Noor Albi

NOOR ALBI 20

Mamuhgee 20

Sungama session dan haka hutun dasukai Mai Dan kwanaki ne taso zuwa Nigeria Amma Mss Na’imah tace sai Ankara Gama wani session dinn
Anne ma ce Mata tayi ta zauna har gaban Dan Haka Dole ta hakura Amma taso tsananin ganin Anty Sa’adah wadda yanzu iyakacinsu vidcall Wanda kusan kullum awuni sai sunyisa yafi so biyu sbd yanzu Kam saidai raunin wani ilimin Kuma Amma wayewa da zama babbar yarinya Laylah tajima dakaiwa saidai nutsuwarta da sanyinta na Nan sai suka qarawa yanayin nata burgewa sbd sai yanayi kamar ajine da yayi Mata yawa,
Ta bangaren addini ma na laifi suna attending Islamic class a wata private school duk weekends itada Sofia Wanda ma sai daga baya da kansu suka gano gurin taiwa mum Na’ima mgnar aka sanyasu suka fara zuwa dakansu Dan ba laifi yanzu tana Jan mota sosai Dan musamman Turaki ya siya Mata motarta fara Sol kirar infinity QX50 wadda taqarasa sauya rayuwarta gabaki daya
Ga qananun kayan tuni tayi sabo da sanyasu tunda babu wasu kayan idan basuba,
Hakama ta bangaren ‘yan matanci Sofia ta Bata sosai dason kwalliya saidai dayake Bata Saba ba sai son jambaki kawai yashigeta Dan Haka duk wasu kamfanin lipsticks masu tsada ba kalar da batada Dan koyaushe kwalliyarta Bata wuce lipstick da mascara sai eyeliner duk da Bata cika sanyataba Dan idanuwanta sunfi Mata kyau ahakan gashi tayi haske sosai idan ta Sanya liner cikin idon sai tayi Kamar zata gurin wata biki ko taro shiyasa Bata cika sakawarba saidai lipstick da idan ya zauna bakinta yake qara Mata kyau da burgewa sosai.

Daga dakinta ta fito tana waya da Anne dake sanar da ita zuwansu Inshallah itada Sa’adah idan Sa’adah tasamu Gama exams din datake
Cikin tsananin farin ciki take tana cewa zata bisu idan sunzo tayi hutu itama,
ta nufi kicin tana cigaba da wayar tana Shiga Cindy dake hadawa Turaki black ginger tea ta dago ta kalla Laylan tana Mata nuni data jira tagama saisu hadawa mum dinta abinda tace Dan tafiya zatai.

Jin mum Na’ima tafiya zatai yasata kallon Cindy bayan tagama wayar tace”

Yaushe mum din zatai tafiya?
Banji tafada ba.

Siddika ce data Gama wanke qaton kifin dazasu gasa ta kalli Laylah tana cewa”

Yau zatai tafiyan Amma kaman kwana biyu ne zatai
Kuma nasan zata sanar Miki.

Gyada Kai Tai tana cewa”

Ok bani snacks dina Bari idan sunyi ku kashemun Zan wuce Sofia na jirana karatu zamu wuni Yi yau a gidansu.

Siddika hannuwanta ta kalla tace”

Hannuwana da kifi Zan Bata muku idan na taba.

Cindy ma Dake juye tea din data Gama dafawa cikin kulawa tace”

Tea din sir AB ne bari nakai Masa Yana jira saina dawo na hada Miki.

Kallon farin gold tray din dak hannun Cindyn tayi tareda miqa dogayen hannayenta da agogon Emporio Armani glitz ke daure akai ta karba tana cewa”

Kawo nakai saiki hada abubuwan.

Karba tayi ta juya ta fice daga kicin din Kai tsaye ta nufi hanyar palonsa na qasa dayake zama da baqi wani lokacin.
Tana Isa Tai knocking ahankali tareda tura kofar tashigo Jin A Abdul yace tashigo Dan yasan Cindy ce dayace ta kawowa Turakin tea.

Qamshin turarenta na splendid wood(Yves saint Laurent) yafara shiga hancinsa yaci gaba da abinda yakeyi batareda ya dago yaduba Wanda ya shigo din ban Dan yasan itace tunda yasan qamshin turaren Na’ima ba wannan bane hakama qamshin bana Cindy bane datake maid.

A Abdoul ya dago yana ganinta kallo daya yayi Mata ya dauke kansa daga kallonta Yana maida kallonsa kan Turaki Dake duba iPad sbd Ganin kayan Dake jikinta.

Qarasowa tayi ahankali ta gaidasa tareda gaida A Abdul din shima tana kokarin ajiye tray din Turaki ya dago idanuwansa suka sauka Kan dogon pencil jeans din Dake jikinta Wanda ya fitarda tsayi iya kaurin cinyoyinta harma da fadin hips dinta Dan rigar jikinta Satin wrapped blouse ce batada wani tsayi kanta daure da scarf fari Hasken fuskarta dake glowing yafara maida kallonsa akai kafin ya maida idanuwansa Kan siraran cinyoyinta yanason mamakin fitar tata ahaka Amma dai baice komaiba ya amsa gaisuwarta tareda maida kallonsa kan A Abdul daya dauke Kai yaqi waiwayowa Yana duba wayarsa.

Juyawa Tai ta fice
Yakuma Dan dagowa ya kalla kofar data fita kafin ya dawo da kallonsa kan abinda yake Yana daukan tea din yafara Sha suka cigaba da abinda sukeyi.

Tana fitowa Kai tsaye dakinta taje ta dauko handbag dinta da keys na motarta ta fito ta nufi tana kokarin Sanya half-zip jacket akan kayanta ta nufi dakin mum Na’ima
Anan take sanar da ita tafiyar gaggawace ta kamata zuwa Athens kwana biyu zatai tadawo.

Daka tawa da fitarta tayi Saida mum din tagama suka fito tare Dan takaita airport,
Koda suka fito itace agaba saddika na bayanta da luggage din mum Na’ima sai Cindy dake gefenta dauke da nata snacks din suka saka a mota suka juya ciki daidai fitowar Turaki Wanda ke gaba Ms Na’ima na gefensa idanuwansa suka sauka akanta lokacinda take tsaye jikin motar hankalinta nakan wayar Dake hannunta..
Lipstick dinta daya zauna dakyau akan lips dinta ya kalla kafin ya dauke Kai Yana sake kallon shigar tata
Ya wuce ya shige motarsa da A Abdul ke jiransa suka fice daga harabar gidan.
Suna fita Suma su Laylah suka fice ta biya ta dauka Sofia suka kaita airport sbd hanyar airport din Bata Gama ganewa dukda Google map take amfani da dama zuwa gurare.

Bayan tafiyar mum Na’ima duk sai taji kadaici ya kamata Dan Haka sai kusan yamma tadawo gida daga gidansu Sofia
Tana dawowa wankan kawai tayi bayan tayi sallah ta saka doguwar free  chiffon shift gown tasaka tareda hula ta fito tana qamshin mist na Creed ta nufi palo ya zauna tana Yan latse latsen wayarta har lokacin sallah yayi Takoma daki tayi sallah
Lokacin cin abincin dare nayi tafito Kai tsaye ta nufa dining room bakowa Dan dama tunda sukazo qasar masu aiki suka daina shigowa dining room lokacin cin abincinsu
Ms Na’ima ce ke serving dinsa.

Zama take kokarin Yi saiga isowar qamshin bois elite Dan Haka tasan shine zai shigo saita fasa zama ta dakata tareda waiwayowa kadan Jin shiru
Tana kalla kofar Yana sanyo Kai sanye cikin Armani’s da slippers gashin fuskarsa akwance sosai farar fuskarsa sai cika ido takeyi
Bata ankaraba sai Jin idanuwansa tayi cikin nata ya dago ya zuba Mata nasa dasuka shanye nata girma da haske,
Faduwa gabanta yayi da sauri ta sauke Kai tana cewa”

Barka da saukowa Abbah.

Amsa Mata tayi Yana qarasawa gurin zamansa ya zauna.
Juyowa tayi ta nufosa zuciyarta na bugawa da idanuwansa dasuka shiga nata saitakejin kamarma tsoro ya kamata da rudu Dan Haka jiki amace ta qaraso batareda takuma dagowa ta kallesa ba Dan yaune Karo na farko da idanuwanta suka taba shiga Suka hadu da wani
Duk da tamkar uba yake gareta Kuma mijin Yar uwarta saitaji fargaban hakan yashigeta.

Gasashen kifine akai da akai garnishing dinsa dasu lemon
Sai fruits da farar pasta.

Matsowa Tai tazo gefensa ta tsaya ahankali,

Qamshintane ne yayi wa hancinsa shigar qarfi daidai lokacinda ta tsaya gefensa zuba Masa Masa abincin.

Agogon diamond Rolex Dake hannunsa ya kalla Yana dan maida bayansa jikin kujerar dining din ya jingina sbd dauke hancinsa daga gurin Dan akaron farko da yaji qamshin mace ya damesa ga lokacin Shan maganinsa ya kusa sbd maganin dayakesha yanzu yafara basa reaction shiyasa ya rage tafiye tafiyensa ayanzu Yana buqatan tsayawa kusada gida.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button