Uncategorized

MUSAYAR RUHI 7-8

 

*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

 *Page 7 & 8*

*S* osai zuciyarta taqara shiga qunci jikinta yayi sanyi sosai fita tayi daga part d’in jiki babu qarfi tana shiga part d’inta tanufi bedroom kai tsaye dubanta Fadil yayi cikin damuwa sannan yamaida dubanshi kan Fadila kafin yace komi Fadila tace ” a a yaya basekace komiba mucigaba dayima Mom addu’a Allah yayaye mata damuwarta kaji ” daga haka tamiqe cikin damuwa tashiga bedroom shima miqewa yayi

yabar part d’in baki d’aya sosai hankalin Hanan yayi matuqar tashi sabida jin sautin kukan Hamut datayi a cikin bedroom d’in Ammi kasa kwanciya tayi hakan yasa dole tafito tanufi bedroom d’in Ammi bayan taji fitar Hamut d’in bakinta d’auke da sallama tashiga jin sallamar Hanan yasa Ammin saurin share hawayen fuskarta zama Hanan tayi fuskarta d’auke damatuqar damuwa duban Ammin tayi cikin raunin murya tace 

” Ammina tabbas akwai damuwa atare daku da yaya Hamut dan Allah Ammi meke faruwa koda bazan’iya yin komiba wajan kawo mafita ba amma zan’iyayin addu’a dan Allah Ammina meke faruwa ne ? ” 

Ajiyar zuciya Ammi tasauke tace ” haba Hanan babu komi kinji kinsande halin rayuwa watarana farinciki watarana baqinciki dole akwai haka cikin rayuwa karki damu kinji zewuce in sha Allah nan kusa ” 

Jinjina kai Hanan tayi tace ” hakane Ammina amma bakisaba ‘boyemin komiba duk abinda yake damunki kafinsu yaya Hamut susani ni nasani ina tunanin dan nakasance mace d’aya tak acikinsu shiyasa kike fad’amin damuwarki sukuma kiboye musu amma yau gashi Ammina tana’boyemin damuwarta amma tabbas zanshiga damuwa sosai yayana Hamut wanda yake sakarmin fuska yayimin murmushi idan inacikin damuwa yasani farinciki  yau gashi yanacikin damuwa banida hanyar sakashi murmushi tabbas dole nashiga damuwa ” miqewa tayi jiki a sanyaye zatabar bedroom d’in har takai bakin qofar Ammin tace 

” Hanan dawo kizauna ” komawa tayi tazauna cikin sanyin jiki yimata nuni tayi  tada kwanta saman cinyarta kamar yadda tasaba babu musu takwantar dakanta saman cinyar Ammin ajiyar zuciya Ammi tasauke sannan tace ” tabbas inada damuwa Hanan kuma damuwar akankine sauran kad’an kikammala karatunki dakin gama aure zakiyi bansan kokinada wanda kikesoba nikuma banason tauye miki dukkan abinda kikeso amma bazanji dad’iba idan baki aure wanda nikeso ki’auraba tsayin shekaru nike jiran wannan ranar amma bazan iya tusasakiba dukda faruwar hakan zaitona wani sirri wanda banaso yafita amma yin hakan shine zai dauwamarmin da wacce nike tsananin qauna ataredani har abada dukda cewa zan fuskanci qalubale sosai  acikin Masarautar nan amma zanjure dan cimma burina kinji damuwata Hanan shikuma Hassan bansan meye damuwarshi ba nima yaqi sanar dani hakan yasakesakani cikin damuwa ” 

Tashi zaune Hanan tayi tashare hawayen fuskarta tace ” Ammin koda akwai wanda nikeso kamar raina wallahi zanfitar dashi na’amshi za’binki zankumayi farincikin za’bin Ammina balle babu kowa ataredani Ammi karatuna nasaka agaba Ammina na’amshi za’binki tun yanzu Ammina kiyi farinciki shikuma yayana Hamut muyimai addu’a babu abinda yafiqarfin addu’a sannan Ammina wane sirrine zaitonu kuma wace irin matsala zaki fuskanta ? ”

Murmushi Ammin tayi tarungumota cikinta tace ” karki damuwa zuwa lokacin zakisan komi ayanzu banida amsha nayi farinciki sosai kuma nasakeyima Allah godiya dayabani ke matsayin ‘ya agareni Allah yayi miki albarka tashi kije ki kwanta kinji ” murmushi Hanan tayi tasumbaci kuncin Ammin sannan tamiqe tayimata sedasafe sannan tafita 

Jiki sanyaye Hamut yashiga part d’in nashi bin inda akajera kayan abinci dana motsa baki yayi sakejin damuwa yayi cikin bedroom d’in shi yanufa yana shiga yarage kayan jikin shi yashiga wanka tsayin lokaci sannan yafito yana dafe da mararshi sabida yadda yakejin ciwo ko yaya yamotsa shiryawa yayi cikin shigar bacci sannan yafito bedroom d’in Hamidat yashiga zaune yasameta tanayin waya da momcy ta cikin sanyin murya yace 

” idan kingama kifito parlour ina jiranki ” zuyawa yayi yafita wajan abincin yanufa leder dayagani agefe yabud’e kajine manya guda 2 aciki da yoghurt mai sanyi sekuma nau’ikan abinci kalakala agurin kasa koda qwaqqwaran motsi yayi sabida yadda yaji zuciyarshi tasake shiga qunci sosai tuno maganar Ammi yayi da alqawarin dayayi mata akan zaici abinci hakan yasa yashiga zuba abincin cikin sanyin jiki yafara d’ibar abincin yanaci badan yanajin dad’in shiba sedan alqawarin dayayima Ammi kawai yasa yakeci dede lokacin Hamidat  tafito ahankali take taku kamar maitausayin qasa sanye take cikin kayan bacci masu bin jiki sun bayayyana surar jikinta sosai tana qarasowa tazauna daf dashi sosai kwantar dakanta tayi saman kafadarshi tad’aura hannunta saman sumar kirjinshi wadda takwanta luf cikin lokaci kad’an taji kasala tamamaye jikinta ajiyar zuciya Hamut yasauke yace 

” yakamata muci abinci ko ? ” shagwa’be fuska tayi tace ” jikina babu qarfi please kabani ” rumtse idanunshi yayi sannan yace shikenan gyara zaman naki ahaka bazai yiwuba ” gyara zamanta tayi ledar kajin yajawo yabud’e duban kaji tayi tace ” a a my D wannan basuda amfani agareni ayau kabari sezuwa ranar daka warke aranarne zanjini amatsayin cikakkiyar amarya ba yauba yanzu irin abincinka zanci ” sosai maganar tadaki zuciyar Hamut amma beko iya cewa komiba bata nashi abincin yashigayi har taqoshi sannan yamiqe yanufi bedroom batare dayacemata komiba yana shiga yakwanta saman bed idanunshi nakallon sama hawaye suka shiga gangarowa tagefan fuskarshi babu jimawa Hamidat tashigo cikin bedroom d’in hawa tayi saban bed d’in takwanta saban qirjinshi tashiga shafa sumar qirjinshi ganin hawaye nasauka tagefan fuskarshi tace 

” haba my D nifa karkaga lefina iya gaskiyata nafad’a idan na’boyemaka najekuma na’aykata kuskurefa yaya zakad’aukeni ? Wallahi bazan iya jure lokaci maitsayi batare dasamun kulawar namijiba My D kafahimta naqosa namatsu dazuwan wannan ranar yawancin dare inakasayin bacci sabida tasowar shi’awata tunaka kawai zanyi naji yanayina yacanza My D balle yau gani gaka dan Allah kasanaji sassauci koyayane tunda har kaga na’iyafurtawa duk irin kunyar mace tabbas akwai matsala please help me my D ” 

Wani irin kunlewa yaji zuciyarshi tayi gawani irin zafi datashigayime jan numfashi yashigayi dasauri dasauri dafe setin zuciyar tashi yayi yashigayin magana cikin wahala 

” karkidamu My B nayimiki alqawarin bazan bari kicutuba koda bansamu lafiyaba zansamar miki damafita in sha Allah  kuma yau zanyi iya iyawata nasaki kibanbance sauran dararan dasukawuce abaya da wannan daran nayau ” daga haka yajawota sosai yasaka bakinshi cikin nata yafara sarrafata sosai yake aykamata saqonni cikin salo ahaka kamar zai’iya aywatar dakomi amma kass itako Hamidat sosai tarikice sake mannewa takeyi ajikin shi sosai yatsinci kanshi dajin tausayinta Zameta yayi daga jikin shi yashiga toilet cikin Sauri tashi tayi  zaune tanasauke numfashi sosai takecikin tsananin buqata  Shiko yanashiga zama yayi yadafe kanshi yanasakin muguwar ajiyar zuciya gazafin zuciya yanaji sosai Kamar zuciyar tashi zata qone sabida zafi  tsayin lokaci sannan yad’auro alwala yafito bai Kalli inda takeba yashinfid’a abin Sallah yatada sallah sauka Hamidat tayi daga bed d’in tabar cikin bedroom d’in Cikin wani yanayi Shiko Hamut kwana yayi  sallah awannan daran hakama  Hammat da Ammi  duk sunayime  addu’ar samun lafiya 

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button