HAUSA NOVEL

Rabo Ajali Episode 1 – 15

[7:00am 11/11/2016] ◆◆ RABO AJALI ◆◆7
By Sulaiman Bomboy
Daren ranar bayan sun gama hirah da mamanta
ta nuna
mata ta hakura da maganar alhj basheer, mum ta
yi murna
sosai dajin hakan daga bakin oyiza,
sai gurin sha ďaya taga mum na hamma ta
dafata tace
mum bacci kike ji, mum tace eh bacci sosai
nakeji bari inje
in kwanta, oyiza ta mike tace bari in kara gyara
miki ďaki
saboda kiji dadin bacci da kyau,
mum tayi murmushin jin dadin ganin yadda yarta
ke
tarairayarta, dakinta oyiza ta wuce ta yaye
shimfiďar zanin
gadon tasanya mata wani fari kall a kasa sannan
ta ďaura
nata akai,
idonta yayi ja lokacin da ta dauko wata kwalbar
farin
magani zata yayyafa a gadon, sai da ta ďan
zubar da
hawaye sannan ta yayyafa maganin ta fita taje ta
taso mum
da ta fara bacci,
har ďaki ta rakata ta rufo kofar ta koma ďakinta
tayi tagumi
tana jiran dare ya raba ta tafi gurin meeting, ,,
2:45am
Tsugune suke gaban “CHUMMY LORD” cikin
jajayen kaya
su kusan goma sha biyar maza da mata masu
neman arziki
da mulki,
jini ne a kwarya wani bakin mutum ya ďauko ya
mika ma
wacce take gaba ta sha ta mika ma sauran duk
suka sha
sannan suka ajiye kwaryar, wani irin kirari haďe
da ihu
“chummy” tayi akan wani farin kyalle sai ga wasu
yara
yanmata basu wuce shekara 14 ba sun bayyana a
gabanta
cikin night gown, yara ne farare kyawawa masu
kama da
juna da ganinsu yan biyu ne,
a firgice yaran suka fara waige2 suna kankame
junansu,
chummy tayi dariya sosai tace Alhaji Sambo
aikinka yayi
kyau lallai ka tabbatar kana son cin wannan
kujerar,
da sauri yaran suka fara kallon mutanen gurin ko
zasu ga
wanda aka kira da sunan mahaifinsu, jikinsu ya
kara rawa
lokacin da idonsu ya sauka akan babansu mai
kaunarsu
dare da rana wanda a wannan daren kafin su
kwanta bacci
saida yayi yawo dasu cikin garin abuja da
kewayenta ya
kashe musu makudan kudi na ban mamaki, cikin
rawar
murya suka ce PA–PA,
alhj sambo ya sunkuyar da kanshi kasa,
daya daga cikinsu tayi karfin halin zuwa gabanshi
ta
dafashi dan gani takeyi kamar mafarki takeyi,
jin da gaske shi ďinne yasa ta rusa ihu ta kalli
yar uwarta
tace “Fanne” ba mafarki nakeyi ba wallhy papa
ne, meyasa
zaka mana haka, yanzu ashe neman duniya zai
iya saka ka
bayar da ya’yanka na cikinka,
papa sanda zaka bada damu bakayi tunanin
bazaka kara
ganin mu ba,
cikin fushi dayar tace “Fanna” meye a ciki dan ya
bada mu
an kashe,
kika san iya adadin mutanen da ya kashe saboda
neman
duniyarshi,
kukan me kikeyi? Saboda bazaki kara shakar
iskar duniya
ba kome?
Inda zamu tafi nan zai zo yau ko gobe ko jibi in
kwananshi
ya kare shima,
gara ma su kashemu da zama karkashin zalunci
da cin
kudin haram da na kawunan mutane,
wani mugun mari aka dauketa dashi ta waiga ta
kalli bakin
mutumin zuciyarta ta kara zafi tace ba mari nake
bukata ba
kashemu zakayi mu huta,
“chummy” tayi dariyar kusan minti uku sannan
tace ai dama
kun mutu ruhinku ne anan,
in naso zan iya barin ruhinku yayita yawo shi
kadai a duniya
gangar jikinku kuma tana rami,
Fanna tace ki so din,
fanne tayi saurin cewa dan Allah dan annabi ku
maida mu
gurin mammi ta waiga ta kalli mahaifinta tace
papa kaji
tsoron Allah,
Oyiza cikin Fushi tace chummy lord yaran nan na
bata
mana lokaci gashi har asuba ta gabato ga kuma
mum can
daure gara ayi mata abinda za’ayi in wuce gida,
Fanne ta waigo ta kalleta a hankali tace mum? U
mean
mum dinki kika bayar saboda— wannan karan
chummy ce
da kanta ta kai mata duka a baki,
chummy tace bazan kashe yaranka yanzu ba alhj
sambo
dey wl be under my control, zan watsasu duniya
saboda
naga za’a dama dasu,
fanne tace karya kikeyi jininmu ne yafi karfin ki,,,
chummy tayi murmushi tana girgiza kai,,
Alhj sambo cikin tsoro yace my lord ina tsoron
kar suyi min
illa, chummy tace babu kai babu su saboda zaku
binne
gangar jikinsu a grave so ka kwantar da
hankalinka, yayi
ajiyar zuciya yana kallon hararar da fanne take
musu shi da
oyiza,,,
dafa kansu chummy tayi da wata sanda mai
kyalli nan da
nan suka bace,,
Mum din oyiza kuwa kuka ta dingayi ganin
ďiyarta ce ta
bada ita, gaba daya magana ma kasa fita tayi a
bakinta sai
girgiza kai kawai takeyi tana tunano rayuwar da
tayi da
yarta,
cikin minti goma aka gama da maman oyiza suka
gama
shaye shayensu sannan kowa ya bace, ,,
Kuka oyiza takeyi a bakin gadon da mum ke
kwance tana
ihu makotan da ta aika mai gadinsu ya faďa
musu suna
kanta suna bata hakuri,
ta kira can kauyensu ta fada musu suma suka
dinga ihu
suka shirya suka kamo hanyar abuja,
Guraren karfe biyu akayi mata sutura da kyar dan
yan
uwanta sunce saidai su kaita can okene a binneta
ita kuma
oyiza ta kafe saidai a binneta anan saboda
tsoron kar
asirinta ya tonu dan tasan kakarta na ganinta
zata san abin
da ya kasheta dan itama mayyar kanta ce,
saida malamai sukayi ma yanuwanta nasiha
sannan suka
yarda akayi mata sutura aka kaita gidanta na
gaskiya…
Washe gari ta kira john a waya tace yaje ya buďe
shago in
alhj basheer yazo ya kawoshi gidansu,
haka kuwa akayi yaje ya bude shago amma har
dare babu
alhj basheer, washe gari ma haka,
oyiza hankalinta in yayi dubu ya tashi tana ta kai
kawo
saboda rashin zuwan alhj basheer gashi har an
kusa sati
daya,
a daren ranar ta bayyana gaban chummy da
matsalolinta,
chummy ta gama incantation dinta tana girgiza
kai tace
yana karkashin kulawar matarshi,
ta nuna mata wata kwarya,
bakar mace ta gani a ciki sanye da hijab tsaye
gefen gadon
mijinta dake bacci tana sallar dare in ta idar sai
tayi adduoi
ta tofeshi dashi sannan ta mike ta kara tada
kabbara,
chummy tace kin gani da idonki ko? Oyiza ta
haďe rai tace
na gani amma ay ni babu ruwana da wannan,
mum na
bayar saboda haka so kisan duk yadda zakiyi,
chummy tayi dariya tace dadina dake wutar ciki,
trust me
Oyee cikin satin nan za’a daura miki aure da alhj
basheer,
cikin farin ciki oyiza tace yanzu naji magana…..

◆◆ RABO AJALI ◆◆ 8⃣
By SULAIMAN BOMBOY
Alhaji basheer tsugune yana gyara canvas din kafarshi cikin
shigar blue nd white track suit,
mikewa yayi bayan ya gama ya kalli matarshi zeenatu dake
gyaran gadon da ya tashi yace to ni na fita training, tace to
a dawo lafiya yallabai,
yace Allah yasa sannan yasa kai ya fita,
Zagaye ya dinga yi yana jogging cikin farin ciki saboda
yadda sanyin safiyya ke kaďashi,
yayi zagaye na tara yana yi yana hutawa, a zagaye na
goma ne ya hango wani shima jogging din yakeyi dai2 gurin
wata katuwar kwata kafarshi ta gurďe ya tafi zai faďa alhj
basheer yayi saurin rikoshi yana fadin subhanallah sannu,
mutumin ya ďago yana gyara kafarshi yace yauwa nagode
sosai gaskiya ka taimake ni, alhj basheer yayi murmushi
yace mu gode ma Allah, mutumin ya mika ma alhj basheer
hannu yace sunana Bara’u ina nan zoo road, “BB close” opp
gidan alhj Basheer Balarabe,
Alhj basheer yayi dariya yace ni kuma sunana Basheer
Balarabe (BB) nima ina zaune a zoo rd BB close cikin gidan
Alhj Basheer balarabe,
Alhj Bara’u yayi dariya sosai yace ikon Allah alhj basheer,
kaga yadda Allah ke abunshi ko, .
alhj basheer yayi dariya yace kai gaskiya bamu fitar da
hakkin makobtaka in ba haka ba ga gida ga gida ace bamu
san juna ba,,
Alhj bara’u yace ko 1week banyi da tarewa ba kuma nasa
ayi min magana da duk makota na kai kaďai ne Allah baiyi
zamu hadu ba saboda ance min baka gari,
alhj basheer yace kwarai kuwa ban daďe da dawowa ba, to
ya unguwar tamu da fatan dai baka samun matsala,
Alhj bara’u yace walhy babu matsala unguwar cike take da
mutanen kwarai naji dadin kasancewata cikin ku, Alhj
basheer yayi murmushi suka fara tafiya yace to ya iyalin fa,
Alhj bara’u yace tukunna dai har ansa rana jiranta nakeyi ta
karasa skull zuwa nan da 3monts sai ayi in shaa Allah,
Alhj basheer yace Allah ya nuna mana kai kadai ne a cikin
gidan kenan, alhj bara’u yace eh ni kadai ne amma
weekends a daura nakeyi saboda rashin iyali, alhj basheer
yace hakan yayi Allah ya taimaka yace ameen har suka
karaso gida suna hira cikin kankanin lokaci suka saba da
juna, a dai2 kofar gida sukayi sallama kowa ya shiga gida,
kanshi tsaye yake tafiya cikin gidanshi yana amsa gaisuwar
masu musu hidima, yazo gab da shiga parlo yaji wata
muguwar faďuwar gaba,
juyawa kanshi ya fara yi sosai ya dafeshi ya karasa parlon
dakyar ya zauna kan kujera, zeenatu na can kitchen bata
san halin da mijinta yake ciki ba,
runtse idonshi yayi siffar Oyiza ta dinga mishi yawo a cikin
kwakwalwar kanshi, buďe idonshi yayi da sauri da ya tuno
da oyiza gaba daya yaji wani abu ya tokare mishi kahon
zuciyarshi, ga wutar son ganinta da ta ruru a zuciyarshi
kamar wacce aka iza da petur,
mikewa yayi da sauri ya shiga bayi yayi wanka sharp2 ya
fito ya shirya da gaggawa ya feshe jikinshi da turare ya debi
kudi a sv dinshi na gida masu yawan gaske sannan ya wuce
kitchen ya sami zeenatu,
Cikin rashin fahimta tace tafiya weekend kaiko ina zaka,
yace abuja zeena alheri ne yake kirana,
tayi murmushi tace to Allah ya kawo mana alkhairin tare,
yace ameen yar matata sai na dawo, tace to Allah ya tsare
ya kuma kiyaye hanya, yace ameen ya fita da sauri,
biyoshi tayi da gudu tace na manta ban fada maka ba, dan
Allah zan shiga gidan Malam atiku gurin Ma’u tayi min
kitso, yace to adawo lafiya tayi miki mai kyau fa, tace karka
ji komai in dai kitson ma’u ne, yayi murmushi ya fita ya
tafi…
Da kyar ya gane restaurant din, yana isa ya fito cikin farin
ciki,,
tsayawa yayi turus saboda ganin gurin da yayi a rufe,
jingina jikin motarshi yayi ya rasa me ke mishi daďi yanzu
wa zai fara tambaya inda take anan gurin, ya kusa 30mins
kafin ya shiga motarshi da niyyar tafiya,
kamar daga sama ya hango john yana bude gurin,
fitowa yayi da sauri kamar wanda akayi ma albishir da
gidan aljanna, karasawa yayi yana kiran yaron, john ya juyo
rai a bace saboda yadda yaji ana kiranshi ganin alhj
basheer yasa john jindadi ya fito da gudu ya tsuguna a
gabanshi ya gaishe shi,
alhj basheer ya amsa suka shiga ciki,
ya kalli john yace ina madam dinku, john ya raunana fuska
yace madam is no more alhj tun ranar da kazo washe gari
ta mutu, alhj basheer ya girgiza kanshi cikin tausayin oyiza
yace Allah ya jikanta to ina yarta oyiza,
john yace tana gida dama tace idan kazo in kaika can gida,
alhj basheer yaji dadi sosai a ranshi dan a tunaninshi kafin
mahaifiyarta ta rasu tayi mata bayanin komai, tashi yayi
suka fito shi da john suka shiga mota suka wuce gidansu
oyiza…
Bayan ya gama yi mata gaisuwa yana rarrashinta saboda
kukan munafurcin da take yi ita a dole tayi rashin uwa,
tausayinta sosai ne ya ratsashi ya tambayeta ko
mahaifiyarta tayi mata bayaninshi,
tayi kasa da murya tace eh a daren ranar ta fada min komai
kuma tace in ka dawo zata yarda ka aureni, ta fashe da
kuka tace ashe bazata ga auren ba,
alhj basheer zuciyarshi ta kara narkewa yace kin yarda to
zaki aureni, tayi kasa da kanta tace ko banaso zan yarda
tunda shine last will din mahaifiyata, alhj basheer yace haka
ne naji dadi sosai da kuka amince dani, yanzu ina son cikin
satin nan a gama magnar komai muyi aure in tafi dake,
wani daďi ya ratsata tace to ba matsala bari in turo maka
kanin babana kuyi magana, mikewa tayi ta shiga ciki ta turo
mishi kanin babanta da wan mamanta,
Kudin da alhj basheer ya wankesu dashi da kuma nuna
yanason ya auri oyiza saboda yana tausayinta shi kadai
yasa suka yarda da auren suka sa rana ya biya sadaki da
komai, sannan ya tafi cikin farin ciki,
A daren ranar ya fita da oyiza yawo ya siyo mata duk wani
abu da mace zata bukata na aure,, sun daďe tare har suka
saba sosai kafin su rabu,
Tana shiga gida ta dinga tsalle tana murna nan ta shirya ta
wuce gurin chummy yin godiya….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button