MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

Da asubah bayan Hanan ta idar da salla take ganin sakon hajja hasinah inda itama ta turo mata da voice note kuma har lokacin tana online,budewa tayi tafara saurara,
“Hanan naji sakonki kuma matsalar ki matsala ce babba kuma ba babba ba,tun farko sakacinki yajawo haka…. Ai baka sallama namiji musamman ma miji irin naki,maza da ake rikesu hannu bibbiyu gudun kada su zame, gaskiya kinyi kuskure babba amma akwai abubuwan da idan kinyi zaki iya gyarasu watakila amma fa dole sai kin dage,sai kuma kin mike tsaye kinyi iyakar iyawarki,yanzu da farko dole sai kin kula da abincin sa,sai kin kula da al’amuransa na yau da kullum sannan uwa uba shimfidarsa wanda wannan shine matakin karshe….. Ki fara sanin wanene ma shi tukunna? Me yafi so? Wadanne abinci yafi so? Me yafi burgeshi? Wacce irin hira ke sakashi nishadi?, Me yafi daukar hankalinsa? Wadannan sune assignment dinki ayanzu kuma sune zaki nemo dan ta nanne kadai zaki samu solution,dan haka ina yimiki fatan nasara dan daga yanzu dinnan zaki fara…..”
Wata iska mai zafi hanan ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya lallai kam wannan babban assignment aka bata mai chaja kwakwalwa da sata nazari gamida tunani,to yanzu ta ina yadace tafara…………………………鉁嶐煆?
*_Ummi Shatu_*馃憣馃徎
8/14/20, 10:14 AM – Ummi Tandama: *41*
***Tafi mintuna goma zaune batare da tasan ta ina yadace tafara ba ganin wankin hula na shirin kaita tsakar dare yasata mikewa daga zaunen da take ta cire hijabin jikinta tafita tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki, kitchen dinta da ke makare da kaya wanda musamman aka tanada dominta a matsayinta na matar gida tayiwa tsinke, to yanzu ita me zata dafa tunda takamaimai bata da masaniyar me yafi so yaci da safe? Amma dai wallahi hajja hasinah ta hadata da assignment me zafi,
Tana nan tsaye harabar kitchen din tana tunanin me yadace dabara ta fado mata,gwara kawai tayi abincin kala biyu daya na gargajiya daya kuma na zamani inyaso duk wanda taga yaci to shi yafi so,
Hakan kuwa tayi nan ta zage ta soma girkinta cikin jin dadi da farin ciki domin girki yana daya daga cikin abubuwan da ke sakata nishadi a lokacin da take gabatar dashi,wainar semovita tayi za aci da suga kuma abarta tayi kyau kamar ta shinkafa tayi laushi libis sai kunun gyada da ta dama haka kuma ta soya dankali da sos wadda taji kwai nasha nasha,
Agaugauce ta je ta shirya Aryan bayan tagama aikin danma dai ba wani mai yawa tayiba shiyasa bai dauki dogon lokaci ba,tana gama shirya Aryan ta kamo hannunshi suka sauko kasa wanda tuni kuku yajima da shirya table, breakfast ta bashi yaci sannan ta shirya masa lunch box dinsa yatafi,yana tafiya takoma sama ta shiga wanka shima bata zauna tajima acikiba tayi tafito aranta tana jinjina kokarin iyaye mata musamman wadanda suka tara ‘yaya ko kuma haihuwar tayi musu sammako,ka kula da yara sannan ka kula da ubansu kai gaskiya isn’t easy,shiryawa tayi batare da bata lokaci ba cikin orange colour din atamfa mai bala’in kyau,dinkin fitted ne shiyasa yayi mata tsantsam ajikinta,bata yi wani dogon lissafi ba wurin kalmasa dan kwalinta ba kawai dan cokara shi tayi tafita kuma hakan sai yabada style mai kyau,
Yau kam ta shirya baiwa Khalil surprise dan duk abubuwan da ta dafa kwasarsu tayi ta kai sashensa ta jejjera bisa table din cin abinci sannan ta nemi wuri ta zauna nan cikin falon, agogon hannunta ta kalla bayan ta zauna karfe 8 saura mintuna biyar,kai amma gaskiya tayi kokari kuma aikin nata ma yayi sauri sosai,yau kam sai dai anty maamy tazo ta isketa duk sammakonta ehe.
Bata jima zaune afalon ba taji alamun bude kofa, kamshinsa ne yafara sanar da ita fitowarshi kafin shi din ya bayyana,sanye yake cikin farin yadi na maza dandakeke mai mutukar kyau mai laushi shara shara, yana tafe yana kokarin balle hannun rigarshi,mamaki yaji ya kamashi kwarai da gaske sakamakon ganinta da yayi zaune cikin falon,mikewa tsaye tayi daga zaunen da take alamar girmamawa,
Da idonsa yake neman karin bayanin ganinta da yayi a daidai wannan lokaci,kasa tayi da kanta ta dan duka ta gaisheshi,
“Ina kwana?”
“Lafiya lau…”
Ya amsa mata idanuwanshi na kaiwa kan dining, warmers yagani jere akai da sauran kayan karin kumallo,agogon hannunshi ya kalla sannan ya dan yi guntun tsakin da bata san dalilinsa ba,
“Waye ya kawo wancan abincin?” Ya bukata batare da ya kalleta ba domin hankalinsa na kan wayar dake hannunsa,
“Nice…..” Ta bashi amsa cike da kwarin gwiwa domin ta dauri aniyar canja komai a tsakaninsu,
Bai kara magana ba ya nufi saman kujera ya zauna yana ta danne dannen waya da alama wani yake nema amma wayar taki shiga dan sai dan guntun tsaki yake ta ja yana kara wayar a kunnensa,zuwa caan taji yafara magana fada fada,
“Wai ina kaje ne inata kiran wayarka tun asubah amma taki shiga?…….. Kana jina…… Ya isa…… Yanzu yanzun nan katashi kaje store ka dauki abinci ka kai gidan yaran nan…….. Abincinsu yakare tun jiya……. Kawai ka wani kashe waya tun 11 ana ta nemanka wayarka akashe…….. Ka tashi yanzu kaje karka bata min lokaci….”
Daga haka ya cire wayar daga kunnenshi yana jin kamar an dauke masa wani nauyi dake kansa, haba har ya dan ji sanyi amma ace anbar yara marayu babu abinci ai akwai matsala,ita dai hanan ba gane kan zancen nashi tayi ba saboda bata san da wanda yake wayar ba kuma bata san akan wanene ba,
Ta glass ta hango anty maamy na tahowa hannunta rike da karamin flask din coffee zata kawowa Khalil mikewa tsamm Hanan tayi ta koma kusa dashi aranta tana cewa ai kuwa yau sai dai ayi wacce za ayi amma Khalil bazai sha wannan coffee dinba breakfast din da ta kawo masa zai ci,
“Ga breakfast din can kar ya huce…….” Ta fada cikin marereta, baice komai ba kuma bai tashi ba yaci gaba da danne dannen wayarshi, falon shiru baka jin sautin komai sai kukan dawisu dake tashi daga bayan dakin baccinsa,ahaka anty maamy tashigo nan Hanan ta dan sake matsawa dab dashi wanda har sai da hakan yaso batawa anty maamy rai,
Fuskarta babu yabo babu fallasa ta karasa cikin falon tana dan basarwa,sanye take da doguwar riga ta material multi colour rigar mai burmemen hannu ta yafa siririn bakin mayafi akanta, karasawa tayi ta zauna kujerar gefensu,
“Ibrahim har kafito kenan…..”
Daga ido yayi ya kalleta,
“Maamy….. Kin tashi lafiya…. Wallahi nafito….. Zanje kwara state ne”
“Allah ya kiyaye hanya….”
Ajiye masa flask din tayi agabansa,
“Ga coffee din…”
“Ok thank you…. Sai dai ma nafita dashi office nasha acan”
Hanan na jinsu batace ko uffan ba kuma da yake yau yan rashin kirkin na kusa ko gaida anty maamy bata yiba sai wani daddauke kai take yi ita ala dole ankula mijinta,
“Me da me aka kawo kan table din can?” Taji Khalil yana tambayar ta,wata irin mikewa tayi babu zato yaji ta kamo hannunsa mai tsananin taushi,
“Uncle kazo ka gani mana……. Kai fa na dafawa”
Ba Khalil ba ita kanta anty maamy saida taji mamakin wannan lamari,jingina tayi jikin kujera yanda zata cigaba da kallon scene din da kyau,
Duk da baya wani sakar mata fuska mikewa yayi yabi bayanta zuwa kan dining din wanda har lokacin tana rike da hannunshi,wani irin shock take ji kamar anjona mata electric amma ta kasa sakinsa har sai da ya zauna saman table din,