MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

Yau ma suna zaune a falonshi misalin karfe 10 na dare sai hira suke yi da maamy hirar sharrin da yesmin tayi masa yana bata labarin irin yanda kotu ta wankeshi dan ankusa kawo karshen k’arar,
Dariya maamy tayi sannan cikin tsokana tace,
“To kai ka aureta mana….”. Dan rausayar da kai yayi yana wasa da wayar hannunshi,
“Nida ke waye yafi dacewa yayi aure yanzu? Ke yakamata kiyi aure ai maamy”
Dan murmushi mai ban sha’awa tayi sannan ta kalleshi,
“Aure fa kace Khalil….. Hmmm aiki jaa”
“Ba wani aiki ja,kawai acikin zawarawan nan naki ki bawa wani dama,in bahaka ba ni sai infito”
Dariya maamy tayi harda rike ciki,
“To dama dama kai din….. Zaka iya fitowa”
Duk da awasa suka yi maganar sai kuma sannu ahankali take shirin fara zama babba, Hanan bata da masaniyar hakan amma jikinta yana bata kamar akwai wani abu tsakaninsu,
Shi Khalil rabonshi da soyayya ko wani abu mai kama da haka tun Ramlat tana raye,wata kulawa ta musamman maamy ke bashi ko office yafita tana dan yawan kiranshi awaya suna hira tayi masa fatan alkhairi kuma idanma basu samu damar yin wayar ba to tana tura masa da text message idan kuma yadawo gida zasu kasance tare suna hira amma aboye kamar soyayya suke yi saboda dama tun asali tun kuruciya maamy budurwarsa ce itace budurwarsa tafarko a tarihin rayuwarsa irin saurayi da budurwar nan na wasa dan ko abu yaci sai ya rage mata, Khalid kuwa bai isa ya tabata agabanshi ba dan baya mantawa sunsha kai ruwa rana akan hakan sunsha dambe da Khalid akanta idan ya mareta ko ya daketa to lokacin da yake da wuri ake yiwa yara mata aure shiyasa aka aurar da ita dan shi lokacin bai isa aureba kuma iyaye ma basu san sunayi ba amma da ansani ta yuyu asamu mafita lokacin,
Tuna hakan da yayi sai yaga ai gara kawai ya komawa maamy domin dama can akwai tsohuwar soyayya kuma ita ba karamar yarinya bace bare suyi ta samun sabani,da hankalinta tasan menene aure kuma ta san yanda zata zauna dashi da irin kulawar da yadace tabashi,dari bisa dari yaji zuciyarshi ta gamsu da hakan,bai fito fili ya fadawa maamy abinda ke cikin ranshi ba itama haka amma dai suna dan nunawa juna alamu ko kunyar fitowa su sanarwa da junansu sirrin zuciyoyin nasu suke yi oho. Hanan gaba daya ta susuce ta sake tsangwamar kanta sai kara lalacewa take yi dayake ita budurwa ba kamar bazawara ba ai wayon ma ba daya bane haka sanin sharruda da ka’idojin auren ma duk ba daya bane,ita abinda ke sake daga mata hankali shine irin yanda Khalil da maamy suka dinke har wani fita suke yi tare,idan zaije office tace zata bishi akwai inda zasu sauketa tace zataje saloon abubuwa dai iri iri,gaba daya hanan bata da kwanciyar hankali,
Yauma asama ta samesu falonshi suna hira da system akan cinyarshi maamy na zaune kujerar dab dashi irin zaman masoya dinnan,wani abune ya tokare kirjin Hanan rufe idonta tayi taje ta zauna akan kujerar da yake zaune akai ya tankwashe kafarshi daya akan kujerar dayar kuma tana kasa,sanye yake da fararen kananan kaya jeans da t shirt fuskarshi tasha kyau kamar ya shafa mai da powder,
Bata taba sanin cewa zata iya haka ba sai yau saboda Khalil din kwarjini yake yimata dari dari take yi dashi,bata taba attempting zama kusa dashi irin wannan ba sai yau,zama tayi gefen shi gata gashi jikinsu na gogar juna hannunta kan tafin kafarshi dake lankwashe amma wannan bata saniba ta zaci jikin kujerar ne,
Juyawa yayi shima ya kalleta da mamaki acikin ransa, idanuwanshi kuma na nuna neman Karin bayani tunda watakila da abinda tazo fada masa tunda har tayi irin wannan zaman,
“Uncle….. Banda lafiya”
Ta fada tana marerecewa saboda tana masifar jin haushin lankwasa murya da anty maamy keyi idan tana yimasa magana kuma bata son zaman nan da sukeyi tare akujeru makusantan juna,tunda ita matarsa ce ai game din tazo da sauki ita zata iya yimasa abinda ita maamy bata isa tayi ba idanma ta gwada yi to shari’a ce zata hau kanta,
Katse abinda yake yi yayi ya kalleta cikin sanyin muryar sa yace,
“Me ya sameki?”
Dan jimm tayi saboda ta rasa karyar da zata yi masa zuwa can ta tuno da datsewar da Aryan yayiwa dan yatsanta tun shekaran jiya ajikin kofar bathroom dinshi amma bawani sosai bane sai dai wurin ya kunbura kuma yaji ciwo,yatsan ta mika masa tana cewa,
“Ka gani…. Datsewa nayi jikin kofa”
Zai iya cewa this is the second time da ya taba riketa nafarko lokacin da glass ya fashe ya watsu ajikinta sai wannan na yanzu,jan dan yatsan yayi cikin sauri ta shige jikinsa domin wani irin azababben radadi taji kamar yatsan zai cire dan saida tayi nadamar nuna masa,yana kara ja tana sake shiga jikinsa dan har jefar masa da laptop tayi kasa, tsakaninta da Allah take yin kukan da take yi saboda zafi abunka da yan auta shagwababbu kuma sakalai LoL….. Maamy yi tayi kamar bata gansu ba,da yake akwai shekaru da kuma wayewa sai kawai ta mike fuskarta awashe tace,
“Khalil bari inje in kwanta kaina ciwo yake yi yau banyi baccin rana ba,see you tomorrow”
Yana rike da hannun Hanan wacce ke cukwikwiye ajikinsa ya kalli maamy,
“Yau da wuri haka? Alright Allah yabaki lafiya, Allah ya kaimu goben,saida safe”
Anty maamy bata kara cewa komai ba haka bata kallesu ba ta wuce ta fita,maida kallonsa yayi kan Hanan wacce ke sharbar kuka kamar yana kwakwale mata ido,
“Targade fa kika yi….”
Dago jajayen idanuwanta tayi ta kalleshi haba gaskiya mana taji ciwon yaki wucewa kuma bata iya amfani da yatsan,
“Gobe da safe zan fadawa nura ya samo miki mai gyara sai agyara….”
D’aga kai tayi amma takasa ko kwakkwaran motsi domin bata son matsawa daga jikinsa ji take inama zata tabbata ahaka,
“To dagani…..” Taji yafada yana kokarin dauko system dinshi dake kasa,
Kunya ce taji ta lullube ta nan ta matsa tana rufe idanuwa da tafukan hannunta,duk da ba hira suke yi ba amma sai da takai 12 saura a wajensa sannan ta tashi ta tafi ta kwanta,kasa baccinma tayi dan haka ta kunna data ta shiga WhatsApp,sakon hajja hasinah tagani ta private tana tambayarta lafiya kuwa 2 days ta daina participating a group? Dan duk abinda za ayi da tana cikin sahun yan gaba gaba masu gwadawa da kuma bada himma amma yanzu shiru kamar bata nan,bata da kawaye na jiki ko aminiya wanda zata fada mata damuwarta anty salaha kuma idan ta fada mata fadane zata sha shi kamar babu gobe har ta goda Allah,anty badi’a kuma yanzu bata da waya a hannunta shiyasa ta yanke shawarar sanar da hajja hasinah watakila zata taimaka mata da shawarwarin da suka dace,nan tayi mata voice note ta tura mata ta zayyane mata matsalar da take tare da ita sannan ta kare maganar da fadin,
“Nikuma wallahi anty ina sonshi tun ranar da na fara ganinsa to kuma shi baya sona hankalinsa da tunaninsa na ga matacciyar matarsa,ga wannan anty maamy din tazo duk tana neman kankane min miji dan Allah kibani shawara”
Kashe data dinta tayi bayan tagama yiwa hajja hasinah bayanin komai,daga nan tayi addu’a ta kwanta.
Shi kuwa Khalil bayan yashiga bedroom zai kwanta da misalin karfe 1 miss called din maamy yagani,bai kiraba saboda yasan yanzu kila tayi bacci,kwanciya yayi ya lumshe idanuwansa,ya kamata kawai ya auri maamy domin rabonshi da wata ya mace shekaru kusan bakwai bayan kuma yana da cikakkiyar lafiya sannan sau da dama halin bukatuwar yana damunsa yana takura masa yana hanashi sakat gara kawai yayi auren ai arashin uwa akanyi uwar daki,insha Allah cikin kwanakin nan zai fasawa maamy sirrin dake ranshi.