MATAN GIDA Complete Hausa Novel

MATAN GIDA
0⃣1⃣
Na
Fauziyya Usman Kogo
Zaune take tana karatun Qur’ani Safwan yaturo kofa yashigo yasami guri daga gefenta yazauna yana kallonta yayinda duk yaji tabirgesa yafada azuciyarsa tabbas nayi sa’ar mata tagari kuma maikyawawan dabi’u bayan takarasa tayi addu’a tashafa shima yasha takai kallonta garesa tana maiyin murmushi yaya Safwan sannu da fitowa yauwa wai Safna maiyasa bazaki dena kirana da yaya Safwan ba nafada maki nafisan Dear akan yaya tayi murmushi sosai maitare da yar dariya yihakuri nadena ok gaskiya Safna dole nakara yiwa Allah godiya abisa samunki danayi Alhamdulillah Safna wallahi ke mace tagari ce kuma abar alfahari tayi murmushi nagode sosai abisa yabani dakake am Safna inasu Salman suna dakinsu Salma tana yimasu karatu yayi murmushi Allah sarki yaran albarka bara nadubasu ok yatashi yanufi dakinsu Safina yasamesu Salma nakarantamasu suna ansawa bayan sunkarasa sungaisa da Safwan Allah yaimaku albarka yarana Amin Dady to kucigaba da karatunku nizan fita Dady Allah yakiyaye Amin yafita yadawo inda Safna toni zanfita Allah yakiyaye yadawomin dakai lafiya Amin
Yana fita kaitsaye gidansu Umma yanufa domin yakaimasu yar siyayyar dayamasu ta azumi ya’isa gidan Habu yariko masa kayan sunshigo bayan sungaisa yace Umma gawannan bayawa tayi murmushi bakomai Safwan Allah yama albarka Amin Umma yadan jima anan suna fira daga bisani yatafi yatafi gidan Hajiya itama yakaimata kayan azumi zuwa la’asar yanufi masallaci gurin tafsir
Kwance take tanata faman malalowa Pikram yashigo yasameta yaja numfashi tare da girgiza kai ya’anbaci sunanta Ikram tadago kai takallesa na’am ya’akaine Ikram waihar saiyaushe zaki tashine dubafa kiga karfe 01:00pm amma ace har yanzu bakigama barciba kamar gareki farau azumi haba yaya Pikram kaimafa kasan azumin farko wahalane dashi amma sai kokarin ganin laifina kake tokinga duk bashiba yanzu kitashi kitafi kiyi salla ga cefanecan nayi kidora girki domin su Fa’iz anan azasusha ruwa ok tatashi tatafi tayi salla bayan ta’idar tafito taga cefanan da yayi tazaro ido tare da dukan kirji tace tirkashi yaya Pikram wannan cefanan harna yaushene kamarya naga siyayyar da yawa eh nayaune kawai kokinmanta nafada makisu Fa’iz anan zasusha ruwa haba yaya Pikram taya zan’iya wannan aikin saikace jaka ka’Auro ko wadda kasiyo to komadai siyoni kayi aisaikatina da kudinka da kabayar gaskiya nidai bazan’iya wannan aikinba dubafa kaga nama kawai Kala biyune Ikram maikike nufi kawai kabarni nayi abinda zan’iya wannanma airashin tausayine inafama da yunwar azumi kuma zaka jibgomin wannan uban aiki haka gaskiya bazan’iyaba takoma daki tayi kwanciyarta tana gunguni takaicinta yamasa yawa wannan yasa yafita yabarmata gidan yayinda bacin rai yayi yawa atare dashi
Zaune yake yaji zaman badadi yatashi saikai kawo yake yayinda tinani iri daban-daban yayi yawa azuciyarsa Islam sai kallonsa take tagagara jurewa takirasa Isma’il waimiye hakane maiyake damunka tin daran jiya nafahimci sam baka cikin farin ciki maiyake damunkane dan Allah kafadamin domin nikaina abin yana damuna yazaune yakalleta tare da sauke ajiyar zuciya Islam ni wallahi bansan yazanyi da raina ba kasan cewar banida komai kuma gashi anfara azumi kowane mutun yana bukatar abu maidadi ni wallahi sambanajin kaina kekawai nakeji bansan yazanyi nabaki abinda zaifaranta rankiba wannan ne abinda yake damuna kuma abin takaici nagagara samun mafita taja numfashi tare da girgiza kai haba Isma’il aiwannan baikai abinda zaisa kadamu kankaba Kaga niwannan sam baya gabana dan haka kadena wani damun kanka komai yayi farko yana da karshe wata rana sai labari fatan anan Allah yakarbi ibadunmu yasamu acikin bayinsa yantattu ya’amsa da Amin
Misalin karfe 12:30pm Safna tashiga kicin tadora girkinta tare da babbar yarinyarta wato Salma Safina da Salman kuwa tabasu dan aikin da baifi karfinsu ba zuwa karfe 06:00pm takammala komai tagyara gidanta tako ina kamshi ketashi tashirya yaranta dama ita kanta koda Safwan yadawo yasamu takammala komai baifi mintuna goma da dawowaba akayi kiran magariba sunyi buda bakinsu cikin kyakkyawan yanayi
Allah sarki Pikram koda yadawo gida ana kiran magariba kuma yasamu ba’abinda tayi masa saima faman juyi dayasameta tanayi bai’iya cewa da ita komaiba saima alwala da yayi tare daukar siyayyarsa yafita yatafi yakaiwa Isma’il dama makocinsa ne tare da basa hakuri akan rashin kakomasa ba akan lokaciba yakarba tare da yimasa godiya sosai yashiga yanunawa Islam tayi dariya tare da nunajin dadinta tatashi jiki narawa tatafi tadora girki bayan wani lokaci takarasa girkinta tasauke tare da zubamasu sunci sunyiwa Allah godiya Pikram kuwa saidai yayi buda baki agidan mamarsa
To masu karatu kubiyoni agobe danjin yanda zatakasance
By. Fauziya Usman Kogo
[1/2, 19:48] Maman Adyan: ????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀MATAN GIDA????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
0⃣2⃣
By
Fauziya Usman Kogo
Ikram yau bazaki azumi bane zanyi mana tomaikike nufi da haryanzu baki tashiba kuma kinaganin lokaci tafiya yake taja numfashi kai wallahi yaya Pikram kafiye takura matun tatashi tahada shayi tasha tinda tagagara nemamasu abinda zasuyi sahur dashi kallonta kawai yake yagirgiza kai tare da sauke ajiyar zuciya Allah yakyauta yatashi yanufi masallaci tabishi da kallo acan gurinsu Safwan kuwa karfe 03:30am tafarka domin dora masu abincin sahur tana kokarin tashi Safwan yakara riketa tare da tambayarta ina zuwa banesa zaniba iyata kicin yace kicin yanzu eh inasan nagirka mana abinda zamuyi sahur ne aiya gashi nikuma sam banasan rabuwa dake Dear kenan aihakan bayanufin munrabu kayi hakuri natafi karmu makara ok yasaketa daga rungumar dayamata tatashi tanufi kicin bawani bata lokaci tayi aikinta tagama tazubo masu sunyi sahur hakama agurinsu Isma’il bawata damuwa sunyi sahur lami lafiya
Misalin karfe 04:00pm Salim yadawo gida jiki asanyaye kallo daya zakayi masa kafahimci yana tare da damuwa yasami guri yazauna tare da yintagumi Nafisa sai kallonsa take tagagara hakuri tashiga tambayarsa Salim wai lafiya kuwa kawani shigomin gida saikace wanda aka’aiko da sakon mutuwa maiyake faruwa ne yaja munfashi tare da sauke ajiyar zuciya cikin kasa-kasa da murya ya’anbaci sunanta Nafisa wallahi inacikin yanayi irin najarabawa yaumadai kamar kullum kinga abinda nasamo mana kiyihakuri kitashi kisarrafa manashi domin musami abin da zamuyi buda baki dashi takai hannunta galedar dayamata nuni da ita tace Salim mainake gani kamar aune aibaka mane aune nayomana domin musamu abinda zamu rufawa juna asiri taja tsaki tirkashi wallahi Allah yawadarar naka yalalace yanzu ace kafita tinsafe amma karasa abinda zaka shigomin dashi sai wannan kayan tsintar muna cikin waran azumi kowane gida anasauya abinci tare da cin adarashi kamarsu nama kifi su lemu ayaba kankana dadai sauransu amma shine zaka kawomin wannan abin harkana ganin waikayi wani kokari tinjiya nakesaka ido danganin sauyi amma sam bawani sauyi atare dakai Salim bara nafadama gaskiya nidai bazan’iya dafa wannan tarkacan shinkafar takaba domin kafin nagama tsinta ankaiga buda baki dan haka gatsiyarkanan andai rako maza wallahi taja tsaki tayi tafiyarta yayinda take wayansu surutai ace mutun yayi azumi amma bazaisami naman da zaiyi buda baki dashiba dazarar kayi magana sai yace dakai babu kamar gareshi farau talauci taja tsaki Allah sarki Salim bayan tatashi yabita da kallo tare da girgiza yace Allah sarki duniya mace kenan maibakin kaza yanzu Nafisa hartamanta dajin dadin datasamu azamanta dani yauni Nafisa zatayiwa tsaki takirani da talaka dan kawai Allah yajarabeni darashi tahantar hada hannun jari danayi yau da ace naci riba tahanyar haka natabbata datafi kowa watayawa amma tinda asaranayi saitake hantarata tahanyar fadamin magana sanranta bakomai Allah yakawomin mafita ta’alkhairi