Uncategorized

MUSAYAR RUHI 1-2

Shiko Hammat yanada Zafin zuciya sosai ga kafiya akan duk wani ra’ayi nashi bairagama kowaba cikin masarautar kaf se mahaifiyar shi da mahaifin shi yatsani soyayya koda bata  tsakanin mace da namiji bace duk wani abu wanda zaiso bayasonshi sabida bai yarda da wata soyayya ba seta tsakanin iyayen shi amma yagasgata yanason abu 1 tsananin so makuwa wato D’an uwan shi Hamut yanajidashi sosai kamar ranshi shine kad’e yakesashi yayi abu koda baiyi niyyaba yasashi yabari koda kuwa yakafe akan abun kowa  acikin masarautar yana jin tsoran Hammat hatta su hajiya Mariya dan take zeyima rashin kunya idan Sarki Jabir yayi magana yabar cikin masarautar natsawon lokaci har se Sarki Jabir yaje yadawo dashi sabida baya iya jure rashin shi a cikin masarautar idan kuwa yadawo tofa kowa yashiga uku cikin gidan yadinga jamusu masifa kenan wajan sarki shidin  Soldier ne me babban matsayi baya had’a hanya damace komi kyanta ko matsayinta sabida yatsani mata sede mahaifiyar shi kawai Sarki Jabir yaso suyi aure lokaci d’aya amma ina sabida shi Hammat yace bashida ra’ayin hakan cikin ranshi dole akabarshi 

Da Hamut d Hammat suna tsananin kama idan suka jero tare baka’iya ganesu sabida komi nasu iri d’ayane tsayinsu farinsu komi se abu 2 wanda yabanbantasu halinsu tawani ‘bangaran se yanayin idanun  su Hamut yanada manyan idanu masu d’aukar hankali farare ne tas shima Hammat idanunshi manyane masu saka sakka da fargaba acikin duk wani sassan wanda yayi tozali dasu amma shi blue eye gareshi sewani ratsin fari Wanda yazagaye black din cikin idon nashi wannan kenan 

Sosai akeyin hidima cikin wannan katafariyar masarautar dagani kasan bikin d’an gatane jiniyar isowar motocin Hammat yasa kowa yashiga cikin hankalin shi daga hadimai har dogarawa masu tsara wajan walima kuwa kowa tsayawa yayi sabida wasu sunyi zaton Angon ne kimanin motoci 7 ne suka danno kai cikin katafariyar harabar cikin masarautar kowacce akwai tambarin sunan Yarima Hammat jikin number motocin itako wadda yake ciki akwai tambarin STARS guda 2 a jikin motar se ‘yar qaramar tutar Nigeria ajikin gaban motar 

Cikin sauri sauran soldier suka fito suka bud’e mishi murfin motar kowannensu yana riqe da bindiga kamar zasu yaqi idon shi sanye da baqin glass fuskar nan tashi amatuqar tamke wani irin tsaki yaja yakwantar dakanshi jikin kujerar babu alamar zaima fito

Tsayin lokaci sannan yafito yadubi inda ake shirya kayan walimar yaja tsaki yanufi cikin masarautar part d’in mahaifiyar shi yashiga yana shiga Hanan tayi saurin miqewa tace ” barka dashigowa yaya Hammat ” wani irin mugun kallo yawatsa mata hakan yasata saurin barin Parlour nufar bedroom d’in hajiya kilishi yayi yana shiga yahangi Hamidat da wasu daga cikin qawayenta zaune saman wata lallausar darduma gabansu da fruit kalakala sosai yaji ranshi yayi mugun ‘baci yaja tsaki yafita boko amsa gaisuwarsuba yana fitowa yacikaro da Hajiya kilishi duban ta yayi fuska babu walwala yace 

” Haba Ammi mekuma wannan yarinyar takeyi cikin masarautar nan ayau inace segobene za’a d’aura auran shine tawani zo tun yau ” murmushi Hajiya kilishi tayi takama hannunshi tazaunar dashi tace ” Huseen kenan to ay haka al’adar masarautar taku take kafin d’aura aure ake d’akko amarya balle wannan datake yar gida kagama tunda kadawo shikenan sekahalarci wajan walimar kaida amaryar bro d’in naka tunda kaga shi bayanan ” jin haka yasa Hammat sake tamke fuska sosai had’ida maida tabaran shi yamiqe yace ” Ammi tofa inde danine sede afasayin wannan walimar subari segobe idan bro na yadawo ” daga haka yasakai yafita mirmushi Hajiya kilishi tayi tace ” Huseen kenan uban rigima ” 

Haka kuwa akayi walimar batare da Hammat yako leqa wajanba washe gari har misalin 02:20 amma Hamut bai’iso ba kuma yakira tun dare yace jirginsu yataso gashi d’aura auran 02:30 ne dole akad’aura aure batareda Ango ya’iso ba a’bangaran su Hamut kuwa hazone yahana jirgin nasu sauka sefaman shawagi sukeyi ganin haka yasa Hamut saka rigar iska maisaukar lema d’aurawani yayi saman kujerarshi yamusu sallama yadiro daga sama yakusa isowa babu zato yayi ido hud’u dawata qatuwar bishiya kafin yayi wani yunquri yadaki wannan bishiyar saurin yin baya yayi dakanshi dakuma girjinshi hakan yasa qugunshi da cikinshi suka bugu sosai wani irin mugun ciwon ciki dana mara yaji alokaci d’aya qarasa fad’uwa qasa yayi cikin tsananin azaba yashigayin salati ciro wayar shi yayi cikin qarfin hali yakira Hammat yasanar dashi abinda yafaru dakuma Inda yake kafin wani lokaci sukazo babu jira akasureshi zuwa asibiti kowa hankalinshi amatuqar tashe Sarki Jabir Hajiya kilishi hajiya Fulani da mahaifiyar Hamidat wato Momcy se mahaifin Hamidat su hajiya Mariya kuwa suna gida suna addu’ar Allah yasa Hamut yamutu tsayin lokaci sannan doctor yafito duban su yayi cikin damuwa yace 

” Maimartaba muje office muyi magana ” cikin tashin hankali Sarki jabir yace ” nan duk iyayenshine kafadi meye matsalar ” ajiyar zuciya doctor yayi yace ” gaskiya Maimartaba Hamut yagamuda muguwar jarabawar ubangiji yasamu babbar matsala wadda tsakaninshi da mace sede kallo sabida bazai iya sauke haqqin aure wajan saduwaba sakamakon buguwar dayayi aguqunshi dakuma cibiyarshi yajawo mutuqar wasu jijiyoyi bance bazai warkeba har abada sabida komi yanagun Allah to amma dakamar wuya mude anan bazamu iyaba kuma bana tunanin akwai wani doctor dazai iya sede nace kuyimai addu’a ” saga haka doctor yabar gurin cikin damuwa ta’be baki Momcy tayi tace ” tab lalle ayko yazamadole yasakarmin ‘ya bazai yiwu tazauna da mace ba ” kallon mamaki kowa yabita dashi 

 

_Marmyn Zarah CE_ ????????????????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button