Uncategorized

MUSAYAR RUHI 23-24

 *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

               *NA*

      *NPEEDY A AJI* 

 _(MARMIY ZARAH CE)_

“`LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE“`

*1. NAYI RAYUWA DASHI*

*2. SANADIN ACCIDENT*

*3. SAKAYYAR CUTA*

*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*

*5. MUGUN SARTSE*

*6. FURUCI….*

*7. JUYI BIYU*

*8. HAYATUL MAHAYAT*

        AND NOW

“`MUSAYAR RUHI“`

*_____________________________________*

 *????????AINUWA ????RITER’S✍????*

*????SSOCIATION????????*

 “`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

 *PG 23  & 24*

*G* anin haka yasa kowa yamaido duban shi kan Hamut ganin haka yasa Hamut sauke ajiyar zuciya yace 

” Alhamdulillah ina matuqar farinciki da wannan albishir doctor Allah yaraba lafiya murna sauran jama’a sukashigayi su Jakadiya kuwa jitayi kamar tatashi sama takoma gida  dan sanar dasu Hajiya  hajara Hajiya Fulani kuwa sosai tashigayin murna sabida batasan maike wakanaba itako Hajiya kilishi murmushin yaqe kawai takeyi sabida tanada tabbacin wannan cikin bana Hamut bane shima Hamut d’in yaqen kawai yakeyi dukda wani irin ciwo da zuciyarshi tafarayi babu jimawa sosai akabata sallama had’ida magungunna da shawarwari suna isa gida  akashiga murnar dawowarsu Sarki Jabir dakanshi yafito zuwa harabar masarautar sabida farincikin dawowar su Hanan cikin sauri Hajiya taqaraso rungume Hanan tayi cikin taushin murya tashiga cewa 

” barkanki da isowa matar Soja tabbas kinzama mace mai sa’a arayuwa kinzama matar jarumi kuma sadauki dukkin kere sauran mata kinyi gudun wuce sa’a Hanan inatayaki murna ” 

Sosai Hajiya kilishi da Sarki Jabir da Hajiya Fulani sukayi farincikin jin wannan kalaman na Kaka wucewa tayi da ita zuwa part d’inta kuyangu suka take mata baya anayimata kirari Hamut kuwa tuni yabar harabar wajan part d’in Ammi yashiga kai tsaye yanufi bedroom kwanciya yayi saman bed d’in Ammi idanunshi nakallon sama wasu irin hawaye suka shiga gangaro mai tagefan fuskarshi sosai yake kuka hannun shi yad’aura saman kirjinshi dede setin zuciyar shi yadafe sabida yadda yajejin ciwo cikin zuciyar shi matsananci itako Hamidat tuni tanufi part d’insu had’ida rakiyar kuyangu da Hajiya Fulani wadda tariqeta sabida doctor yace jikin nata babu qwari jakadiya kuwa tuni tanufi cikin masarautar dan fad’in abindake ranta jiki babu qarfi Hajiya kilishi tanufi part d’inta tana shiga tun a parlour tafarajiyo sautin shasshekar Hamut cikin bedroom cikin sauri taqarasa ciki ganin yadda yakeyin kuka sosai yasata saurin zama d’aga kanshi tayi tad’aura saman cinyarta cire hannunshi tayi daga saman qirjinshi tad’aura nata d’ayan hannun nata tashiga sharemai hawayen fuskarshi addu’a tashiga yimai tsayin lokaci sannan yafara sauke ajiyar zuciya itama   Ammi ajiyar zuciyar tashiga saukewa cikin taushin murya tashiga cewa 

” Kabar kuka Hassan Allah yasan halindakake ciki kuma shine zaiyima magani in sha Allah nan gaba sekamanta dawata damuwa a rayuwarka tunkafin naga damuwarka nasan cewa bakada alaqa da wannan cikin na Hamidat sabida nasan babu yadda za’ayi kasamu lafiya bakasanar daniba nasan farincikin ka baya ‘boyuwa agaremu sannan yadda naga kacanza kamar kayi muguwar jinya yasa tun a lokacin nasan cewa lalle akwai damuwa Hassan inaso kayi haquri kataushi zuciyarka karka yanke wani hukunci ayanzu mubi komi sannu sabida idan kad’auki wani mataki ayanzu musamman nasaki dole akwai tambayoyi idan hakan tafaru sabida kasan al’adar gidan saurauta babu saki idan bada wani babban daliliba wannan dalilin yakai matsayin sakin Hamidat to amma yanzu bakada hujja Hassan idan kuma mukamatsa tofa tabbas dole batun lalurarka zatafita inamai baka haquri kasake miqa komi ga Allah kaji Hassan ” 

Tashi yayi zaune yadubi Ammi sosai idanunshi sunyi jah sosai yace ” Ammi Dan Allah kibarni nasaki Hamidat dama tanemi hakan nace tabari semundawo gida kuma gashi mundawo Ammi ayanzu bandamu da kowama yasan lalurata ba aybanine nad’aurama kainaba Ammi ganin Hamidat a cikin idona yanzu mugun baqinciki ne agareni dan…….. ” tabbas nima banyarda Bro d’ina yazauna damata irin Hamidat ba Ammi gaskiya…….” 

” dakata Hussain kamar yadda nace abikomi sannu to abi nima banyarda yacigaba dazama da Hamidat ba amma akwai lokaci kaji ” miqewa Ammi tayi tafita zuwa part d’in Sarki Jabir  bayan fitar Ammi Hammat yadubi Hamut fuska tamke yace 

” Gaskiya Hammut kanabani mamaki wai nikam wannan Hamidat d’in itakad’ece mace ko idan karasata shikenan kadena rayuwa toma wallahi gara kadawo rakiyar mace yadda kakeson Hamidat idan da haka takesonka bazata ta’ba bama wani kantaba koda kuwa itace sugabar masu mugun shi’awa bazan iyayin rayuwa irin takaba Hammut kacanza dan Allah kacanza zuciyarka ” 

Yanagama fad’ar haka yajuya zaifita kamo hannunshi Hammut yayi cikin rauninmurya yace ” kayi haquri d’an’uwana amma inaso kasancewa ita soyayya makauniyace  tanashiga lokaci d’aya amma fitarta baya yiyuwa alokaci d’aya tanad’aukar tsayin lokaci kafin tabarka musamman soyayyar mutun ta farko aduniya tabbas Hamidat tayimin butulci a rayuwa ko cikin mafarki banyi zaton kwatankwacin haka daga garetaba amma Hammat  zuciyata tanatuhumata da lefi inaji kamar nine sanad’in saka Hamidat ta’aykata zina da’inada lafiya dabatayi shi’awar aykata hakanba  kuma danasaketa dabatayiba tunda tasan zata auri wani kum……..” 

” dakata Hammut ko kayarda koma karka yarda dole Hamidat mailefice itad’in jahilace koda bata ta’ba zuwa Islam ba tata’bajin cewa aykata zina haramunce balle mutun mai aure lokacin datake gidansu yayatayi da shi’awar tata seyanzune zatakasayin haqurin kadawo Nigeria kurabu tunda ita tacire rai da samun lafiyarka Hammut Allah natsani Hamidat batun yauba balle yanzu dako qaunar ganinta banayi ” 

Sosai zuciyar Hammut tasake karyewa sabida aduniya duk abinda d’an’uwanshi bayaso to shima jiyakeyi yatsane shi maganganun Hammat ayanzu sunsake sashi jin tsanar Hamidat  sosai  

Cikin tashin hankali Sarki Jabir yamiqe tsaye sabida tashin hankalin jin wannan mugun labarin tsayin lokaci yanakaiwa yanakawowa sannan yadubi Ammi yace 

” tabbas Hamidat tayima Hassan mugun butulci amma kamar yadda kikace abi komi sannu ko babu komi mahaifin Hamidat qanine agareni amma duk da wannan dangantakar bazaisa nayarda Hassan yacigaba dazama da Hamidat ba ” daga haka yafita daga part d’in cikin ‘bacinrai 

Hanan zaune cikin parlour Kaka kuyangu sungama tsaramata kwalliya sefaman kamshi takeyi wooow masha Allah gaskiya tayi matuqar yin kyau dama abu gurin mai kyau fitowa kaka tayi daga bedroom tadubi Hanan sosai tace masha Allah gaskiya Hammat yadace damata qarasowa tayi tace ” Gimbiya Hanan zakije part d’in Hammat yanzu tareda rakiyar hadimai don kai gaisuwa agareshi bayan kindawo shikuma zaizo dan tayaki hira irinta masoya tashi kije zakitafi da madara mai sanyi sabida yajiqa maqoshi wannan al’adar cikin masarautar nan ce damasauran wasu kuma yazama dole ayisu duka tashi kije hakan zesa kowa yasan cewa Hajiya kilishi tabaku tarbiyya ” sosai Hanan taji zuciyar ta nabugawa

Marmyn Zarah Ce

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button