Uncategorized

SALON SO 39-40

 ????????????????????????????????????????            ???? SALON SO ????

????????????????????????????????????????

    BOOK ONE ????

Story & written by

Mommyn fareesa

   ????️ 39&40

Lumshe idanuwanta yasmeeen tayi tanajin  wani irin farin ciki aranta”

tana ahakan taji motsin zai shigo motar”

daidaita nutsuwarta tayi tana murmushi”shima murmushin kwance akan fuskarsa”yashigo yana cewa sonake da kanki kiyi feeding nawa”nima da kaina zanyi feeding naki kin yarda?”yafad’a yana k’ok’arin saka k’wayar idanuwansa acikin nata”tsintar kanta tayi da cemasa Eh”sbd tasan idan ta musa masa zasuyi fad’a ne”

      gyara zamansa yyi yana fuskantar  ta yarufe k’ofar”ya aza mata ledar ice cream d’in asaman cinyarta”

      kanta ak’asa tana wasa da yatsun hannuwanta masu jan lalle”

     murya can k’asa yace” k’auyancin meye haka yasmeen??”idan nafahimta kunya kikeji kome??”yafad’a yana kallon ta”

kunya ai adoce ko?”tafad’a batare data kallesaba”

hakane amma ni banaso kinajin kunya ta”kinga yanzun 5 ta wuce kinaso kiyi magrib awaje?”

Ah ah wlh”muje dan Allah kamayar dani gida”idan kinga munbar nan to mungama shan ice cream d’in nan”

  

   batace komaiba ta bud’e ledar”ta fito da rober guda “bayan ta bud’e tasaka spoon d’in”d’ebowa tayi ta d’ago kanta suka had’a ido”turo baki tayi tana d’auke idanuwanta dg kansa tace”.nidai kadena kallona”

    Laifine dan nakalli wacce bataso namutu?”

murmushi tayi tace”.ah ah tana nufar bakinsa da spoon d’in”tayaya zaki dinga bani abu bakya kallona saina k’ware ne??”

      yaya Aliyu kaima Allah rigimammene!duk rigimata ai bankai kuba keda imaan ko?”

yanzun yaya kakeso nayine?”juyowa zakiyi ina baki kina bani muna fira har mugama”

batayi musuba ta juyo sosai ,shima yad’auki spoon yafara b’ata”suka dinga feeding juna”dukda yasmeen atakure take”mr Aliyu kuwa ko ajikinsa”

gaba d’aya yasmeen takasa sakewa”lura  yyi da hakan yasakashi cewa yama k’oshi”

nima yaya Aliyu na k’oshi”wannan robar guda ka kaiwa imaan dan Allah”

zanje dashi nasha anjima”nidai ah ah imaan nabamawa”yana tada motar yace”.to waye yasiya?”

Kaine mana”amma kuma waka siya mawa?”

yasmeeen kinada wayo sosai”yanzun naji zanje mata dashi shikenan?”yafad’a yana bawa motar wuta….

wani boutique suka wuce, yasaka adole yasmeen ta jidarwa  Ahmed kaya y’an kanti masu kyau”ta k’yar tasamu yabari ta d’aukar masa kala 10″asma’u aka d’aukar mata dogayen riguna kala5″ suma tasanar masa kar umma tayi fad’a…sai gab da magrib suka iso gida”yasmeen nata masa godiya da adduar samun bud’i da rahama ga mahaifiyar sa”wanda haka yasakashi nishad’i”

     yaya Aliyu nah!juyowa yyi suka had’a ido yad’age mata gira guda yana shafa kansa yace”yes my baby yasmeen….

 murmushi tayi tace”.na wuce sai kuma gobe insha Allah”ka kula da kanka Allah yatsare ku kaida imaan a duk inda kuke”

Ameen thank you so much my yasmeen”

sai mun had’e a online ko?”Eh insha Allah tafad’a suna yin sallama ta d’auki kayan ta wuce gida”

      Ab’angaren su anty lokacinda zakiyya ta dawo tasanar mata yadda tasamesu”

Hankalinta yatashi”amma datayi wani tunani”sai taja kwafa tace”.idan yasan wata ai besan wataba”

Ai akwai hanyoyi da yawa zamu sake bin wata hanyar”

zakiyya tace”. damuwata y’ar iskar yarinyar can (yasmeen)nifa ina zaton sonta yakeyi wlh”

inma sonta yakeyi da gaske bazai tab’a mallakartaba indai ina raye……

    *************

mr Aliyu masjeed yawuce yyi salla,kafin yadawo gida yabawa imaan icea cream d’in ta”

Parlourn sa yawuce yazauna ya d’auki wayarsa”

Online yahau yaga yasmeen itama tana online d’in”

murmushi yyi yamata mgn da cewa”

Dawa dawa kike chats??”

   ” nida friends nawa”

Okay”kidena kulasu dani kawai zakiyi chats”to shikenan yaya Aliyu nah”ta masa reply da emojis na murmushi”

Reply yamata da meye labari to?”

    Uhmmm! kaidai zaka bani labarin ban dariya”

saidai nabaki naban tausayi”idan nayi kukafa?”

MAI NASSARA meke damun ka ?”inata sallama harna shigo amma hankalinka nagun waya”

Cewar khaleel yana fisge wayar”yakalli screen d’in”my baby yasmeen”yagani a number d’in”

Mr Aliyu banza yamasa yak’i mgn”sbd yabashi haushi daya karb’e wayar”

Khaleel ya aza masa wayarsa ajikinsa yana k’yalkyata dariya”

Mr Aliyu yatab’e baki yana kashe datar yace”.da alama week end d’in tazo maka dayin gamo ko?”

Hmmm abokina kenan dad’i na da yau da gobe saurin zuwa”

kaida wacece kuke chats  gaba d’aya baka anutsuwarka”hankalinka nagun ta??”

tamke fuska mr Aliyu yyi yace”.kaga mlm dakata yasmeen ce muke chats da ita akan abinda yashafi aikina” zakayi mun wata fassara daban…..kafin khaleel yyi mgn imaan tashigo cikin parlourn”

tana sanye da jallabiya bak’a”tayafa d’an kwalin”

suna had’a Ido da yaya khaleel yasakar mata tsadaddan murmushi”

k’asa tayi da kanta akunyace tace”.yaya khaleel ina wuni?”

Imaan y’ar gidan daddy, kuma y’ar gatan yayanta”lafiya qlau ya shirye shiryen exams?”

Munatayi yaya khaleel sai atayamu da adduar samun nassara”

Khaleel nak’ok’arin mgn wayar mr Aliyu tayi ringing”yana dubawa yaga yasmeen ce”

Tashi tsaye yyi yawuce bed room d’in sa”sbd beson yad’aga agaban khaleel”

Shikuwa khaleel yaganosa”murmushi kawai yyi yana kallon imaan suka cigaba da fira”

ganin mr Aliyu beda lokacin fitowa kawai yayiwa imaan sallama” bayan yasanar mata ranar bathday nata dazata cika15 yrs zai sanar mata da wata mgn”

    

     *bayan wasu kwanika dasuka wuce*

Abubuwa sunfaru da yawa”aciki harda tashin su yasmeen dg anguwar kawo suka koma anguwar sarki”agidan da mr Aliyu yabasu kyauta”wanda saida baba me kuka da khaleel suka saka baki umma ta amsa”

  gefe guda kuma ansaki sanusi da d’ahara”wanda sanusi yaji jiki”kuma yasha warning akan yakiyayi yasmeen”

aikuwa yaji tsanarta da kinta aransa shida baba d’ahiru”daya dinga ikrarin bazai d’aurawa  yasmeen aureba”

yasmeen kuwa shak’uwar data shiga tsakaninsu da mr Aliyu bata misaltuwa”ta wuce wasa”bayason ganinta cikin damuwa ko fushi”

da wannan damar tayi amfani aka maido salim bakin aikinsa”

daga ita har mr Aliyu wani irin masifar son juna suke da kishin juna” amma basu gane sunayiba azatonsu shak’uwa ce”

yasmeen tasakeyin haske ta murje ,takara kyau da wayewa”sbd canzawar sutura da cimaka dakuma kwanciyar hankali”

Ayanzun haka yasmeen acikin kud’in ta tasiyawa umma injin markad’e da fridge tana sana’arta ashigo cikin gida asiya”

Kuma masha Allah umma nasamu”

Ahmed nasamun kulawa da ingantattun magun guna da mr Aliyu yasiya masa”hakan yasa ciwon yarage tashi bakamar daba”

       Anty kuwa gaba d’aya ayanzun burinta takawar da mr Aliyu adoron k’asa kota halin k’ak’a sbd cikar burinta….

ayau yakama Friday”k’arfe 1:am suke tashi”

mr Aliyu na wajen meeting”amma gaba d’aya hankalinsa nagun yasmeen”dake office nashi tana masa aiki a loptop”

dalilin dayasa kenan bema zo da itaba agun meeting d’in”

Ana gama meeting yanufo floor d’in”

wani irin bak’in kishi mr Aliyu yaji yatokare masa akirji”sbd ganin wani yaro sabon ma’akaci suna mgn da yasmeen”tana murmushi…… d’ago kanta dazatayi sukayi 4eyes da mr Aliyu….✍️

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button