SAMEEHA A

Sallama ta fara ahankali,ya amsa mata kamar yanda yasaba cikin sallon soyayya da qaunar abar sonshi,,Amaryata ya akayi ne ko kin fara zumudin ganina ne kamar yanda nakasa zaune nakasa tsaye,ummm,ta iya furtawa yace,waini Dan Allah kwanakin nan ba’a jawosu ne Samee wlhy na qagu naganki kusa dani koya najuya najiki ajikina kinsan ko irin son danake miki cikin zuciyata samee zan iya fadawa cikin mawuyacin halli idan har na rasaki a rayuwata,cike da kunya tace,ummm dama sunje gidan kai kaya ne sun tarar arufe shine nake tambaya,ohhhhh ya salam Dan Allah ki basu haquri wlhy Momy ce ta sauya shawara wai tace gidan yamana girma tunda akwai part din da bakowa kusa danata mu zauna anan hankalinta yafi kwanciya kuma wlhy sha’afa nayi Samee sonki ya mantar Dani komai inaba ambaton kiba da begen ganinki akoyaushe dake Shirin tarwatsa zuciyata ban Sanar dake da wuri ba,,umm ba komai yanzu ina zance musu zasu je,nan gidan momy zasu kawo angama gyara komai na 6angaran namu ki qara bawa Umma haquri nasan bazasuji dadi ba,to bari in fada musu suna jirana,saurin me kikeyi ne Samee ko baki son jin muryana ne,a a naga……Sameeha tayi shiru ajiyar zuciya Sameer ya sauke a hankali yace.
Nidai gaskiya ki aje wannan kunyar tun daga gida karma kibari akawo ki da ita dan ba saurara mata zanyiba,dariya Sameeha tayi hade da,umm aikuwa tare za’akawo mu da ita kamar cingom,baki Sameer ya bare da zumar yin kuka da sauri Sameeha ta katseshi,plssss Samee ina gidan kwalliya fa kuma time na ja,idan kina son nabarki sai kinmin alqawarin wani abu guda daya,to mene shi,zakiyi mun idan na fada miki,ina jinka indai baifi qarfina ba zanyi maka,baifi ba ma,to ina sauraronka,plsss Samee karki bare azomin da wannan abar kinji ki yakiceta dazaran andako minke zuwa ni’imantaciyar fadda ta,,ummm mekenan fa,kunyar mana,,tom naji bazata biyoni ba,yauwa kokefa Samee tawa ni kadai,kai kuma nawaye,na Sameeha ta mana har abadan abada….,,dariya Sameeha tasaki sukayi sallam daga qarshe Sameeha tace,ai ko tare zamu zo da abar taka kamar hanta da jine,baki Sameer yakuma budewa da zumar kuka Sameeha tayi saurin kashe wayar tana murmushin jin dadi.????
_Tab akwai chakwakiya,aradu harna hango kunnan ya jummai da bakin_????????????????