MUSAYAR RUHI 7-8

Washegari misalin 3pm doctor ya’iso Nigeria kasancewar tun jiya yataso Hammat neyaje filin jirgi dakanshi yataho dashi koda Suka’isa cikin masarautar nanfa gulma tatashi kowa yanatambaya me wannan d’an China yazoyi cikin masarauta ayau Kiran jakadiya hajiya Mariya tayi cikin part d’inta itama hajiya tana cikin part d’in duban jakadiya sukayi hajiya Mariya tace
” jakadiya tabbas akwai abinda ake ‘boyemana acikin masarautar nan naga hajiya Salma tashigo cikin masarautar nan jiya afusace hadima larai tacemin taji tanacema gimbiya Hamidat bazai yiyuba bazatabari ‘Yarta tazaunada namiji irin maimatsala ta Hamut ba tabbas akwai wata aqasa dubada daga airport akawuce dashi asibiti wai yasamu accident segashi yadawo babu alamar ciwo jikinshi Sekuma maimartaba yafara qoqarin hana aywatar da al’adar shinfid’a farin gyalle bayan haka gimbiya tace tanayin jini senan dakwanaki 6 bayan Kowa yasan yanzu ba’ayin haka anatsara komi a yadda yakamata Lalle akwai wani abu hmmmm ayau kam nizan rikita komi jakadiya inaso kiyi duk yadda zakiyi kigano mana wani abu idan kikayi hakan kinada kaso maitsoka nikuma zanje wajan hajiya nazugata Sena rikita komi ”
Tashi jakadiya Tayi tace ” nikuma sena ganomuku komi “fita tayi cikin sauri part d’in Hamut tanufa zaune tasamu Hamidat itada hadimanta gaidata tayi cikin girmamawa sannan tad’an zauna jim bataga alamar cewa Hamut yana cikin part d’in ba hakan yasa tatashi tafita zuwa part d’in Ammi nanma babu Hamut ba Hammat se Ansar da Hanan zaune gaida Ammi tayi sannan tace
” Allah shi taimakeki Allah yaqaramiki lafiya dama zuwanayi natambaya naga anyi baqo maiyakamata akawo mishi tunda naga shi bad’an Nigeria bane dole za’asamu banbancin cima ”
dubanta Ammi tayi tasaki murmushi tace ” a a wannan baqon Husain ne kuma lamarine na aykinsu dan haka shi yatanadar mishi komi kuma kinsan halin Husain bayason anashiga cikin harkarshi idan kuma zakishiga tojeki kitambayeshi babu ruwan hajiya kilishi ”
zaro ido Jakadiya tayi tace ” ina nina isa yarima Hammat a a nabarki lafiya ” daga haka tamiqe tafita binta hanan tayi dakallo sannan tadubi Ammi tace ” Ammina nifa gaskiya wannan jakadiyar banfa yarda da’itaba tafiye gulma ” Murmushi Ammi tayi tace ” ay bama itakad’eba akwasu dayawa kede shi’anin gidan sarautar se ahankali ” tsaki Ansar yaja yamiqe yace ” Allah yasa nakama mata tana gulmana wallahi daga ranar senasaka ancanzamata kamanni ” daga haka yabar parlour afusace girgiza kai Ammin tayi tace ” shegiyar zuciya kamar Husain shide hassan babu ruwanshi ” murmushi Hanan tayi tace ” hakane amma shikuma akwai jin kai da miskilanci ” murmushi Ammin tasakeyi tace ” ay wannan jinine Hanan sarauta gaba da baya kinga kuwa dole ayi jin kai ” murmushi Hanan tasakeyi tace hakane kam
a part d’in Hammat doctor yake duba Hamut tundayazo yakeyin aykin har dare amma kamar babu nasara misalin 9:pm doctor yadubi Hamut da Hammat yace
” gaskiya sede kayi haquri nayi duk abinda yakamata nayi amma wa’innan jijiyoyin sunriga sun mutu kwata kwata bazasu sakeyin ayki ba kayi haquri zanbaka magani zakadenajin ciwon marar k……” kafin yaqarasa Hamut yamiqe yace banabuqatar maganin naka nagode Hammat kasallameshi kasa akaishi masaukinshi zuwa safe yakoma china kuje kudawo inason magana dakai ”
ganin yadda ranshi ya’baci yasa Hammat yin abinda Hamut yace bayan yasallameshi yadawo zama yayi kusada Hamut d’in idanunshi sunyi jah sabida tsananin ‘bacin rai kafin Hammat yayi magana Hamut yadubeshi cikin damuwa yace
” d’an uwana ayau inaso kanunamin qarfin dangantaka nasan babu alfarma agaremu tsakanin ni dakuma kai amma ayau zanroqeka alfarma nakumasan zakayimin ita sabida girman alfarmarne yasa naroqeka nasan duk abinda nikeso kaima shi kakeso natabbatar dahakan ayauma zansake tabbatarwa!!!!!!!!!!! Hammat Inaso kayi auran sirri kaida matata Hamidat ko ita banaso tasan haka idan kayi haka zan…….”
” dakata Hamut bazanyiba bakuma zan iyaba kai kasan banida ra’yin mace balle matarka Hamidat yarinyar danayi matuqar tsana ina gaskiya bazan iyaba ”
miqewa Hamut yayi yashare hawayen fuskarshi yanufi hanyar fita ja yayi yatsaya yace ” tabbas ayau natabbatar dacewa Hammat bazai iya yin musayar ruheey da Hamut ba kasani idan narasa Hamidat tabbas nima zakarasani dama iya haka qarfin dangantakarmu take dukda rayuwa damukayi a ciki d’aya kuma lokaci d’aya dama ba uwa d’ayace tahaifemuba dabazanji damuwaba dan kaqi ceto rayuwataba to amma kasani tabbas zantafi nabarka ” hannu yasaka zai bud’e qofar Hammat yayi saurin kamo hannunshi dubanshi yayi yadda hawaye suka wankemai fuska sharemai hawayen yayi yace ” zanyimaka duk yadda kakeso amma kasani zuciyata bazata ta’ba son Hamidat ba ”
ajiyar zuciya Hamut yasauke yace ” hakan nikeso duk ranar dakasota bazan iya yafe makaba inaji ajikina zanwarke nangaba in sha Allah zansaki Hamidat saki batare dakowa yasaniba zamuje ad’aura maka aure da’ita ayau tunda batada iddata akanta zandawo nace mata namayar da’ita kuma nasamu lafiya zakazama miji agareta amma nasirri duk dare zakajemata amatsayin nine kuma yazama dole kakusanceta amatsayin nine tabbas zanji babu dad’i cikin zuciyata amma hakan zaifimin sauqi akan ace wanine ta’aura duk ranar dana warke zakasaketa tadawo gareni komi dad’ewa ”
rumtse ido Hammat yayi yace ” tayaya Hamut idan bata ganeni takomiba zata ganeni ta yanayi dakuma launin idanuna Hamut tayaya zan’iya kusantar yarinyar dakabama zuciyarka tun tana ‘yar qaramarta k……..” dakatar dashi Hamut yayi dafad’in zan’iya sadaukar dakomi akan farincikin Hamidat kuma kai d’an’uwanane idan wanine yayi hakan to wallahi sena kasheshi sannan maganar lauyin idanu natanadi ledar dazakasama idanun naka yanayi kuma kayi qoqarin setashi yadawo irin nawa idan kayi haka zancigaba da rayuwa akasin haka kuma mutuwa zanyi zanje nayima Ammi bayanin komi ita kad’e nikeso tasani sabida banta’ba ‘boyemata komiba bakumazanfara akan wannan ba ”
Comments and shire please