM – Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.*

*40*

       ***Sakin fuskarta tayi bata bari umma barira tagane komai ba dan bata nuna mata cewa tana tare da damuwa ba,har magriba suna tare da umma suna shan hira da yake umman gwanar hira ce,suna kokarin tashi su shiga salla su Anty maamy suka dawo tana rike da hannun Aryan wanda keta tsallen rashin ji,

Damm Hanan tayi tana kallon anty maamy wacce ta hade cikin bakar riga gown mai stones ta dan yafa mayafin rigar akanta kuma hakan ba karamin kyau yayi mata ba sai dai ko hassada irin ta mai ita,

Sannu da zuwa suka yimusu Hanan bata jira komai ba ta tashi ta hau sama tare da Aryan,bayan sun idar da salla acikin dakinta Aryan sai labari yaketa bata na unguwar da suka je dan har abokan wasa yasamu agidan shiyasa fitar tasu tayi masa dadi ita dai hanan saurarenshi take tana jinjina kai amma idan taga fitar tana neman tayi yawa to zata sanarwa ubanshi dan babu abinda yayi mata zafi kar abu yafaru Khalil yazo yana ganin laifinta saboda shi ba sakaka yake bari ana fitar masa da yaro ba dan kullum ma sai yayi wannan takarar yanzu ne ma ya hakura ya daina,

Sai bayan da tayi sallar ishah sannan ta fito nan ta iske umma da su Zaid ana shan hira harda anty maamy,itama zama tayi akayi da ita sune har wurin 11 dan saida Khalil yadawo tukunna sannan hirar ta tashi. Haka dai aka cigaba da lallabawa Zaid kam tuni yakoma gombe yabar anty maamy wanda hakan gaskiya bai yiwa Hanan dadiba domin bata son zaman anty maamy atare dasu bawai dan kasancewar ta bazawara ba a’a sai dan zata rusa mata target dinta,zata bata mata plan dinta,ahalin yanzu ita babban burinta shine ta yanda zata ja mijinta ajiki su shirya yasaki jiki da ita suyi rayuwa irin ta ko wanne ma’aurata shiyasa zaman anty maamy atare dasu kamar karan tsaye ne agareta, gashi kullum suna tare da Khalil idan har yana gida sai dai idan baya nan amma idan yana gida zaka samesu zaune shida maamy suna hira har abinci maamy ke zubo musu tare amma kowa da flate dinsa hakan ba karamin bawa Hanan haushi yake ba,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button