Noor Albi

NOOR ALBI 3

NOOR ALBI
Mamuhgee

3
Tana zaune tsakar gidan tsaye bakin kicin tana wanke hannu a fanfo Dr Abbakar yafito ya fice Tai Masa asauka lfya cikin biyayyarta
Ya amsa Mata cikin kulawa shima ya fice.
Qarasa wanke hannayenta tayi sbd miyar abincin da anty Sa’adah ta zubar a Palo batareda sani ba tagama kashewa shine take wanke hannun,
Kofar palon abban ta nufa Kai tsaye tashiga da sallama
Har lokacin Yana yanda Dr Abbakar yafita yabarsa cikin zurfin tunanin abinda ke addabar zuciyarsa da shawarar dayake nanatawa kansa akan ya yanke Dan inganta rayuwar yarsa ko baya Raye ko Yana raye
Tabbas idan tana qarqashin inuwar Amininsa Kuma Aminin mahaifiyarta zata samu gata da kulawa tareda samun Amintacciyar rayuwar kwanciyar hankali.

Kai tsaye gurinda flask din abincinsa yake ta nufa tafara daukan flask din ta bude wani tiririn zafi da qamshin kunun alkama da gyada ya ringa fitowa daga ciki
Ta dauki dauki cup daya cikin cups din Dake gurin wainda aka Ware musu aka Bata na Abban
Ta tsiyaya kunun Mai Dan yawa aciki kafin ta maida sauran ta rufe ta dauki kofin ta baro gurin bayan ta jefa cokali aciki tana juyawa ahankali ahankali Dan ya huce ta nufi gurin Abban tana kallon yanayinsa da a fili qarara yake nuna yayi nisa a tunani.

Aje kofin tayi tafara tura kujerarsa zuwa bakin windo bayan tasake yaye musu labule sbd iska Dan yanzu tana basa kunun zufa zai taso Masa.

Janyo tata kujerar tayi ta zauna gabansa tareda aje tissue gefensu ta dago fararen idanuwanta ta kallesa cikin kulawa shima ita yake kallo
Ahankali tasaki wani irin murmushin dayasa Abban rufe idanuwansa ahankali sbd murmushinta bakomai yake bayyanawa ba sai zallar tausayinta.

Saida ta tabbatarda ya huce ba zafi kunun ta dauka tafara basa ahankali da spoon ta nufa bakinsa,

Sam bayajin yunwar Shan komai ayanzu sbd damuwar dayake cikinta sosai,
Jin inda lafiyarsa ta dosa ya wargaza duk wani Dan sauran qwarin gwiwarsa da dukkanin jarumtarsa
Tunaninsa ‘daya yanzu yanda zai Fadawa TURAKI buqatarsa Dan kuwa wannan babban abune Mai girma zai roqa agurinsa duk da girman banbanci masu tarin yawa dasuke cike a tsakani.

Sbd kawar da sabuwar damuwar da hanata shiga wani sabon halin yasa hakanan take basa abincin Yana sha tanayi tana goge Masa da tissue
ahaka yakesha har sukai nisa yakusa shanyewa.

Cikin nutsuwa ta Dan kallesa kafin ta bude Baki kamar ko yaushe da taqaitaccen sauti tace”

Koma menene sakamakon asibitinka
Bana cire Rai ga falalan ubangiji akan samun sauki da lafiyarka.
Karka saka sabuwan damuwa
Ko ahakan Ina godiya ga ubangiji daya bani ikon tasowa nayi rayi rayuwa da mahaifina.

Kallonta yake da idanuwansa dasuke jajir har lokacin zuciyarsa na sake zurfafa da tunani.

Tas tagama basa kunun ta dauko maganinsa shima tabasa kafin ta goge Masa ta dauko wani Dan turarensa da baya yanke musu Abdullahi ke siyowa ta ‘dan fesa Masa kadan sbd abdullahi din yamasa wanka kafin zuwan dr Abbakar
Tana gamawa ta fice Dan yau tana Dan da ayyuka
Ga wankin Momy ma ta Tara gwara na anty Sa’adah ta rage Mata jiya tayi abunta da kanta.

Harta fita Jin zafi a garin yasa tadawo ta turo kujerarsa ta fito dashi tsakar gidan Dan Tasha iska musamman dayake yamma tafarayi ba rana.

Wankin kayan Momy tafara a natse sai kayan anty Sa’adah kadan Wanda anty Sa’adah din Bata qarasa ba jiyan tana cikin Yi anty Sa’adah ta fito ta zaune gefen Abban daukeda takardunta na makarantar jami’a datakeyi tana karatu Dan tanada test a satin.

Sama sama take karatun tanayi tana Jan laylan da surutu duk da tasaba Laylah ba wani surutun zataiba musamman ma datake aiki Amma dai Haka sukeyin surutun sama sama tana yiwa Laylan bayanin wasu abubuwan dake cikin handout dinta tunda ita Layla Bata karatu tunda tagama secondary School last year shikenan iya inda nata karatun zai tsay kenan Kuma
Dan Momy tariga tafadawa Sa’adah da Abban hakan,
Bazata iya qarawa daga Nan
Tayi iya abinda taji zata iya
Idan akwai Wanda zai iya daukan karantun nata acikinsu biyun bismillarsu zasu iya dorawa daga Nan,
Shi dai Abba yasan baqar maganace tafada Masa Amma ko ahakan ya gode Mata Dan Koda laylan makarantar datai ta gwamnati ce yaga alamar tasamu ilimin Dan Haka shi ahakanma ya gode matuqa.

Sallamar momyn ce data dawo daga fitar datai tasaka Anty Sa’adah kallon kofa ita Kuma Laylah sauke kanta tayi qasa tana cigaba da wankin sbd sanin fuskartace abinda yafi komai tada zafi da ciwon Dake qunshe cikin ran momyn na shekaru yasa so da dama ita da kanta take dauke kanta da duk inda momyn zata kalleta din.

Kallon abban Dake zaune zugum idanuwansa a rufe yanajinsu sbd ganin yanda rayuwar yaransa biyu takeda banbanci Mai girma.

Direct Palo take neman shigewa Sa’adah tace Mata”

Momy zafi ake sosai fa gashi kin dawo kilama kin gaji.

Matuqar Laylah ko abba na guri bakajin muryarta cikin sakewa ko walwala Dan Haka batareda ta juyoba ta qarasa ciki tana cewa”

Bari nayi sallar la’asar saina fito ai.

Tana shigewa ciki Laylah ta tsame hannuwanta daga ruwan wankin ta dauraye tareda gogewa ta miqe taje ta dauko babbar daddumar da momyn ke zama akai ta dawo ta Kama kujeran abbanta ta matsar dashi gefe kusada ita sosai kafin ta shimfidawa momyn daddumar ta dauko Mata ruwa da abincinta duk ta aje Mata akai kafin ta koma ta juyarda kayan wankinta dayan gefen tana fuskantar abbanta sbd bawa momyn baya kamar yanda yake tun yarinta.

Wankinta taci gaba dayi har lokacin Sa’adah na janta da labari Amma tunda momy ta fito tayi tsit bayan motsin wankinta Babu abinda ke tashi sai qarar cokalinda momyn kecin abinci
Sa’adah ma datasan Laylah bazata Kuma maganaba Kuma saitayi shiru tamaida firarta gurin momyn.

Kusa rayuwar gidan gabaki dayansu Sa’adah ce kawai wadda Allah yabawa ikon gudanar da rayuwarta cikin walwala da sakewa tareda wadataccen kwanciyar hankali da nutsuwa harma da farin ciki sbd Sam bata dauka komai tasakawa rantaba,
Abban nema so da dama batada shaquwa dashi Sam Sam sbd farko datana yarinya abunda yafaru yaso cusa Mata tsanar mahaifin nata Amma Kuma qaunarta da ‘yar uwarta da batada kowa saishi dakuma yanda shima Bai boye qaunar Laylah din ba ko a idanuwansa yasa takasa riqe komai aranta saima Suka dawo tausayinsu yayi rinjaye akan Jin zafin cin amanar da yayiwa momynta da mahaifiyar Laylah din Dan Haka tana qaunarsa saidai ba wani shaquwa a tsakaninsu musamman dayake Mata kallon wadda sbd itane mahaifiyarta take taimakonsu take riqe dasu duk da hakan ta wani bangaren itama Yana farin ciki da ingantacciyar rayuwar farin ciki da kwanciyar hankalin datake.

Sai gab da magriba tagama wankin lokacin tuni Momy tayi baquwa suka shige ciki Dan hakama wankin nata yayi sauri cikin tayita tashi kaiwa baquwar momyn ruwa da abinci.

Jin anfara Kiran sallar magriba yasa ta aje shanyar datake ta goge hannuwanta dasukai sanyi ta nufi gurin Abban da idanuwansa suke zuru dan dama hakan suke rayuwar kullum.

Maidasa ciki tayi tasaki labulai sbd sauro tana kokarin fitowa saiga abdullahi yashigo tace”

Anyi sallah Yaya abdullahi shima Abban sai yayi.

Eh dama shine nashigo Dan dubawa.

Ficewa tayi shikuma ya qarasa ciki yaja Abban zuwa toilet din dake dakinsa Dan Koda Abban na buqatan toilet.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button