NOOR ALBI 11

Shiru Abdullahi yayi Yana sauraron Kawun kawai sbd fahimtar ba sauraronsa zaiyiba bare ya fahimci zancensa sbd ya tsinke da zance.
Kwana biyu da zancen suka kwasa zuwa Abuja
Suka fara sauka gidan Haj Karima sukaci abinci suka huta tareda salloli sai dare sukai Shirin zuwa gidan Turaki,
Da Alhaji Atiku da alhajin qarami sai Haj Karima umma Jamila dai bata biyosuba sai Kawun.
Da farko ko babban gate din farko da qaton gidan ba’a Bari sun qarasa ba bare shiga ciki su Isa gate na biyu Wanda dagashi sai harabar gidan.
Daqyar Suka samu ganin A Abdoul wanda tashin farko ya sanar dasu cewar Turaki yariga yashige Yana sashen Mahaifiyarsa wadda idan Yana can bamai Kuma ganinsa Dan Yana jimawa sosai daga can Yana fitowa yake shigewa.
Neman appointment din ganinsa gobe sukai ya sanar dasu cewar goben akwai tafiya Mai mahimmanci a gabansa Wanda zaiyi tareda Mahaifiyarsa.
Sunajin hakan Alhaji Qarami yace”
Idan harda Haj Anne zaiyi tafiya Inshallah ba tantama gurin duba Mahmoud zasu tafi sbd Babu zuwan dayake batareda itaba itama ta dauka Mahmoud tamkar ‘da.
Duk da hakan Dan karsuyi tsammanin daba shiba
Kawu ya kalli A Abdoul cikin nutsuwa yace”
Kayi hkr ka kirasa a waya kokuma kakira Haj Anne a waya kace Kawu saidu ne na Mahmoud.
Shiru Abdoul yayi Yana ganin girman Kawun sbd Kiran kansa da yayi a Dan uwan Alhaji Mahmoud Wanda yariga yasan irin Aminci Mai girma dake tsakanin Alhaji Mahmoud da Turakin duk da daga baya yasan labarinsu shida Turakin
Ta wani bangaren Kuma Yana jinjina tsari da kaidar Turaki Dan Haka ya kalli Kawun cikin Yar mutuntawa yace”
Kayi hkr Kawu gskia bazaku samu ganinsaba daga yau din har goben,
Amma idan har Yan uwan Alhaji Mahmoud ne ku taimako daya dazan bada shine ku koma gida ku jirasa sbd zuwansa duba Alhaji Mahmoud kamar kaidace da baya takewa.
Shiru sukayi dukkaninsu suna kallon makeken gate din gidan Da securities ke gadi Babu alamar zasu iya barinsu Shiga Koda kuwa da sakon mutuwar Mahmoud din sukazo bare,
Dan Haka sukaiwa A Abdoul din godiya suka juya
Tsabar Babu Jin dadin rashin damar ganinsa Tun a Daren sukai booking tickets washe gari qarfe Tara na safe suka biyo jirgi Suka dawo gida.
Tunda suka dawo shi kansa Kawun yakasa nutsuwa gida yakeson komawa Amma sun hanasa
Dan Haka a matse yake Kuma takure dason komawa.
Ganin wannan bazata fishesaba yasa abdullahi ya dauko Masa wayar Mahmoud din aka saka caji yace a Nemo Masa numbern Turakin Akira masa.
Kira Kan Kira Amma Bata Shiga Dan Haka Kai tsaye yace anemo Masa numbern Haj Anne Akira masa.
Cikin sa’a kuwa tata wayar tashiga Dan haka ya karba tareda nutsuwa yana jiran ta dauka.
Harta tsinke ba’a dagaba Yana Shirin sake Kira saiga kiranta yashigo wayar Kai tsaye ya dauka cikin tattaro nutsuwa da mutuntuwa yace”
Assalamualaikum
Haj Anne muna lafiya?
Ya gida?da iyali da Turaki?
Duk kowa na lafiya?
Cikin wata irin murya Mai tarin nutsuwa da Kamala tareda zallan ilimin bokonta Dana addini dasuke bayyane ciki lafuzanta tace”
Amin w slm,
Malam saidu ya gida ya iyali?
Lafiya kalau Alhmdlh Alhmdlh,
Ya Turaki? Ance Yana qasar nazo shekaran jiya bansamu damar ganinsaba Jamian kofar gidan sukace yariga yashige Kuma washe gari tafiya zaiyi
Sai kawai muka juyo Muka dawo..
Da mamaki a sautinta tace”
Subhanallh
Lallai ansamu kuskuren rashin sanine da tabbas Turaki bazaiqi ganinkaba kuwa duk uzurin Dake gabansa.
Hakane,shiyasa ban takura akan saina gansa din ba nabari idan yasamu zuwa duba Mahmoud ne sbd maganace Mai mahimmanci yasa naso ganin nasa.
Cikin bada hankali Haj Anne tace”
Allah yasa lafiya dai?
Ko jikin Mahmoud dinne?
Akwai wata matsala ne?
Zaka iya fadamun.
Numfashi ya sauke cikin sake nutsuwa da abinda zai fada yace”
Wata babbar maganace anan da Mahmoud yabar wasiyarta wadda na takeda Dan tsauri.
Uhmm Ina jinka..
Mahmoud yabar wasiyar cewa yabada auren ‘yarsa Sa’adah ga Turaki Wanda daga hakan Allah ya tsananta yanayinsa yake cikin halin Rai da mutuwa dayake ciki ayanzu,
Babban dalilin dayasa nazo neman Turakin nayi maganar dashi shine ita Sa’adah din ta Isa aure manema Bata zuwar Mata Amma anqi Basu dama sbd wasiyar Mahmoud din,
Da nazone naji daga bakinsa idan zai karba auren kokuma abawa wasu damar aiko nasu magabatan.
Shiru Anne Tayi tana juya zancen cikin ranta,
Duk da zancen yazo wani iri sbd banbancin shekaru masu yawa dakuma yanayin rayuwar Turakin da baya son mace cikin rayuwarsa shiyasa yakeda mace daya ita dinma daqyar yayi auren bayan ta nuna bacin ranta to tayaya zai iya qara wani auren da qanqanuwar yarinya ma?
Ta wani bangaren Kuma tunanin Mahmoud din tayi tasan bazai taba barin wannan wasiya Mai nauyi hakaba Babu dalili Mai kyau
Hakama batajin akwai wata buqata ko Alfarma da Mahmoud zai nema agurinta ko Turaki su kasa cika Masa ita ko wace irice matuqar Bata Saba addini ba Dan Haka Kai tsaye tace”
Allah yabasa lafiya yasa Munada rabon shaida wannan Alkhairi daya qulla ko acikin ciwo,
Inshallah Aure Kam an karba Allah yazaba Mana abinda yafi alkhairi
Zan sanarwa da Turakin da kaina saidai shi din ba mazauni bane kamar yanda kuka sani Dan Haka idan har aure za’ayi saidai ayisa kafin yakoma cikin satin nan
Saiku shirya Inshallah idan zamuzo duba Mahmoud din zamuzo da komai sai ayi agama ba Abu bane daza’a Tara duniyaba inaga ayi al’amarin a saukake kawai abada Matar.
Godiya kawu yashiga zubawa Yana kori mata addu’a sbd dama can yasan Haj Anne macace Mai kaifi daya kamar namiji Bata Wasa kai tsaye take komai na rayuwarta shiyasa takeda matuqar girma da daraja agurin manyan mutane da dama.
Labari na isarwa su Alhaji Atiku da umma Jamila take dangi kowa yaji Wanda Sa’adah zata aura hayaniya ta kaure ko Ina ya dauka a dangi masu murna nayi masu baqin ciki nayi,
Su kam masu abun tuni aka hau fara shirye shiyen auren duk da dai auren kawai za’a daura Haj Anne tace basa buqatan hayaniyar biki
Gashi idan sukazo za’a daura auren su tafi da ita sai Yan rakiyarta su umma Jamila.
Hankalin Sa’adah yaso tashi Sosai Jin Wanda zata aura saidai hankalinta Bai qarasa mugun tashiba Saida taji umma Jamila suna maganar da Momy a daki cewan Laylah Abban yabada ba itaba sauyi sukeson Yi da ita take jikinta yayi Sanyi Takoma daki ta zauna bakin gado gefen Laylah Dake zaune tayi zuru.
Kallonta Sa’adah tayi take Idanuwanta suka ciko da hawaye ta riqo hannun Laylan Ahankali ta furta”
Bazan taba karban abinda yake naki ba nawaba har abada Laylah.,
Duk da bakida lafiya Zan tsaya tsayin dakan kin zama Matar mijinda Abba ya zaba Miki Amma ta Yaya zakije wani guri rayuwar aure a Haka bakida lafiya,
Bakida sabo,
Baki tana zuwa koinaba arayuwarki.
Washe gari ba kunya aka dauko masu gyaran Amarya takanas Dan fara gyaran Sa’adah
Ta rufe idanuwanta ta tsaya akan bazata yarda da gyaraba bare auren matuqar baza’a yarda da buqatarta tason zuwa da Laylah ba.
Umma Jamila da Haj Karima sakin Baki sukai suna kallon tsabar taurin Kan Sa’adah din,
Umma Jamila ta hauta da fada tako Ina Rai abace
Sa’adah kuwa ta kafe harda saka kuka
Haj Karima dataga suna Shirin rasa hamsin Kan biyar tace sun amince taje da ita Amma idan tayi kwana biyu zata dawo da ita gida.
Kai tsaye tace ta amince da hakan aka rufe zancen aka fara shirye shiyen biki Wanda Amaryar take matseda ganin Kawu Wanda Kiri Kiri Umma Jamila ta hanata ganinsa qarshema dauketa tayi daga gidan tamaidata gidanta aka bar Laylah da kadaici.