NOOR ALBI 6

Yanaji Yana gani Kiran yaringa shigowa Yana katsewa Amma baya iya dauka take hawaye suka ciko idanuwansa suna gangarowa ga azabar ciwo daya taso Mata ataken sbd tilasta kansa dayayi gurin son daukan wayar Bai ankaraba sai fadowa yayi sosai daga kujerarsa zuwa qasa
Momy data fito daga palonta tana waya taji karar faduwar tasa duk da Bata tabbatarda ko shidin ne yafadin ta katse wayar tareda juyowa tana kallon kafar palon nasa kafin dai taqarasa ciki da tunanin menene ya fadin,
Ganinsa qasa zube yanata neman juya kansa cikin azaba yasata qarasowa gurin tana kai hannuwanta duka biyu ta kamasa da dukkanin qarfinta daqyar ta dorasa Kan kujerarsa idanuwanta akansa cikeda mamakin ta yanda ya Fadi saidai ganin halinda yake ciki da hawayensa dasuka kasa tsayuwa yasata kasa magana tafara gyara Masa zamansa.
Wayarsace takuma daukan wani ringing din da Dan sauran karfinsa daya rage Masa ya kalli wayar Yana bayyarda buqatarsa ta tadaukar Masa wayar Dan Allah.
Juyawa tayi ta kalli inda wayar take
take gabanta ya buga da ganin sunan Mai Kiran ta zubawa screen din wayar ido.
Hannunsa Dake rawa yafara kokarin dagawa da neman nuna yanayi magiya akan ta taimakesa ta daga Masa Kiran.
Har saaidata kusa tsinkewa takai hannu ta dauka wayar tareda receiving Kiran tana kaiwa Kan kunnensa Abdullahi na shigowa da sallama Dan Haka ta fasa ta miqawa Abdullahin wayar tareda juyawa ta fice daga palon.
Da sauri abdullahi yaqaraso gurin abban tareda Ciro earpiece ya jona a wayar ya sakawa Abban ya Dan fita Dan basa guri yayi waya Dan idan zaiyi waya da Turaki bashi guri akeyi har saisun Gama.
Akaro na farko da Momy taji zuciyarta takasa nutsuwa da wayar Abban da Turaki sai zuciyarta ke Bata Kamar akwai wani abun daban dan kuwa zaquwar Abban da yanayinsa daya bayyanarda ‘dacin zuciya fiyeda kullum yasa taji tanason Jin abinda yake faruwa Dan Haka ta fasa komawa ta juyo ta dawo tana sako qafarta palon taji abinda Abban ke fada cikin kakari da kakkarwar muryarsa dake fita daqyar cikin tsananin azaba duk da likita ya hanasa takura kansa gurin mgn sosai Dan zai iya yiwa kansa illa Amma shine ya dage a hakan yake magana Dole?
Tabbas Yau tasake shaidawa da tabbarwa da Abban baya qaunarta da ‘yarta tun farko shiyasa ya zabi yaci amanarta gashi ayauma tanaji da kunnuwanta ya fifita kaunar ‘yarsa akan Sa’adah,
Ta Yaya zai bude Baki ya roki Turaki akan yabasa auren ‘yarsa…..
Tu.raki…..akwai…alqa..wa.rin aure tsaka..nin yayana…da..naka..idan ba..ka man..taba?
Allah..Haka..yayi damu..Akan cewan…hakan…bazata…Yi..yuba…tunda.. Allah…bai…kawo….naka…rabon…na haihuwaba…
Ayau…Ina..rokonka..Alfarma ta qarshe…wadda banda…buri ko fatar data wuce wannan alfarmar….
Nasan Allah yabaka girma….da daukakanda…kafi karfin Abinda Zan rokeka sbd banbance….da dama….
Ka cika… alqawarin hada…zuria Dani daka dauka akan…hada yayanmu auren nabaka….’yata ka aureta…..wannan itace Alfarma mafi girma dazakamun da har abada…bazan daina… gode makaba….
Innalillahi wainna ilaihirrajiun” momy yafara fada cikin mutuwar tsaye da mamaki da firgici tareda zallar mamakin Abban Dan kuwa kobai Kai zancen qarsheba tasan ‘yarsa daya ambata ba babbar yarsa yake nufiba ‘yar Dayafi dauka ‘ya ita yake nufi.
Dan Haka Bata tsaya qarasa Jin sauran zancenva ta juyo tadawo idanuwanta na rufewa cikin tsananin takaicin kanta da haryanxu taki yarda da Abban baya qaunarta tun farko shiyasa take qara haduwa da baqin ciki,
Tayaya zaiyi tunanin bawa Turaki auren yarinyarda ba itaba hatta uwarta ya girma?
Ta Yaya zaiyi tunanin bawa Turaki auren ‘yar Aminiyarsa Dan kuwa akwai shaquwa sosai a tsakaninsu Kamar yanda tasamu bayani?
Tayaya zai bawa mutuminda ko manyan masu kudi ba kowa yake samun damar ko gaisawa dashiba sai daqyar bare wannan da Babu abinda yake cikin kanta bayan aiki Dan Bata gane kowane yare saina aiki bayan ga Sa’adah Nan duk da itama turakin ya haifeta amma tanada ilimin bokonda zai iya Dan nunawa duniya ita matsayin matarsa duk matarsa tafi gaban akawo macenda zata nuna Mata komai a rayuwa sai ikon ubangiji.
Daqyar qyashin da shedan ya saka Mata ya barta takai kanta dakinta duk da tsoro ma na abun yafi yawa Dan kuwa Turakin tasan Koda kalau Abban yake shi kansa yanzu Turaki saidai a waya badai ya ringa ganinsa ba
ta zauna bakin gado tana aje numfashinta dake fita daqyar daqyar.