NI DA DR. SADEEQ Book 1, page 9&10

BOOK ONE 📖
Story & written by
Mommyn fareesa
Dedicate to all my commenters🥰🥰
🅿️9&10
Office d’in ta nufa”ta murd’a k’ofar ta shiga”kamar jiran ta yakeyi ,yamik’e tsaye yana nunata da yatsa”last warning dazan miki”nakoma sakaki abu kikamun gardama zakisha wahala”
zaki wuce idan kin gama kukan ko kuwa??”kanta ak’asa batace komaiba ta wuce cikin toilet d’in”
Tafi awa guda tana d’ukiyar wanke tales na jikin bango”tanayi tana kuka harta idar”
kanta yadinga ciwo sbd kuka, idanuwanta sukayi jawur”duk sun kumbura gwanin ban tausayi”
wani irin mugun tsanar dr sadeeq takeji aranta”tana masa kallon marar imani”
Fitowa tayi dg cikin toilet d’in”tasamu yana duba wata patient”
kaji nagama dan Allah?”tafad’a kanta ak’asa”banza yamata yana cigaba da aikinsa”
har matar ta fita, wata ta shigo beko kalli Inda Aysha take tsayeba”
ganin k’afafuwanta na niyar tsami yasaka cikin k’unar rai ta nufi k’ofa….. wayabaki izinin tafiya?”yafad’a cikin husky voice”batare daya kalletaba.
banza tamasa tana k’ok’arin bud’e k’ofar”cikin b’acin rai yace”.wace irin yarinyace ke?”muddin kika fita zaki gane bakida wayo….
wlh ni inada wayo”saidai in kasheni zakayi ka kasheni”amma wlh nagaji”kuma saina fita har abada nida asibiti na….ganin datayi yanufota gadan gadan yasaka tayi saurin bud’e k’ofar”yarik’e gefen hijab nata da sauri taja da k’arfi tayi waje aguje”yana mara mata baya”
wlh kika bar asibitin nan saikin raina kanki….gaba d’aya mutane suka bishi da kallo”ga Aysha ta zura aguje tana kuka”
y’allab’ai kayi hak’uri ka koma ciki dan Allah”cewar murtala daya taso”jeka kiramun sister murya yanzun nan”muddin ka b’atan lokaci bakin aikinki”
yafad’a yana huci zai juya wata sister khadija ta iso tana cewa doctor pls…your are fire”kije Anas (P’A nasa) yabaki takardar kora….bejira cewartaba yaja tsaki yakoma office d’in”
Innalillah wa Inna ilaihir raju’un!!ta furta cikin tsananin rud’ewa.gaba d’aya nurses d’in dake gun sun tsorata”suntabbatar ransa ab’ace yake yau”
murtala da gudu ya isa ward d’in da sister murja take”ko gaisawa basuyiba yace”.maza kizo inji dr sadeeq”wlh bbu lafiya”yafara kora”nima yace idan nab’ata masa lokaci zai koreni…..nashiga ukku kaddai ace Aysha ce tamasa wani abu?”
Eh itace wlh”ahanzarce tamike tsaye suka fito dg ward d’in”
murtala yarigata isa office d’in dr sadeeq”y’allabai gatanan zuwa tare muka taho da ita.
banza dr sadeeq yamasa”yanata huci sbd yana shiga yayi waya get karsubarta ta fita.
jikin sister murja na kirma tayi sallama ta shigo”
Dr gani”inaso yanzun kidawomun da wannan yarinyar”koda tace”. tadenamun aiki ne”to dole tayishi”ko kuma kema ki rasa naki aikin”
subahanallahi! Allah yabaka hak’uri doctor”tana ina yanzun?”
bakin get”yafad’a atak’aice yana zama”batace komaiba ta juya ta fita”
murtala yamara mata baya”suna fita dr habib yashigo”
Ko zama beyiba yakalli dr sadeeq yace”.lafiya dai abokina?”shiru yamasa bece komaiba”
Kujera yaja yazauna kafin yace”.gsky baka kyautaba dazaka biyewa yarinya k’arama kuna haka”ai ba girmanka bane”
Mlm ita bakaga abinda tayiba?zaka kama azan laifi”natsaneta wlh”kuma dole tayi aiki anan “saina gama saitata sannan zan koreta”tunda yarinyar nan tazo take b’atamun rai”
Amma ance tafita tanata kuka meka mata?”tab’e baki yayi yace”.wanda yakaimaka gulmar yaka mata kayima wannan tambayar”
yanxun ba wannan ba”mutum 2 ka kora fa yau”dan Allah karka sake korar wasu”
muddin aka shiga hurumina saina kori mutum”gsky ka hau da yawa bara naje saika sauka”yafad’a yana dariyar tsokana”yatashi yafita”yana tunanin yaushe abokinsa zai canza?”
Aysha kuwa tana isowa bakin get d’in fita tasameshi akulle”get man yahad’e rai yace”. y’allab’a yace”kar abarki ki fita”
Uffan batace ba, ta matsa gefen shukoki ta zauna hawaye na zuba afuskarta”tana tunanin kodai ta gudu kawai..
Tana ahakan sister murja ta iso gunta”tana ganinta tasake fashewa da wani sabon kukan”wlh anty nagama zama a asibitin nan”
sosai anty murja ta tsorata da yadda taga idanuwan Aysha d’in”
Amma saita wani b’ata rai tace”.wato godiya kikamun ko Aysha?”namiki hanyar aiki,shine ni zaki salwantarmun da nawa aikin?
banganeba anty?”dama ta yaya zaki gane”umarni biyu zan baki”na farko muje kibawa dr sadeeq hak’uri”na biyu ki koma bakin aikinki”
Idan kika k’iya babu ruwana zai saka arufe ahalinki”kuma duk Inda zakije zai saka abincikoki”yanada iko,yanada kud’i (ta tsoratar da ita)
Amma gsky anty nidai zalintata yakeyi”kofa yanzun dukana zaiyi na gudo”tafad’a tana sanar mata yadda akayi”
muje kibashi hak’uri bazai dakeki ba”kidena masa rashin kunya”sannan duk abinda yasakaki kiyi masa indai besabawa addini ba.dr sadeeq beda matsala mutumin kirkine bazai miki zancen banza ba.
Idan kuwa bazaki iyaba to nacire hannuna akanki Aysha”
Tana share hawayenta tace”.zanyi anty”yauwa to muje”
tana rik’e da hannun ta suka shigo ciki sai kallonsu akeyi a reception”
Adaidai bakin k’ofar shiga office d’in sister murja ta tsaya tace”.kije anjima da k’arfe d’aya zansameki anan”
Anty dukana fa zaiyi wlh idan nashiga”murtala dake saurarensu yadinga dariya”
Fuskar anty murja ad’aure tace”.wuce kije bazai miki komai ba.
Atsorace ta tura k’ofar ta shiga”dr sadeeq na zaune kan kujera ya aza santala santalan k’afafuwansa kan table”yadad’e da bak’in glass”
Dg nesa ta tsaya da nufin idan zai daketa ta gudu”duk’awa tayi k’asa”cikin siririyar muryarta dataci kuka”ta wani turo baki tace”.kayi hak’uri dan Allah bazan koma ba”
ni sa’ankine?”abinda kikayi kin kyauta??”
Ah ah"dan Allah karka dakeni"tafad'a tana matsar k'wallah"sai asannan yakalleta yaga yadda idanuwanta suka kumbura sbd kuka"
nazata ai rashin kunyar taki tasaka miki baki tsoron duka”
Duk time d’in dakika koma yimun kuka anan saina kakkaryaki”stupid girl kawai”
Kanta ak’asa batace komaiba”dan Allah ka hak’uran?”bansaniba”
kitashi ki wanke kazamin hannunki ga basket can kihad’amun coffee”
Dato ta amsa tana tashi tsaye”dan Allah karkamun wayo idan nashiga toilet d’in kabiyoni kadakeni”
Tsaki yaja sbd yalura yarinyace sosai ita”toilet d’in tashiga”
tana k’okarin wanke hannunta”kyankyaso ya hau saman yatsun k’afarta”
wata razananniyar k’ara tasaki”sbd mugun tsoronsa takeyi”tayi baya da sauri zata yi waje…sulb’in tayis yajata tatafi suuuuuuuuuuuu!jikake tim”ta rintse idanuwanta tana koma sakin wata k’arar”da hanzari dr sadeeq yashigo cikin toilet d’in…..✍️
Comments kawai guys yanzun aka fara buga game d’in….
Karkuyi jaje idan anji shiru
Mom fareesa🖊️