Noor Albi

NOOR ALBI 16

Mamuhgee 16
Ranarda Ms Na’ima tadawo Bata shigo gurin Anne ba sai ta fake da cewar da zazzabi tadawo na sauyin yanayi,
Wanka tayi taci lafiyayyan abinci da masu aikinta suka jere Mata a babban dining din Dake sashenta.
Bedroom dinta Takoma tana wayoyinta hankali kwance cikin hutawa Dan kuwa USA takeda Shirin bin Turaki kowane lokaci idan tagama shirye shiyenta Dan babban abin data lura dashi ayanzu shine Kamar yana Kan magani
Dan Haka tagama daukan shawarar Haj Zinat qawarta binsa zatai ta maqale Masa ko bayaso Dan kila harda rashin Jin mace jikinsa yasa lafiyar tasa taqi samuwa a cewar haj Zinat,
Batason zuwa Dan batada raayin barin Nan Dan kuwa dukiya Babu irin wadda baya sakar Mata anan Dan taji dadin rayuwarta Dan Haka Bata raayin zuwa koina,
USA baida lokacinta tunda busy yake koyaushe hakama bazata sakata tayi yanda takesoba acan sbd wasu qaidojinsa da matuqar Yana gida Dole ake kiyayesu Koda anan ne kuwa yazo
Amma dai zata gwada binsa din ko shekara daya tayi taga idan zata samu Koda so dayane,
Koda sunan tsautsayi ya sadu da ita tasamu ciki
Idanma Bata samuba Idan ya sadu da ita din angama Mai wuya ciki Kota inane zuwa zaiyi.
Tana Gama wayar datake ta miqewarta a gado.

Sai dare tafito tazauna dining tafara cin abincin Daren Mai aikinta Kuma Yar rahotonta siddika tana tsaye gefenta bayan tagama zuba Mata abincin ta kalleta cikin zaquwa da fargabar fada Mata abinda takeson fada matan.

Ganin yanda saddiqan take Dan satar kallonta yasata kallonta Kai tsaye tana cewa”

Fada koma menene Dan nasan magana kikeson fada.

Dan so tayi ta waske da zancen Amma sanin Ms Na’ima din batada sauki yasata Dan gyara tsayuwa tareda qara matsowa tana rage sautin muryarta tace”

Anne tafiyar datai kwanaki tareda Turaki da zankada zankadan ‘yan Mata biyu tadawo masu tsananin kyau musamman dayar wadda da alama itace qarama
Kuma Kamar dai ba lafiyayya ba likita gareta kullum sai anzo gurinta
Hakama da alama Anne na tsananin sonta Dan ko yanda take Kiran sunansa a zaka gane,
Saidai babbar naga Kamar su halima sunfi bawa girma da alama itace kila Anne zata……
Kasa qarasawa tayi sbd mummunan tarin daya sarqe Ms Na’ima cikin tsananin firgici da baqin ciki tareda zallar mamaki.

Ruwa ta miqa Mata da sauri tana cewa”

Sannu,kiyi hkr bansan zancen zai damekiba Haka ba.

Ruwan tagama Sha tana kallon siddikar da jajayen idanuwanta da tari dakuma tashin hankali suka sauyasu ta aje ruwan tana cewa’

A Ina suke zaune?
Me kikaji Annen ta fada akansu?

A Sashen dake maqale da Annen Wanda yake kusan hade da nata,
Ita qaramar wadda sunanta Laylah ita naji Kamar Annen nata yabont kamanninta da Matar Aminin Sir Turaki wadda ta rasu
Itadai inaga riqo ta dauko ta sbd Yar Aminin Sir ce Wanda duk yazo kike cewa Yana zuwa dubosa
Dayar ce dai bansan komai akanta ba shiyasa nake zargin itace wadda Anne  ake cewa zata aurowa Sir Dan Bayan sun dawo agurin securities na gate din farko naji kamar Suna maganar an dauro aure da sir wallahi Amma ba tabbatarwa nay…..

Wani irin dannewar kirji takeji ta dagawa siddika hannu tana cewa”

Ya Isa kafin ki kasheni
Dama ke bana samun labarin alkhairi daga gareki kullum Kika fara bani rahoto sai ciwon zuciya ya kamani.

Shiru siddika tayi tana sake miqawa uwar dakin tata ruwa Aranta tana cewa”

Kekikace komai da komai na ringa fada Miki.

Miqewa Ms Na’imah din tayi tadawo Palo tana kokarin zama jikinta na rawa sbd duk mugayan labaran da siddika me kawo Mata rahoto a gidan ba kamar wannan,
Wani zafi da ciwo takeji cikin zuciya da jiki,
Ta yarda tabbas dama daga Anne har Turaki zasu qaunaci ‘yar Mahmoud sbd tsananin kaunar Dake tsakaninsu Dan Haka Dan Andauko Yar Mahmoud riqo ba matsalarta bace Dan itama tasan Dole zata nunawa ‘yar kauna da janta ajiki ko Dan wannan sabuwar hanyar kame Turaki da Anne ne takara samun durmiya cikin dukiyar gidan,
Babbar matsalarta da baqin cikinta tareda takaicinta da damuwarta shine ‘dayar da siddikar ke magana wadda tasan tabbas da wata niyar Akan Turaki Anne takawota gidan.

Kallon siddika take kallonta tana jiran  tagama fitowa tashin hankalin data Shiga tayi tace”

Me sunan dayar Dan kuwa yanzu Kai tsaye zanje na tambaya Dan bazan taba yarda da wannan rashin kauna da kashe Jin dadin da koyaushe Anne keson yimun ba,
Kafadamun komai da kikaji Kika sani,
kinzama Mara amfani ko kadan da zakice mun bakida tabbaci,
Meye amfaninki a gurina idan bakya da tabbaci akan duk wani Abu da kikaga alamar cutace gareni Zinat zankira nafada Mata bakida wani amfani tazo ta tafi dake…

Cikin rashin abin cewa da fadan Uwar dakin nata data Gama Shiga tension  da tabbatarwa siddika ta hada zancenta Dan bawa Ms Na’ima data Gama Hawa sosai sbd itakam ko a mummunan mafarki bazataso barin gidan Amb Turaki ba Dan Haka tace”

Dayar matarsa ce anriga an daura aure Kuma saboda ‘yar riqonsu da suka dauko aka aurota Dan ta kula da ita ace hannun matarsa take Kuma duk Dan sbd basuda magajin gidan ne yanzu itace magajiyar Anne da Turaki……

A haukace Ms Na’ima tace”

Da  dafarko ubanwa ya Hana ki fadan komai Kai tsaye kike fadamun Baki tabbatarba?
Siddika Allah ya kwashe Miki da wannan mugun labarin naki
Wallahi bazan yarda ba
Da anbani rikon ne ban karba ba daza’a auro wata kawai sbd riqo
Dan ita datai riqon ta riqe harda tarin dukiyar da za’a bawa yarinyar kenan
To idan hakan ne ai nice nasan taren Mahmoud din da Turaki..

Miqewa tayi ranta na tsananin Kuna zata give daga palon saiga Kiran Haj Zinat wadda siddika takira daga Nan inda take tsaye Dan itace kawai Mai iya dakatar da Ms Na’ima idan ranta ya baci idanuwanta rufewa sukeyi.

A matuqar hasalce ta daga wayar
Haj Zinat tace”

Karkije koina yanzu Yi zamanki gobe da wuri zanzo gidan musan abin Yi
Kinsan siddika munafuka ce karki hau zancenta duka kiyi abunda Zaki qarasa Bata kanki agurin Anne tunda dama ba wani Yinki takeyiba,
Idanma duka gaskiya ne ai a ruwan sanyi Zaki qwace riqon yarinyar Mahmoud din tadawo hannunki mu taru mu ringa nuna Mata gata da kauna
Kinga a sauki ga babbar damar mamaye zuciyar Annen dakuma ogan Mai gaba daya
Idanma tafiyarki tayi USA gurin Turakin sakata gaba Zakiyi kije da ita can danma yagani da idonsa yanda kike tsananin kauna da kulawa akan ‘yar tasu.

Haka Zinat tayita lallaba Ms Na’ima din harta fasa zuwa Sashen Amaryar bawai Dan ta sauko ko taji sassauci ko kadanba a ranta saima wani sabon zafi da tiririn datake ji tayi hanyar bedroom dinta tashige tabar siddika na Mata Saida safe cikin girmamawa.

Saida tashige siddikan ta juya ta nufi dining tafara kwashe kayan Kai tana gyarawa saiga Kiran Haj Zinat
A ladabce ta dauka tana cewa”

Eh tashige Bata tafin ba.

Siddika abinda Kika fada kin tabbatar dashi?
Idan kikai qarin zance Dan ki Kare kanki daga Na’ima Ni karkimun qarya  fadan gskia.

Sanin daga Haj Zinat har Ms Na’ima halinsu daya sbd Aminin gske ne yasa takuma fadar abinda tafadawa Ms Na’ima din Dan ko gskiyar tafada musu cewa batasan komai akaiba ba yarda zasuyiba karshema Mara amfani zasu kirata Kuma tsaf zasu iya korarta su sauyata duk da dadewar datai Mai tsayi ataredasu shiyasa duk lokacinda taga gskiyar zance Bata fiddataba abinda tasan shi sukeson rahotonsa take hadawa ta fada shiyasama takawo har tsawon lokacin ataredasu sirrinsu Babu Wanda bada Bata saniba Dan itace Yar aiken sirrinsu.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button