NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 21-22

21&22
…..babu b’ata lokaci ta wuce cikin parlourn gidan”babu kowa sai masu aiki nata goge goge”gaishesu Aysha tayi ta wuce parlourn ammi”hindatu na zaune suna vedio call da dr sadeeq”Aysha naganin haka tabar parlourn da sauri”ta wuce bed room d’in ammi.
ammi na kwance idanuwanta abud'e"Aysha tayi sallama tana kallonta"ak'asa kan carpet ta zauna tace".ammi ina kwana yajikin naki?"Allah yak'ara lafiya yatsareki daga dukkan abin k'i...,
ammi nata kallonta cike da farin ciki"tarasa meyasa takejin tsananin k'aunar yarinyar da tausayinta aranta....ta kuma yarda da cewa" Aysha najin tausayin halin datake ciki"murmushi ammin tayi"wanda bata tab'a yiba tun bayan fara ciwon....
Shigowar hindatu yasaka ammi dubarta tana mata murmushi”zaro ido hindatu tayi tana shafa idanuwanta ta matso gefen ammin ak’asa ta duk’a tace”.dan Allah ammi da gske kece ke murmushi?”bara na Kira yaya nasanar masa”gsky zuwan baby gidan nan alkhairi ne wlh.
Alama da ido ammi ta mata karta kira shi”shikenan ammi bazan kirashiba”
Ina kwana anty hindatu?”lafiya qlau baby ya gida?”shine kina ganin muna waya da yaya kika gudo?ah ah Allah ba haka bane”
yanzun kije parlou adining area break fast naki na nan”idan kingama zamuje anguwa”dato Aysha ta amsa ta fita.
Hindatu ta kalli ammi tace”.ammi yarinyar nan tana bani tausayi”da alama gidan masu ruk’onta basuda hali”dubi suturan jikinta”zamuje namata shopping gsky”
sosai ammin taji dad’in hakan”dama tanaso tayiwa hindatu ishara datayi hakan”sai kuma tamata mgn”da ido ammi ta amsa mata”
Aysha nagama break fast ta gyara bed room d’in ammi”sannan aka bata magani tasha aka
shafa mata ajiki”sukabar iya agunta suka fita.
Shopping sosai hindatu tayiwa Aysha”ta siya mata”dogayen riguna gownt dana materia,da hijabai ,da mayafai da kayan kwalliya da turare”wanda sai bayan ansiyo Aysha tasan natane”tak’i amsa kuwa.
saida hindatu ta nuna mata ranta yab’aci sannan ta amsa”
gun saloon suka wuce tasaka aka gyarawa Aysha gashinta”wanda hindatu ta rud’e akansa”
Tasaka amata kalba”akabi da bant akayi parking “
suna dawowa gida hindatu tasaka Aysha tayi wanka tasaka riga guda……wayyo Allah ba hindatuba”harta ammi kallon Aysha sukeyi”
gaba d’aya kamar ma ba itaba(amfanin gyara”mata mudena kashe kanmu bbu gyara)
masha Allah baby!k’ilan idan yaya yadawo bazai ganekiba ko?”gaban Aysha yafad’i”tarasa meyasa hindatu kemata yawon zancensa?idan kuma akayi zancensa sai taji fad’uwar gaba”
zamanta Aysha tayi batace komaiba”hindatu na murmushi ta dinga mata photo bata saniba”
Rayuwar Aysha taci gaba da wakana agidansu dr sadeeq”tayi shak’uwa sosai da mutanan gidan”
yyinda hindatu kebata kulawa da koyar da ita abubawa daban daban”har girki acikin sati 4 Aysha ta iya kalolin abinci”
Tayi haske ,fatarta tayi frash sbd canjin abinci”ga kayan shafa masu saka kyan jiki hindatu ta siya mata”
Aysha ta canza sosai dukda tsiwarta na nan”amma yanzun ko mgn batason yi”
Anty murja ta siya mata nokia suna gaisawa da ita”
B’angaren jikin ammi kuwa saidai muce Alhamdllh”domin yanzun ammi na murmushi ko dariya,tana motsa hannu da k’afa”tana iya girgiza kanta”tana iya d’aga kanta”abinda yarage mata mgn da tashi tayi tafiya.
Aysha kuma nacigaba da mata addu’a”tamata saukar alk’ur’ani me girma”yanzun kuma tana rubuta mata shi tana wankewa da zam zam abata tasha”
gefe guda kuma honorable lawal be gidan tun kafin tafiyar dr sadeeq”ita kanta ammin batasan Inda yajeba”dukda dama yanada mata da yara 3″
Dr sadeeq tunda yatafi hidimar gabansa yakeyi”mantawama yakeyi da wata aba wai Aysha”
sai idan suna waya da hindatu kemasa zancenta”sannan yakema tunawa da ita.
kuma har yanzun besan Aysha nakulawa da lafiyar ammin ba.
kawaidai yana ma tunanin idan yadawo yaga tayi hankali yabarta “idan batayiba yasallameta.
Baffa idi kuwa yana ankare da canzawar da Aysha tayi”hakan kuma yamasa dad’i sosai”domin saura kiris burukansa sufara cika akanta”
Ayau yakama Wednesday!kuma ayau dr sadeeq zai dawo”hindatu kuma tak’i sanarwa Aysha “
Atare suka shiga kitchen”komai sai suka raba”hindatu tace”.ai mijinta yau zaidawo gari”shine zasu yiwa girke girke.
Ita kuwa Aysha dama zuwan mijin hindatu 2 tana gidan”kuma idan zaizo haka ake masa girki”saita d’auka hakane”
Dambun kaji Aysha tayi da meat pie”tayi kunun aya”
Hindatu tayi friend rice da farfesun kayan ciki”
tun k’arfe 10 nasafe suke kitchen sai 1pm suka idar”gaba d’aya tun abakin get har zuwa main parlour k’amshin girkine yacika gidan…
Hindatu tace”.suje suyi sallar azahar”bayan sun gama sallar sukaci abinci”
Ammi kuwa bacci ma takeyi”Aysha taga babu abinda zatayi kawai tamik’e kan 3 seeter d’in parlourn ammi,bbu jumawa bacci yyi awon gaba da ita….
Cike da nutsuwa da kamala dr sadeeq yayi sallama cikin nutsatstsiyar muryarsa aparlourn”
babu kowa a parlourn”yana janye da troley d’in sa”k’arewa parlourn kallo yayi sbd ganin bbu kowa….. idanuwansa suka hasko masa Aysha dake kwance tana bacci”
Hular kanta ta zame bak’in gashinta yazubo”tab’e baki yayi yad’auke kansa”sbd shibema gane ko wacece ba.
yana k’okarin nufar bed room d’in ammi hindatu ta fito”ihun murna tayi ta fad’a jikin sa”murmushi yayi yana shafa bayanta yace”.bakya girma ko baby?”
yaya sannu da dawowa”kaga yadda kayi kyau? k’asar ta amsheka wlh”tafad’a tana barin jikinsa tayi tsaye tana kallonsa.
yana sanye da suit bak’ak’e”yyi kyau masha Allah yanata k’amshi”sai kayi kamar irin black american d’in nan”
Tab’e baki yayi ya gallah mata harara yawuce ta gefenta” yabud’e k’ofar bed room d’in ammi yashiga”hindatu ta biyosa”
Ammi dake zaune tasaki murmushi dasuka had’a ido da dr sadeeq”
zaro ido yyi yana sakin troley d’in hannunsa yak’ara so gefenta kan bed d’in”Alhmdllh sauk’i yazo ammi”yaushe Kika fara murmushi bansaniba?baby meyasa baki sanarmun ba?”
ammi kuwa hannunta ta d’aga ta aza saman kan dr sadeeq”ai gaba d’aya saiya rud’e”
Hindatu na murmushi tace”.ai yaya akwai labari saika zauna ma wlh”
yanzun bara naje nakaimaka kayanka ,kayi wanka kaci abinci”sannan zan sanar maka silar fara samun warakar ammi”
Dr sadeeq yace”.to shikenan baby”ammi ina wuni ya gidan da jikinki??”d’aga masa kanta kawai ammi tayi”
Hindatu ta fice dg d’akin”dr sadeeq nata kallon ammi yanajin farin cikin tafara samun lafiya”
tashi yayi yafito ya wuce shashensa yayi wanka “
yasaka jallabiya brown yashigo cikin gidan”hindatu tagama shirya masa komai adining”be nufi can ba”sbd yanaso yaga amminsa”d’azun dayaganta jiyakeyi kamar a mafarkine”
Ahankali yatura k’ofar yashiga”ammi na kwance kamar yadda yabarta”yazauna kan bed side drower”yana kallonta yace”.ammi wane maganine wannan ake baki???”yana k’okarin sake mgn hindatu ta shigo”yaya katashi kaje kaci abinci mana”
keni ta ammi nah nakeyi ba wani abinciba”nidai komai normal fa”kaje kaci abinci pls tafad’a cikin shagwab’a….dr sadeeq na k’ok’arin mgn Aysha ta turo k’ofar toilet d’in ta fito”jikinta duk ruwa da alama alwalah tayi….gabanta taji yyi mugun bugawa sbd had’a idon da sukayi da dr sadeeq….
Yanzun za’a fara wasan guys