Uncategorized

MUSAYAR RUHI 21-22

 *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

               *NA*

      *NPEEDY A AJI* 

 _(MARMIY ZARAH CE)_

“`LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE“`

*1. NAYI RAYUWA DASHI*

*2. SANADIN ACCIDENT*

*3. SAKAYYAR CUTA*

*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*

*5. MUGUN SARTSE*

*6. FURUCI….*

*7. JUYI BIYU*

*8. HAYATUL MAHAYAT*

        AND NOW

“`MUSAYAR RUHI“`

*_____________________________________*

 *????????AINUWA ????RITER’S✍????*

*????SSOCIATION????????*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

 *Pg 21 & 22*

*S* osai Hanan takeyin kuka kamar ranta zaifita numfashintane yafarayin sama alamar asumarta zata tashi yunqurawa tayi daniyyar tashi tad’akko Inhelar ta amma ina sema sake jitayi numafashin nata yasakeyin sama sosai dede lokacin Ammi tashigo ganin halin da Hanan take ciki yasata qarasawa cikin tashin hankali Fadila dake bayan Ammi ta’idasa shiga aguje nufar wordrop d’in jikin bed tad’akko mata Inhelar ta cikin sauri Ammi takafamata ita itama Hanan d’in cikin sauri tafarayin amfani da’ita zuwa can lumfashin nata yafara dedeta ajiyar zuciya kawai take saukewa fuskarta dukta kumbura tayi jah sabida jarfatarta  ajiyar zuciya kawai take saukewa rungumeta Ammi tayi tanacigaba da lallashinta sosai Ammi takejin tausayin Hanan 

Washegari bayan sungama breakfast Ammi tadubi Hanan tace 

” Hanan inaso kisanar dani gaskiyar abinda yake cikin zuciyar ki kisani bazanyimiki doleba idan har bakison auran Husain kisanar dani Hanan ke amanace agareni idan kika cutu bazan yafemakaina ba Hanan zan dauwama cikin baq’in ciki sanar dani Hanan ” 

Hawayen dake shirin zubowa cikin idanunta tayi qoqarin mayer dasu cikin raunin murya tace ” a a Ammi  bakiyimin doleba hasalima gata kikayimin har abada banida wata uwa seke babu cutarwa a tsakanin uwa da ‘ya dan Allah Ammi kidena fad’in haka abunda yasani cikin tashin hankali Ammi shine tayarda najicewa bakece mahaifiyataba narasa uwa irinki Ammi zuciyata tashiga cikin damuwar tunanin ina iyayena maiye dalilinsu nakaini gidan marayu Ammi inajin tsoron kar’ace nid’in ba’yar hal…….” 

Dakatar da’ita Ammi tayi dafad’in ” karki furta Hanan inaji araina in sha Allah ked’in ‘yar  halakce gaba da baya kinji Hanan kidenafad’in cewa kinrasani a matsayin uwa  zansake fad’a  har abada banida wata ‘yah mace aduniya seke Hanan ” 

Hawayen da Hanan take ‘boyewa suka silalo saman kyakkaywan kuncinta cikin sauri Ammi tasa hannu tasharemata tarungumota dede lokacin Fadila tafito tsaf cikin shirin tafiya skul ganin haka yasa Hanan saurin miqewa tanufi bedroom tashirya sutafi kwanan Ammi 5 takoma Nigeria seda ta tabbatar Hanan tasaki ranta sosai sannan tabar qasar  bayan tafiyar Ammi Hanan takoma cikin qunci fiye da dah dama sabida Ammin ne yasatake daurewa kullum  Fadila cikin lallashin Hanan takeyi sabida itama lamarin yagirgizata dan ko amafarki  batayi tunanin cewa ba Ammi ce tahaifi Hanan ba gakuma wani  babban tashin hankalin shine auran yaya Hammat balle tasan yatsani Hanan gurin kowa bashida sauqi cikin lokaci kad’an Hanan tayiwata muguwar rama kamar wadda tayi shekara tana jinya abubuwa ukun nan sunsata cikin tashin hankalin dababu misali lamarin fyad’en da’akayimata batason kowayeba ga jin wannan mugun labarin nacewa ba Ammice mahaifiyartaba ga wani tashin hankalin na auran yaya Hammat kuka sosai Hanan takeyi cikin kukan take fad’in 

” nashiga uku yaya zanyi da rayuwata wane matsayi nike cikin ‘ya’ya masu cikakken asali tayaya zan’iya zamada yaya Hammat amtsayin miji dawane baki zanfahimtar dashi cewa fyad’e akayimin wazance yayimin kenan banida mafita ya Allah banida dabara da mafita akan wannan lamarin agareka namika kaina tunba yauba inaneman d’auki da agaji agareka ya Allah ”  sosai takeyin kuka hatta muryarta tadishe 

Allah sarki Hanan gaskiya kinacikin matsala 

Akwana atashi yau bikin Hanan da Hammat garage saura 1 week yaune su Hanan suka  sauka Nigeria cikin tsananin fargaba da bugun zuciya Hanan take ciki Fadila kuwa sefaman tausarta takeyi sabida yadda taga hankalinta yasake tashi sosai girjinsu yanasauka Fadila tamiqe ganin  Hanan batada niyyar tashi yasa Fadila takamo Hannunta d’an zabura Hanan tayi sabida tatafi duniyar tunani bamatasan jirgin yatsayaba takowa sukayi ahankali sunariqe  da hannun juna suna idasa fitowa Hanan tahangi Ammi cikin sauri taqarasa rungumesu Ammi tayi cikin farinciki cikin kissa Jakadiya taqaraso garesu jawo Hanan tayi jikinta tace 

” Amaryarmu barka da dawowa Nigeria zomuje ga motar  Angonki can tamusamman dayabada ad’akkoki gaskiya kinyi sa’ar miji inama munsan cikakken asalinki ? ” qasa qasa tayi maganar yadda babu Wanda zejita se Hanan d’in sosai maganar jakadiya taduki zuciyar Hanan wasu irin hawaye sukashiga gangarowa daga cikin idanunta saurin shanyesu tayi sabida kar Ammi tagani babu jimawa datsayawar jirginsu Hanan su Hamut ma suka diro Nigeria sosai Ammi tatsurame ido tunkafin yaqaraso gareta sosai taga yayi wata irin muguwar rama itako Hamidat tayiwani kyau sosai taqarayin haske saura gaf suqaraso wani irin jiri yakwashi Hamidat tafad’i cikin gigita Ammi da jakadiya dasauran masu tarbarsu sukayi kanta cikin sauri akasureta daga nan se Asibiti duk dasu Hanan tsayin lokaci doctor yanadubata kafin yafito dubansu yayi yace ”  ina mijinta ? ” cikin sanyin murya Hamut yace ” gani doctor miqame hannu yayi sukayi musabaha yace ” inatayaka murna matarka tanada ciki kimanin wasu satittika ” zaro ido Hamut yayi had’ida dafe girjinshi sabida yadda zuciyar shi tayi wani irin mugun bugu 

Tofa 

Marmyn zarah ce

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button