Uncategorized

MIJIN MATACCIYA Page 41 to 50

Tea yace ta hada masa rabin cup amma ganin kunun gyadar da tayi sai yace tabar tea din ta zuba masa kunun,da kunun da waina ta saka masa yaci sai wani kwarkwasa take yi wanda hakan ke baiwa anty maamy dariya, lallai yaro yaro ne,yaran yanzu akwai rawar kai da feleke ita ala dole mai miji sai wani karairaya take yi mijin da ba ma lallai ta burgeshi ba,mikewa tsaye anty maamy tayi domin ta gaji da kallon dramar tasu,

“Ibrahim bari naje na kwanta…. Zamuyi waya anjima”

“Ok mammy thank you”

Fita tayi Hanan tabita da harara aranta tana cewa ai wayar ma insha Allah baza ayita ba,shi kam har ga Allah yaji dadin waina da kunun da yasha haba amma ace kullum tea tea babu wani canji,mikewa yayi yawuce cikin bedroom dinshi tana ganin haka tayi wuff ta mike taje ta dauki flask din coffee din da anty maamy ta kawo taje ta tuttuleshi cikin sink din dake dinning area din,

Fitowa yayi tsaf cikin shirinsa na fita sai zuba kamshi yake yi,tsaye take hannuwanta abaya tana wasa dasu,

“Amm…….. Am nace…… Maganar mai gyaran targaden da kace…..”

Shiru ya dan yi na dan wani lokaci kafin ya daga ido ya kalli side din da take,

“Za aturo shi….”

“Nagode….. Adawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya….”

“Amin,nagode” Ya fada a takaice sannan yawuce zai fita har yaje bakin kofa yajiyo,

“Yawwa bani wannan flask din wanda maamy ta kawo min coffee”

Dauka tayi ta nufeshi ta mika masa batare da ta nuna wata alama ba wacce zai sa ya zargi tana da masaniya akai,hannu yasa ya karba sai kuma yaji empty,dan jijjigawa yayi yana son ya tabbatar da abinda yaji nan kuwa yaji wayam babu komai,

“Ya najishi empty??” Ya fada ahankali amma kasancewar akusa take dashi taji abinda yace,

“To ko dai dama bata saka maka komai ciki ba?” Ita kanta ta san wannan tambayar da tayi masa ta rainin hankali ce, baice mata komai ba ya mika mata flask din yawuce yafita tana biye dashi abaya kamar wata bodyguard,sai da ta rakashi har kasa suka gaisa da umma barira sannan yafita,sai lokacin tajuya ta koma sama saboda dama bata son ya hadu da anty maamy ne a kasa shiyasa ta zame masa jela,

Falonshi ta gyara masa ta tsaftace shi tas amma bata yi garajen shigar masa cikin bedroom ba,sai dai amma abinda yakama tun daga kan falonshi zuwa bathroom din dake cikin falon da sauran lungu da sako dake harabar sashen nasa duk ta samu nasarar kalkalesu tsaf,

Bayan ta gama gyara nata sashen kasa ta sauka wurin umma wacce ke kishingide a d’akinta,anty maamy kuma na falo tana rike da novel na turanci tana karantawa, tsaki Hanan tayi aranta tace to ko me anty maamy din take jira da taki tafiya ta share daki ta zauna? Shifa Zaid kwata kwata ma kwananshi biyu ya tafi amma ita anty maamy taki tafiya koda yake ai gidan dan uwanta ne ta sake fadin hakan acikin ranta,dakin umma ta shiga bayan ta shigar musu da sauran kayan breakfast din da Khalil yarage,

Zama tayi suka fara cin wainar da ta yiwa Khalil itada umma,umma na sake kara mata haske akan irin kalolin girke girken da Khalil yafi so wanda shi yafi son abincin gargajiya dan bai ki ya yi breakfast da dumamen tuwo ba ko koko da kosai watikil wannan ne dalilin da yasa bai cika cin abinci ba yake zama da yunwa saboda su ma’aikatan gidan sunfi maida hankali wurin girke girken zamani,murna tayi sosai saboda jin wannan daddadan labari daga bakin umma.

Bayan mai gyaran targade yazo yayi mata sama ta koma ta shiga dakinta ta samu dan karamin littafinta da biro ta soma tsara jaddawalin girke girken da zata rinka yi asati duk na gargajiya amma zata dan rinka hadawa da na zamani shima ba wani mai yawa ba,bayan tagama kwanciyar ta tayi ta huta har azahar tana kwance,bayan ta idar da salla sai maganar anty maamy ta fado mata wacce tayiwa Khalil da safe wai sai sunyi waya,

Wayarta ta jawo ta shiga ta tura masa massage tunda dai ita bazata iya kiranba domin koda ta kirashi bata san abinda zata ce masa ba.

Khalil na zaune tare da mukaddashin mai girma gwamnan jihar kwara sakon Hanan yashigo,

_Uncle ya hanya? Ya aiki? Allah yataimaka ya tsareka ya dawo mana dakai gida lafiya._

Mamaki da al’ajabi sakon Hanan suka bashi,to wannan yarinyar lafiyar ta kuwa? Domin daga jiya zuwa yau gaba daya ta sake canjawa fiye da da,sai kace ba itace ta rufe ido a kwanakin baya ta rinka yimasa ruwan tijara da rashin kunya ba,to yanzu kuma ko me ya canjata? Oho,

Reply ya tura mata kamar yanda yasaba da Thanks kawai sannan yaci gaba da harkokinsa.

Hanan kuwa sai la’asar ta shiga kitchen ta shirya lafiyayyen tuwon semovita dinta miyar ganye, sannan ta sake dama kunun gyada wanda yasha lemon tsami sai kamshi yake,

Bayan tagama Aryan taja suka tafi garden suka haye lilo nan suka shantake har magriba sannan suka shiga cikin gida,anty maamy ce kadai a falon kasa tana daddanna waya,ganin Aryan yasata kiransa ita kuma Hanan ta wuce sama bata bi ta kansu ba,salla tayi bayan ta idar ta yi zamanta a daki tana kallon wani kayataccen labari mai dogon zango na hausa,anan Aryan yazo ya sameta suka cigaba da kallon tare.

Misalin karfe 9 Khalil yashigo gidan,babu wanda yasan ma yadawo,wanka yafara yi,yafito yana shiryawa anty maamy ta kirashi,dauka yayi yana tsane jikinsa da dan karamin towel,

“Hello…. Ka shigo ne?”

“Hy mimimi……”

Murmushi anty maamy tayi ta shafi gashin kanta dake bude tana kwance saman gado,

“Kai baka rabo da tsokana Ibrahim,ka dawo dinne?”

“Ehh…. yanzun nan nashigo nayi wanka”

“Ok….to ya? Zamu je dinne?”

“Uhmm bari na shirya,bani 10 minutes”

“Ok”

Katse wayar yayi yaci gaba da shiryawa,mintuna kadan ya karasa shiryawa bama zaka taba ganewa shi bane sai dai idan kayi masa kyakkyawan sani,

Itama Anty maamy dan sake gyarawa tayi sannan ta fito,da motarshi sukayi amfani suka fita PA yana jansu yayinda su kuma suka kame agidan baya bodyguards dinshi na biye dasu,

Wani Park suka je kayatacce ma’abocin sanyi da sanya nutsuwa,zama sukayi suna fuskantar juna da wani dan table a tsakiyar su,

“Maamy….” Yakira sunanta cikin taushin murya,daga idonta tayi ta kalleshi fuskarta cike da annuri,

“Khalil….”

“Maamy bazan boye miki sirrin dake cikin zuciya ta ba….. Ni dake ina kyautata zaton duk abu iri daya muke ji agame da juna…..”

Dan murmushi tayi sannan ta tallafi kumatunta da hannunta guda daya tana kallonsa,

“Amma wai me ya rabaki da uban yayanki? Saboda a iya sanina dake ke macece mai hakuri though dai zaman aure yana da banbanci da kowanne irin zama”

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta dan lumshe idanuwanta ta budesu akansa,

“Khalil mahaifiyar shi ce ta rabamu,bata sona aduk shekarun da muka shafe tare da danta,ni babu abinda ya hadani da Bilal….. Mahaifiyar shi ce bata kaunata kuma ta sanadiyyar ta nabar gidan”

Jijjiga kai yayi sannan yayi murmushi mai dauke hankali,

“To insha Allah yanzu zaki samu uwar mijin da take ji dake take kaunarki kamar ranta…… Maamy shin zaki iya karasa sauran kwanakin da suka rage miki a duniya tare dani?”

Duk da tajima tana zargin jin wad’annan kalaman daga bakinsa amma bata tsammaci zata jisu da gardi da zaki irin haka ba,

Rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta cikin farin ciki tana jin iska na kadata kamar tana yawo cikin gajimare,

“Woww…….. Khalil….. Wadanne irin dadadan kalamai ne wadannan? Wow…..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button