SALON SO BOOK 1 PAGE 11-12

dan Allah kizauna damu da amana”yasmeen tace”.insha Allah bakuda matsala indai agunane”
Imaan na murmushi ta bita har bed room d’in sa, ta nuna mata duk abinda yafiso”anan yasmeen ta had’a masa ruwan wankan”kafin ta tambayeta Inda kayansa suke”
Imaan ta bud’e wardrobe ta tsakkiya tace”.idan yaya yadawo office yawanci three Quarter da t-shirt yafi sakawa “kinga fannin k’ananun kayan sa nan”tafad’a tana nuna mata”kafin tace”.kifito masa muje muci abinci”nima 4 insha Allah zantafi islamiya”
Ah ah imaan na k’oshi”ai wlh idan bakici girkinaba”yaya zankira nahad’aki dashi tam”
murmushi yasmeen tayi tana k’okarin fito da kayan ta ajiye gefen bed”
Imaan tace”.ga turaruka can muje kid’auk’a kifesa masa”
Sosai yasmeen tayi mamakin tulin turarukansa”
bayan tafesawa kayan sukabaro d’akin atare”
A parlou suka zauna”imaan ta had’a musu abinci acikin tray suka zauna”
Imaan tadinga mata shagwab’ar saita cire hijab nata”
Cire hijab d’in tayi ta yafa d’an kwalin asaman kanta zuwa kafad’arta”
Imaan na murmushi tace”.wlh kinada kyau anty yasmeen kuma da alama kinada gashi”
yasmeen na murmushi tace”.kema haka imaan”
Aini anty yasmeen rashin me kitso ne matsalata”yaya be bari naje kitso”dole saidai azo anan amun”yanzun haka kinga kaina kusan 2 weeks akwance yake”
To kibari mugama saina miki kalba”zuwa week end namiki me kyau k’ananu”
Lah kin iya kitso dama?”
Inadai koyone”cewar yasmeen tana bisimillah suka Fara cin shinkafa da miyar kaji”wacce taji kayan lambu”ga drinks kala kala agabansu”yasmeen azuciyar ta tace garin dad’i yana nesa”
Cikin nutsuwa takecin abincin bbu nuna had’ama ko rashin sabo da bata yawan cin irin wannan cimar”
naman ma cinya d’aya taci tacire hannunta”
Hmmm bakyason sakin jiki ko anty yasmeen saina gayawa yaya”
Ainaci na k’oshi imaan” nagode k’warai”,amma dan Allah karki sanar masa”
murmushi kawai imaan tayi ta kwashe kayan takai kitchen”
bed room d’in ta ta wuce ta d’akko cum da kibiya da man kitso tadawo parlourn”
yasmeen ta aza kan imaan asaman cinyarta, ta since bant d’in kanta”kafin ta taje mata dogon gashinta bak’i ta tsaga”
basufi sunyi k’wara 3″mr Aliyu yashigo cikin parlourn”
surutun imaan yasaka yasmeen bataji sallamar saba”saidai taji k’amshin turarensa”
Da sauri ta rarumi hijab nata tasaka”
yatsina fuska yyi yana tab’e baki”yakauda kansa”dukda ak’asan ransa yaji dad’in yadda yazo yasamesu da imaan tashi tana bata kulawa”
Yaya sannu da dawowa!yauwa baby”kaga anty yasmeen tanamun kitso ko?
Cikin k’osawa yace”.nagani”kasan wani abu yaya?kinga baby agajiye nake zanje na watsa ruwa ne”
To shikenan yaya afito lafiya”itadai yasmeen kanta ak’asa batako yadda ta kalli sashen dayake tsayeba”
Imaan bara neje naji ko yana buk’atar wani abu ne?
To shikenan bbu damuwa”cike da fargaba yasmeen ta tashi ta wuce parlourn sa…✍️
[ad_2]