MUSAYAR RUHI 17-18

*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*
*NA*
*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_
“`LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE“`
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
- *3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI….*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*
AND NOW
“`MUSAYAR RUHI“`
*_____________________________________*
*????????AINUWA ????RITER’S✍????*
*????SSOCIATION????????*
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*PG 17 & 18*
*S* osai Sarki Jabir yaji babu dad’i cikin zuciyar shi to amma yaya zaiyi da hukuncin da Hajiya tazartar sede yana jinjina wani lamari kiran wayar Hammat yashigayi bugu 2 yad’aga gaidashi yayi cikin yanayinshi narashin son magana sannan yayi shiru yanajiran yaji abunda mahaifin nashi zaice cikin dakakkiyar murya yace
” Hammat inaso kajini dakyau kuma duk abinda zancemaka ayanzu babu shawara aciki umarnine kawai nasan harzuwa yanzu bakafidda matar aure ba don haka inaso kanemi izini wajan manyanka nawajan ayki kataho gida inaso kaje wajan hajiya bayan kadawo kasanar da’ita cewa kanabuqatar auran Hanan kuma inaso ka kafe akan haka idan kaine babu shakka zata amince Hammat kasani umarni nike baka ba shawaraba ”
Kafin Hammat yace wani abu tuni Sarki Jabir yadatse kiran wurgi Hammat yayi dawayar cikin mugun ‘bacinrai yace
” tabb lalle ni Hammat nine zan auri wannan qaramar yarinyar hmm lalle Hanan anashirin sakaki cikin wahala tabbas zanyi yadda kace maimartaba amma sekowa yayi nadamar wannan had’in ”
TURKEYA
Tsayin kwanaki 4 kenan dafaruwar wannan lamarin ga Hanan tun daga wannan lokaci tasake zama shiru batadawani kuzari kullum cikin damuwa kamar kullum safiya suna waya da Ammi cikin damuwa Ammi take tambayarta lafiya kuwa ” Hanan tabbas kinacikin damuwa nifa mahaifiyarkice idan banji damuwarkiba waye zeji ko asuman takice take neman tashi ? ko’inzone ? ”
Jin haka yasa Hanan qaqalo murmushi mai sauti tace ” a a Ammi babu abinda yakedamuna karatune kawai kuma babu wata damuwa nasamu sauqin asuman sosai sabida inashan magungunana akan qa’ida ” ajiyar zuciya Ammi tasauke tace ” masha Allah in sha Allah kinatare danasara aduk inda kike Hanan kinji kidage akan karatunki sannan inasake sanar dake dakuma jan hankalinki akan kitsare mutuncinki idan kikayimin haka tabbas kinyimin halacci arayuwa ina alfahari dake Hanan auta ta ” wani irin kuka Hanan taji yakwace mata sabida maganar Ammi cikin qarfin hali tadake harsukagama wayar bayan sungama kukan da Hanan take riqewa yakwace mata tunanin halin datake ciki ayanzu tashigayi afili tashiga furtacewa ” tabbas kacutar dani komawaye kai bazan ta’ba yafemakaba har abada in sha Allah se Allah yasakamin mugu azzalumi dawane idon zandubi Ammi nasanar da’ita cewa anyimin wannan muguwar illar ya Allah kakawomi d’auki da mafita cikin rayuwata ” sosai take kuka marar sauti tsayin lokaci dandanan wani irin mugun ciwon kai da zazza’bi yakamata hakan yasa tamiqe zuwa saman bed takwanta sosai tatakure tana tanarawar sanyi hatta haqoranta had’uwa sukeyi sabida tsabar mugun sanyin datakeji cikin shigar qananun kaya kasancewar qasar ma’abociyar sanyice Fadila tafito daga bedroom nufar bedroom d’in Hanan tayi tana shiga tahangeta saman bed qudundine sefaman rawar sanyi takeyi cikin sauri taqarasa gareta hawa saman bed d’in tayi tashiga tambayarta maikedamunta jin yadda jikinta yayi zafi sosai yasa Fadila sake rud’ewa wayar hannunta tashiga latsawa tana qoqarin kiran doctor ganin haka yasa Hanan saurin riqe hannunta cikin raunin murya tace
” a a Fadila banaso kikiramin doctor kibani magani kawai nasha ” girgiza kai Fadila tayi tace ” a a Hanan gaskiya gara akira doctor kusan kwana nawa inalure dake bakida lafiya amma kinqi yarda akira doctor kibari akirashi ” sake girgiza kai tayi tace ” a a Fadila inada tabbacin idan doctor yadubani to tabbas se Ammi tasan banida lafiya idan kuma tasani hankalinta tashi zaiyi banaso nahana zucuyarta natsauwa kibarashi kinji dan Allah zansha magani kawai in sha Allah zanji sauqi idan baisaukaba semukirashi kinji ”
Jinjina kai Fadila tayi sannan tasauka taje takawomata magani tasha babu jimawa bacci mai nauyi yakwasheta
NIGERIA
misalin 5pm jiniyar motocin Hammat suka fara karad’e cikin masarautar kafin kace mai tuni kowa yafara shiga tetayinshi anayin parking baijira anbud’emai murfin qofar motar ba yabud’eta afusace yafito cikin sauri dogarawa suka shiga yimai kirari cikin tsawa yace ” ya’isa!!!!!!! ” babu shiri sukadakata takuyafarayi cikin izza da’isa cak yaja yatsaya yad’an juya kad’an yadubi masu takemai baya fuskarnan tamke yace ” banabuqatar kowa ” jin haka yasa dole kowa yajuya qarasawa ciki yayi kai tsaye part d’in hajiya yanufa yana shiga kuyangun dake yimata hidima sukashiga gaidashi cikin tsawa yace ” banason ganin kowa cikin part d’innan kowayafita ” jin haka yasa sukafara fita cikin sauri tashi zaune Hajiya tayi tasaki murmushi tace
” maraba da Soja kaga mazan fama jarumi agida jarumi a daji zaki kake bakason raini duk wani maqiyi dayaganka yakeshiga cikin tetayinshi tabbas yau nasan akwai abunda yake tafe dakai mai mahimmanci zauna soja naji damuwarka kuma nayima magani cikin ikon Allah ”
Zama yayi fuska babu annuri yadubeta yace ” kaka inaso nayi aure…..” Kafin yaqarasa hajiya tarangad’a gud’a tashiga fad’in Allah nagode maka Hammat yau kaine kake fad’i kanason kayi aure lalle komawacece wannan zataga gata daga gareni ‘yar gidan wacece ” sake tamke fuska yayi yace ” Hanan ce ” zaro ido Hajiya tayi takasa koda qyafta ido ganin haka yasa Hammat miqewa cikin sauri Hajiya tace ” amma Hammat duk matan dake cikin d’angi karasa matar aure se Hanan dadai zai yiyu daka nemi wata ”
Wani irin haushi yasake taso mushi sabida tabbas abinda kaka tafad’a shikam agareshi dedene badan bin uwamarnin Ammi ba dababu abinda zaijamai auran Hanan dakewa yayi yace ” inda zai yiyu kikace Kaka nide ita nace idan kuma kince a a to tabbas banajin zanyi aure har abada ” cikin sauri hajiya tace ” a a a ina ay koda banason abu idan har kanaso tokam zansoshi fiye dakomai yanzu gayamin yaushe kakeso asaka lokacin bikin ? ” cikin ‘bacin rai yace ” duk lokacin dayayi muku ” daga haka yasakai yafita part d’in Ammi yanufa yana shiga yazauna saman cushion kasancewar Ammin bata parlour sosai yakejin zafin wannan lamarin cikin zuciyar shi amma yasha alwashin kasa Hanan sabida tasanadinta akasashi yayi abinda bai shiryaba sallamar Ammi tasa Hammat duban hanyar parlour ganinshi yasa tasaki murmushi had’ida qarasowa tana zama yashiga gaidata cikin girmamawa cikin farinciki Ammi take amshawa sannan tace
” tabbas Husain kanuna kai d’ane mai biyayya agareni in sha Allah zakaga haske cikin rayuwarka yaya kukayi da Hajiya ? ” rumtse ido yayi yaja iska yafesar sannan yace ” ta’amince ” wani irin murmushin farinciki Ammi tasaki tashiga saka mishi albarka kafin wani lokaci tacikamishi gabanshi da nau’ikan abinci kala kala baiwanici sosai ba yamiqe yabar part d’in wannan daran Hammat baccin qunci yayi sabida yanaganin shikam ancutar dashi washegari misalin 10am Hajiya tasa akakirawomata kowa zuwa cikin babban parlour ta bayan kowa yazauna tafarayin magana kamar haka