MUSAYAR RUHI 15-16

“Abokina ashe kayi aure shine babu sanarwa haka wannan baby maizafi haka ? ” kafin Hamut yayi magana Hamidat tayi saurin karyar damurya tace ” ina ay yaya Hamut bai shiryayin aure ba ay dakaji nid’in qanwarshice tajini ” miqamishi cup din ruwan kayan itatuwa tayi had’ida sauke mishi wani irin mayen kallo sannan takoma tazauna tana fesin dinshi binta dakallo Muhseen yayi yanajin wani irin yanayi nadaban duban Hamut yayi yasaki murmushi yace
” abokina inacikifa ” murmushin yaqe Hamut yayi yace ” ay babu matsala idan har ta’amince zanyi magana da’ita komi kenan zakaji ” mido dubanshi yayi kan Hamidat yace ” baby d’an bamu waje kad’an ” miqewa Hamidat tayi takoma ciki bayan tavar parlour Muhseen yadubi Hamut yace ” gaskiya abokina inason wannan qanwar taka amma sede akwai matsala dad d’ina yamaqale akan dole sena auri wata kucakar yarinya nikuma wallahi banaso kagama shiyasa nayi tahowata nan Ummy na tace nabar qasar kawai dan Allah kayimin jagora na auri sis d’inka batare dasanin iyayenaba ”
Nisawa Hamut yayi sosai cikin zuciyar shi yanajin zafi sosai wai yau shine wani yake mai maganar auran matarshi wadda yake tsananin so maganar Muhseen tadawo dashi cikin wannan tunanin saurin dedeta natsuwarshi yayi yace
” karkadamu zanyi tunani akan hakan ” hira sukacigabadayi segaf da magrip sannan Muhseen yabar gidan misalin 10pm Hamidat tashiga cikin bedroom d’in Hamut zaune yake saman abun sallah yayi jigum yanacikin matsananciyar damuwa ta’be baki tayi sannan tazauna tace ” wai kai yaya Hamut maiye nufinka aykai gabama takaika tunda ga abokinka yanason aurena kuma gashi bayaso kowa nashi yasani kaga shikenan kaima seka’boyema kowa shikenan sirri kan sirri kenan ham……..” dakatar da’ita Hamut yayi cikin zafin rai
” ke Hamidat dakata kibar ganin inakauda kaina akan duk wani abun dakikeso sabida inasonkine kawai dakuma darajar yan’uwantaka amma badan hakaba datuni najima damantawa dake seme dan kowa yaji lalurata aybanine nad’aurama kainaba Allah ne kuma in sha Allah zai yayemin nibazan goyi bayan wannan shirmanba amma zanbaki za’bi idan bazaki’iya zamadaniba har zuwa lokacin da Allah zaibani lafiya to nabaki dama dakinemi saki daga gareni nikuma zansakeki kinemi wani mijin wanda zai’iya yimiki maganin wannan jarabar taki ”
Shewa Hamidat tayi tace ” gara kasakeni zefimin zaman jiran tsammani ” sosai Hamut yaji kanshi yashiga sarawa kamar zaifad’i dubanta yayi sosai da idanunshi wa’inda sukayi jajur yace tabbas zanyimiki abunda kikeso amma bazan sakeki ananba kibari semunkoma Nigeria in sha Allah zanmayar dake gabansu dady amatsayin qanwa ba mata ba ” wani irin tsaki taja tace ” hmmm ina sauraranka ” daga haka tajuya tabar cikin bedroom d’in tana fita Hamut yadafe kanshi babu zato yaji wasu irin hawaye suna gangarowa daga idanunshi cikin rawar murya yashiga cewa ” ya Allah kaine kajarafceni dawannan lalurar inaroqonka daka yayemin ya Allah kabani lafiya kabani ikon cinye wannan jaraftar taka ” kuka yaci qarfinshi babu abinda yake tashi se sautin kukanshi kawai a wannan daran ko runtsawa baiyiba yana saman abin sallah yana gayama Allah damuwarshi
NIGERIA
Afusace hajiya wato mahaifiyar Sarki Jabir tanufi cikin parlour Maimartaba kishin gid’e yake Ammi tana daga gefanshi suna hira gabansu kayan marmarine kala kala tana shiga tanemi guri tazauna fuskarnan tata atamke tadubesu tace
” garama danasameku kuduka anan kai Jabir inaso kacire wannan qudirin naka nacewa wai Hammat zai auri Hanan sam hakan bazai ta’ba yiyuwaba sabida bazan yadda jikana ya auri tsintatciyar mageba babu tabbas d’in cewa Hanan marainiyace wama yasani ko cikin shege iyayenta sukayi suka jefar da’ita aka kaita gidan marayu shine ku kuka jajibo ko harma kuke shirin had’ata aure dajikana mai cikakken asali ko to banyardaba bakuma zanyardaba kunji nagayamuku kusamu wani can irinta kuhad’asu ”
Ajiyar zuciya mainauyi Sarki Jabir yasauke yace ” Allah yahuci zuciyarki ya mahaifiyata amma wayene yace zamuhad’a Hammat da Hanan aure ? nide banyi wannan maganar dakowaba amma kuma Hajiya ay baikamata ace munware Hanan cikin zuri’ar muba sabida idan akaduba bamakowane yasan cewa Hanan ba ‘yata bace tamkar jinina takefa hj…….” toni nasani idan kowa baisan cewa Hanan ba jininkabace toni nasani kuma bazan ta’ba yarda agur’batamin zuri’aba ” nagamayin magana ” daga haka tamiqe tabar parlour kallon juna sukayi sosai Ammi taji zuciyarta tayi babu dad’i kafin sarki jabir yace komi tamiqe tace ” matsalar gidan saurauta kenan gulmar tsiya koda cikin uwar d’akinka zakashiga kayi magana se’ansamu waniyaji tabbas idan Hanan bata auri Hammat ko Hamut ba zuciyata zatadauwama cikin qunci babu ruwana da yadda Hanan tazo gareni har abada mai cikakken asali nike kallonta idan hajiya tahana d’aya dagacikin yarana auran Hanan in sha Allah Allah zaimaye mata gurbi da wanda yafisu alkairi agareta ” daga haka tabar part din cikin damuwa
MARMYN ZARAH CE ????????????????