SALON SO 41-42
???????????????????????????????????????? ???? SALON SO ????
????????????????????????????????????????
BOOK ONE ????
Story & written by
Mommyn fareesa
????️41&42
……..ayanayin yadda yasmeen taga fuskarsa” ta tabbar dayaji haushin ganinta da suraj”(cours mate nata) yyinda suraj besan matsayinta a company d’in ba”sbd yau
yafara ganinta aciki” shikuma befi 1 week da fara aiki anan ba”shikansa Suraj d’in yanayin yadda yaga yasmeen tazama yasaka yajuyo yaga metagani?”kawai yaga mr Aliyu na nufo wajen”da sauri yasmeen tace”.suraj kaje sai anjima”ina zaije?”yafad’a murya akausashe”yana k’arasowa kusada dasu”dg yau kadena aiki anan…. subahanallahi!menayi ogah?”suraj yafad’a arikice yana kallon mr Aliyu dake jifarsu da wani irin kallo”yasmeen na k’okarin yin mgn”kallo d’aya yamata tajuya da sauri tabar gurin ta wuce office nashi”
kallonsa yamayar agun suraj”kafin yace”.laifinka shine kulata dakayi”anan ba’a mana fira”sbd bashi yakawo muba”and last warning ko a gida kuka had’u da yasmeen”ka kulata wlh abinda zan maka saika raina kanka”suraj atake yafahimci kishine kedamun mr Aliyu”yaso yabashi hak’uri amma yak’i sauraronsa”hakan yasa yabar gurin kawai”shikuma mr Aliyu ya wuce office nashi”
yasmeen na zaune akan kujerar dayake zama”atsorace take da masifar dazaizo yamata”ak’asan ranta tana addua Allah yasa k’arya kori suraj”
bata gama wannan tunanin ba yashigo”
sak mr Aliyu d’in sa nada yadawo mata”ke wai yaushe nafara wasa dakene?”ban isa nakafa miki doka kibi bako?”
To wlh nakoma ganinki da wani d’an iska sai kin gane kuranki”
d’ago kanta tayi ahankali tace”.kagama fad’an?”ban saniba”kaddai ace kakori suraj?”
Eh nakoresa yakuma koru”wai meyasa wani lokacin bakayiwa ma’aikatan company d’in nan adalci?”
Okay rashin kunya zakimun sbd narabaki da wannan d’an iskan?”
yaron nan d’an iskane!amma ke kinkasa kigane ko?”
wai dan Allah ina ruwanka to?”
“Idan d’an iskane ai betab’a mun maganar banza ba”
yasmeen nikike cewa ina ruwana?”
yaya Aliyu meyasa wani lokacin baka fahimtata?”
da kaina nake neman shawara agunka”bana tsallake umarninka” kasani inamaka biyayya”
Amma shikenan tunda kafin son kullum raina yana b’aci shikenan”tafad’a hawaye na wanke mata fuska”
Har yanzun be sauka dg dokin fushin daya hauba”zama yyi kan kujera bece komaiba yanata huci dajan tsaki”
yasmeen ta tashi tsaye,hakan yyi daidai da shigowar khaleel da shirinsa na zuwa masallaci”
yasmeen bata ko kallesaba tayi ficewarta”khaleel nazama gefen mr Aliyu yace”.abokina meke faruwa ne?”
na lura duk kuna cikin fushi”tsaki mr Aliyu yaja yalabarta masa meke faruwa”
to kai MAI NASSARA meye damuwarka sbd kaganta da wani??”ina cefa budurwa ce ita”kaga kuwa budurwa ba’a….look mlm!taya raina na’a b’ace zaka k’aramin wani b’acin ran?” da wasu kalamanka….
Allah yahuci zuciyarka”ni ina parking space,ka tattara komai kasameni mu wuce masjeed lokaci yakusa”yana fad’in hakan yamik’e tsaye yafice”
gaba d’aya mr Aliyu hankalinsa yyi mugun tashi akan fitar yasmeen”
sulaiman yakira yace”amayar da suraj bakin aikinsa” suyi masa waya yadawo”
Ajiye wayar yyi yafara k’okarin had’a abinda zai saka a brief case nasa”
yasmeen ta turo k’ofar ahankali”d’ago kansa yyi suka had’a ido”
Idanuwanta jajir da alama kuka taje wani guri tayi”
yaya Aliyu!!takira sunansa ahankali”
Uhmmm!da kika tafi ina kikaje?”kuma wannan fushin nameye?nafa rigada na cewa sulaiman yadawo dashi aikinsa….
Ajiyar zuciya tasaki tana murmushi”tamkar ba itace tayi kukaba yanzun”
matsowa kusa dashi tayi “tasaka hannunta ta karb’i brief case d’in”
murya can k’asa tace”. nagode sosai yaya Aliyu”insha Allah ko gida bazan kula kowaba”
Da gaske?”Eh”good girl”yafad’a yana kallon yadda take had’a masa komai acikin brief case nasa”
masjeed zakaje ne?”Eh nida khaleel”to ni ina zaka barni?”
Tafad’a ashagwab’e tana narke murya”
Kinga banso kisakemun wani kukan”zan kirashi yaje kawai”nikuma dake zantafi nabarki amota”idan angama saimu tafi gida”
k’arfe nawa zamu dawo office to?”sai 4 pm ko?”sai 6 namayar dake gida”
To kuma yaya Aliyu idan yaya khaleel d’in yaji bbu dad’i fa?”kodai kabarni anan kadawo”
bazan iyaba yasmeen”meeting ma banje dakeba, nabarki nadawo nasameki da wani….baka yarda dani bane?”
Kinga abar maganar muje mota”
batace komaiba ta d’aukar masa brief case nasa suka fita bayan yarufe k’ofar office d’in”
Khaleel na hangosu yadinga dariya abinsa”shikansa yana ganin dacewarsu sosai”
back sit yasmeen ta zauna”khaleel na front sit”mr Aliyu driver sit yazauna yaja motar”
bayan sun hau titi yasmeen ta gaishe da khaleel”
Mr Aliyu yace”.yasmeen gida zamuje na ajiyeki gun imaan kafin nadawo”
amma bazaka jimaba acan?”Eh bazan jimaba”
sosai khaleel ke dariyarsa aransa”sbd yama lura itama yasmeen d’in takamu da soyayyar mr Aliyu”
da haka suka iso gida”yasmeen bbu kunya agaban khaleel tace”.mr Aliyu yarakata ciki sannan yadawo”amamakin khaleel yaga mr Aliyu na murmushi yafito suka wuce atare cikin gidan….
ya girgiza kansa afili yace” wannan irin SALON SO haka?”gsky kun burgeni”Allah yasa imaan tasoni kamar yadda najima da soyayyar ta araina”
na yarda SO bbu ruwanshi da wasa”baka sanin yashiga saidai ka ganka ka kamu dashi…
yana wannan zancen zucin mr Aliyu yadawo suka wuce masjeed”
**********
yasmeen ce da imaan zaune a parlour suna fira bayan sun idar da sallar azahar”imaan plate d’in abinci shak’e da nama agabanta tanaci”yyinda yasmeen tace bazata ciba sai mr Aliyu yadawo suci atare”
suna ahakan yashigo parlourn da sallama”
idanuwansa k’yam akqn yasmeen”turo baki tayi kamar y’ar yarinya tace”.yaya Aliyu shine sai yanzun?”
yana zama gefen ta yace”.ba haka bane yasmen”office akamun kiran gaggawa wlh”
nasan kinata jirana muci abinci ko?”imaan na dariya tace”. Eh mana”nikuwa gashi nama kusa gama cin nawa”
kin sakamana ido ko baby”yafad’a yana kallon imaan”
Dariya tayi kawai batace komaiba ba”
yasmeen muje muci abincin kinjiko?”dato ta amsa yatashi suka wuce dining area”
Imaan na murmushi ta kallesu kawai”sbd ita azatonta soyayya suke tuni sun sanarwa juna ma”
Komai yasmeen ta zuba musu suka fara cin abincin anutse”yasmeen najansa da fira sama sama”
bayan sun idar ne yakalleta yace”.yasmeen Abuja zan tafi ta jirgi k’arfe 4 sai gobe da marece zan dawo insha Allah”
Atake annuriin dake a kan fuskar yasmeen yab’ace”
tayi k’asa da kanta takasa mgn”menene?”kinyi shiru kuma”
nima tafiyar ta dolece yasmeen”amma banaso nayi nesa daku keda imaan”
nidai yaya Aliyu gsky banason tafiyar nan kaje ka kwana” ina laifin kaje kadawo”tafad’a hawaye na wanke mata fuska”
ga wani tsoro yakamata sbd bata manta abinda aymaan yamata ba da mr Aliyu baya gari….✍️
[ad_2]