Uncategorized

SAMEEHA B

 


*_????SÂMÊÊHÂ????_*

          *_(B)_*

Kan Sameeha ta sauke wayar, wayar ya jummai har ta kutso kai,gaban Sameeha ya yafadi batasan ta ina zata fara fadawa ya jummai ba tatsan yau anshiga (9) kowa saiya ji, abinda kefaruwa dakewa tayi ta daga wayar dazumar magana kanta furta wata kalma tini ya jummai ta katseta da.


    “”Ya dai kin kirashin,Nakirashi ya jummai,shine kika qi ki kirani kina jira ni zan kiraki,ba haka bane ya jummai yanzu nan muka gama wayar dashi,to meyace miki,shiru Sameeha tayi chan tayi qarfin halin cewa gabanta na faduwa.

     Wai gidan Momy sa yace za’akai kayan saboda chan din yamana girma kuma hankalin momy shi saiyafi kwanciya idan muna tare, Kan uban chan……da chan sun san gidan nashi yai miki yawa suka bada makuli harda turo mota nifa bansan iskanci saboda sun rainamu bazamu iya zuba kayan da zaicinye gidan ba shine zai tsiro da wannan fitinar mai suka maida talaka Mara zuciya ko Wanda yakasa,bafa haka bane ya jummai, idan ba haka bane to yaya ne Sameeha wato kareshi zakiyi tun ba’a daura muku auran ba kenan kin qoqarin boye lefinsa,ban boye ba ya jummai momy sa ce tace hakan kinsan kuma bazai mata musuba,,dama ina zaiyi mata musu saboda ubanki ne ina fada kina fada wai ke kin girma zakiyi aure akai ki dakin miji,innalillahi,Sameeha ta furta da sauri ya jummai ta qarasa da’Wa inna ilaihirraju’un ga bala’i ko bari nasami uwar taki dif ya jummai ta katse wayar Sameeha tabi wayar da kallo,,Na shiga uku ni banga aibun wani Abu anan ba duk inda Allah yarubuta zaka zauna anan zaka zauna da gidanshi da gidansu duk daya ne tunda zaman aure zakaje kayi,wai meke faruwa ne Sameeha,zee rigima irinta ya jummai mana daga Sameer yace a gidan momy sa zamu zauna munfasa zama a gidan daya gina saboda hankalinta zaifi kwanciya shikenan fa ya jummai ta hau fada da masifa harda zagina,kice kema dakike amarya guda kin kar6i naki rabon yoni daga cewa kwaliya ake miki na amshi kasona mai tsoka,Sam ba halinsu daya da Umma ba, ita halin Umma daban yake Dana ya jummai, yanzu nasan Umman zataje tasa agaba da masifa wai anrainasu ke kiji Ina zanchan raini anan,ummm nifa wallahi tsoranta nakeji ko ido banso mu hada da ita,dariya Sameeha tasaki zee tace,Dama masifaffu kwarjini garesu musamman irinsu ya jummai da kagansu kasan basuda wasa, kamar kuwa akunan ya jummai zee,Dan Allah ki rufamini asiri Sameeha karkisa daga nan na saita gidanmu wallahi da bazaki ganniba sai agidan ki,kinma isa,suka saki dariya a tare mai makeup tacigaba da aikinta.


A cike dakin Umma yake da jamma’a sai raha ake ana dariya yawanci masu zuwa kafi ne suna jiran ya jummai ta qaraso suji ko mukulin aka bada bashiba ai tundaga tsakar gidan ta fara bala’i harta shigo dakin tanayi duban Umma tayi tace.


“”Hafsa kinga abinda nake gudu ko Dan tsabar rashin mutunci da rainin hankali saida aski yazo gaban goshi sannan zasu chanja magana ai raini ne da wulaqanci wañnan ance ga inda za’aje kafi yanzu kuma sunzo sun sauya magana kamar qananun mutane,suwaye suka sauya din,daya daga cikin matan dasuke dakin ta tambaya,suwaye kuwa banda uwar angon nifa hankalina gaba daya bai kwanta da Matar nan ba tun farko wallahi,,ya jummai Umma ta kira sunanta dawo da dubanta ga Umman tayi tana jiran me zata furta,cikin sanyin murya da fahimta Umma taca.


     Meyake faruwa ne me aka sauya ya jummai.


wai Sameeha Mana Sameer yake fadawa momy sa tace tare da ita zasu zauna a gidanta wanchan gidan daya bamu mukuli mukai kayya yamusu yawa saboda suna tunanin bazamu zuba abin da zai cika gidan ba,a a ya jummai karmiyi saurin yanke hukuncin akan abinda bamu saniba duk abinda zasuce muyi haquri musawa zuciyarmu sallam tunda har anriga an fara bikin nan lfy to mugama shi lfy,badai gidanta tace su zauna ba to babu komai ko ina tace su zauna munsan ‘yarmu zata iya zama da kowa lfy batare tashin hankali ba dama buqatarmu su zauna lfy yanzu muna yin wata maganar zamu iya shafawa Sameeha tabo a idon uwar mijinta da danginsu gaba daya tunda tazama mallakinsu Kinga wa gari ya waya Kan ‘yarmu matsalar zata je ta dawo tun ba’aje ko inaba,hakane kam kowa ya amsa yana fadin gaskiya ne wannan batun na Umma ai zaman aure ba inda baya kai mace qarewa wasu garinma ake bari dasu bare Sameeha da gidane kadai ya hada,maganganun mutane yasa bakin ya jummai mutuwa dolle ba yanda ta iya aka dunguma sai gidan momy danyiwa Sameeha Jere dama kayan duk sun hallara tafiya kadai ake jira,nan matasan mata da qawayen amarya da sauran dangi aka fito filin gidan dayasha (Decoration) da kujeru aka fara (Arabian night) Dan Sameer Babu yanda Bai su hada gaggarin pty ba SÂMÊÊHÂ tace a a ita Babu inda zata zatayi komi nata agida,,, har amarya ta iso aka shiga dansewa ana chashewa da irin rawar nan ta larabawar kowa yasha (Abaya) gwanini burgewa nima ba abarni abaya ba don saida na taka, tsakiyar fili na afa ina kada kai da hannu kamar achan (Sudan) abinka da baqar balarabia????,chan na hango amarya tasha wankan sukari cikin red din doguwar riga mai dutsuna dagani rigar taja ‘yan chanji Dan wata kwaliya ce aqirjin har kusan ciki na manyan dutsuna da qananu masu walwali ba qaramin kyau tayi ba kamar ‘yar tsana dama kyau ya hadu da gyara yakenan masu (pictures) suka fara haskawa kowa kaganshi cikin farin ciki da walwala anata sambadar rawa Ana nishadi kamar Kar Adena ido nane yakai kan wata (Gurasa) datasha kayan hadi gashin yai mugun kyau a ido bare akai baka ga wani (shayi)dayasha (Na’a,na’a)da kayan qamshi tini nafara dumama maqoshina ina yagar gurasar (Larabawar) kadan kadan gudun karta qare nan nadinga raba ido kozanyi arba da (Labal) amma hiru kakeji babu (Labal)babu dalilin(labal).????




“”Koda su ya jummai suka isa gidan momy jere wato inda za’akaiwa amarya kayan dakinta kafin afara sauke kaya sukashiga 6arin momy dansu sanar da zuwannasu su gaisa,sun gaggaisa cikin mutunci da girmama junna Momy kuwa Kamar zata hadiye su sai tambayar ‘yarta take cikin fara’a daga ita sai qanwarta datazo bikin daga (Dubai),Anti Basma kadai a hadaddan fallonta dayasha kayan alatu iri iri daganinsu Kasan akwai’yan chanji jikin luwai luwai kamar najirirai yasha sanyin (Ac),suturar jikinsu ita kanta abin kalloce kunnuwa da hannaye sun kwashi gwala²gwala sai qamshi suke kamar agidan turare,part din da Sameeha zata zauna Anti Basma tayiwa su Yaya jummai jagora da sauran matan ta bude musu (Main)qofar dazata kaisu cikin qaton Fallon mai hade da dakuna aciki da wangameman kicin afalo ta juya tabasu waje suka shiga ciki baki gaba dayansu suka saki kowa yabi dakin da kallo (aljannar duniya) musamman kicin din da komai an zubashi kamar anyi kayan dominsa dakin babu abinda babu aciki na amarya ‘yar gata masu ji dakansu,dukkansu zancan zuci suke suna qara qarewa sarautar Allah ido chan dai daya daga cikinsu ta kasa haquri tace..


Tirqashi yo wannan me mukazo yi kallon daki ko jeran kaya,acewar ya Asabe budar bakin ya jummai kuwa sai cewa tayi. 


Ai da cewa sukayi kawai muzo muga kayan dasuka zuba ba jereba dama ni nasan za’arina sun raina abinda zamu zubawa ‘yarmu saboda su sunfi qarfin muzuba mata dai dai abinda talaka zai zubawa ‘yarsa hmmm harka da masu kudi kwata kwata bashida amfani komai araine sukeyinsa su gasu manyan mutane.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button