SAMEEHA B

”A a’A a fa ya jummai Dan Allah karku kawo wata magana anan kunga agidansu muke muyi abinda yakawomu kawai mu juy ya larai ta furta tana duban ya jummai da fuskarta kwata kwata ba annuri,numfasawa tayi tace.
Yo mai zamiyi Larai ina kikaga inda zamu zuba namu kayan ko ina maqil da kayan qarya da iyayi nifa tafiyata ma zanyi Kar akai ga wulaqantamu,,Babu wani walaqanci anan daganin mutanan Nan suna da mutunci bakiga yanda haqoran Momy suka kasa rufuwa ba ita kanta qanwar ai fuskarta fall da fara’a mu dai yi haquri mu shisshiga muduba din zaifi ai ba’ace komai sunyi ba koba komai muma mazuba abinda babu akayan komai qanqantarsa amma dai mu iya bakinmu harkar Alkhairi ce takawomu ba tsiyaba idanma sun zuba ba ‘yarmu akaiwa ba kuma naga ba roqa mukayi suyi mana ba ra’ayin Kansu ne banamu ba,bawani ra’ayin kansu rainamu sukayi Kawai saboda suna taqama suna da kudi mu bamudashi,,babu zanchan raini anan ya jummai……..sallamar da Anti Basma tayi yadakatar da muhawarar da ya jummai da larai ke tafkawa fuska asake Anti basma ta qaraso ta ajiye wata qatuwar kulla ‘yan matan dake biye abayanta kuma suka ajiye katan din lemuka guda (5) dana ruwa guda (5) suka juya Larai ce tayiwa Anti basma sannu hade da godiya sannnan tace.
Immm baiwar Allah munga abin arziqi muna godiya Allah yasaka da gidan Aljanna yasanya Alkhairi sai dai gashi munzo dakaya babu wajan sakawa,murmushi Anti Basma tayi hade da yi mata nun.,kinga wanchan dakin ba komai a ciki dama shi aka bari domin kuyi naku jeran aciki idan kunshiga zakuga yanda cikinsa yake shi wannan dakin bedroom din na Sameer ne,to to munko gode kuwa Allah yasaka ayiwa momy sannu da hiddima kafin muzo da kanmu,tom ba komai ai anriga anzama Abu daya Anti Basma ta juya tatafi.
Kunga rashin haqurinnaku ko bayin Allah nan Ashe sun bar inda zamusaka namu kayan wlhy Ku dinga ayyana alkhairi akan komai gashidai kunji da kunnanku kuma kun gani,kinga Larai muje muyi abinda ya kawomu ya Asabe ta furta suka nufi dakin da ya jummai, dakin shima qaton fallone da ciki daya babba aciki da bandaki babba mai kyau anan suka jerawa Sameeha kayanta kayan kincin kuwa suka barshi amota aka dawo dashi gida Dan Babu wajan sawa sun kwashi kaji wato (Pepper Chicken) da lemuka harya musu yawa su ya jummai kuwa ko dan²danawa batayiba sai hade Rai take tana kumbura ita adole an rainasu sukaje sukayiwa Momy sallam da Aunty Basma aka rakosu da rafar dubu (20k),Koda suka dawo labarin tsaruwar gidan suka shiga badawa sunata zuzuta kyan da part din SÂMÊÊHÂ yayi Banda ya jummai data fuce daga gidan daga dawowarsu.
Washe gari aka daura aure akan nera na dukan nera har sadaki dubu (1000k), karkuso kuji surutu wasu suyaba wasu su kushe ai anyi qarya mahaifin Sameeha ma dagewa yayi akan sai an rage sadakin yayi yawwa aka dai barshi ahakan aka daura aure anan fa ya jummai tasa masifa Wai basiyar da ‘yarsu zasiba itafa hankalinta Bai kwanta da auran Sameer da SÂMÊÊHÂ ba,Umma tace ai maganar aure yazama tarihi tunda har an riga an daura saidai ayi musu Addu’a Allah yabasu zaman lfy ya Kade fitina,maganar ta 6atawa ya jummai Rai matuqa gaya hakan yasa ta hada kayanta tabar gidan acewar ta bazata zauna akai SÂMÊÊHÂ ba ranta ya 6aci abanxa tunda Umma da Abba sunqi ganne metake nufi,qiri qiri tayi ficewarta kowa na kallonta wasu nabawa Umma haquri.????
Yinni akayi sosai babu abinda ba aciba ba ashaba da yamma akayi walima malamai mata sukayita wa’azin zaman aure da fa’idojinsa da falalar dake tatare dashi idan har mace tabi Allah da Manzonsa tayiwa mijinta biyaya tsakani da Allah,anbada shawarwari akan zama da miji da yanda zaki ja hankalinsa da yawan kwaliya zama cikin qamshi iya girki iya magana tattalinsa da daginsa da girmama uwar miji ita kanta da sauran abubuwa na zamantakewa tsakanin miji da mata su Sameeha kam tasha kuka jikinta duk ya mutu saboda wani girma da nauyi daya hau kanta ga rabuwa da iyaye da ‘yan uwa sai kuka take abin tausaya kowa da haka ya girma inji manya????,Umma kam tamata nasihar da kowace uwa keyiwa ‘yarta idan zata kaita dakin aure hade da yafiya da yimata fatan Alkhairi azaman auranta haka mahaifin Sameeha nasiha sosai yai mata mekashe jiki shima yaimata fatan Alkhairi aka fito da ita da qyar qanwarta moona na kuka Umma nayi itama tanayi kamar bazasu qara haduwaba.
“” Koda aka miqa Sameeha gidan miji bangaran momy aka farayi da ita qawayen momy duk sunsha gayu wasu na tauna cingom wasu na yatsine fuska duk gwala²gwalai ne akunnuwansu sai yauqi suke suna kallon kowa dai dai,haka dai akabawa momy amana tasa hannu ta amsa hade da Allah yabasu zaman lfy cikin fara’a da haba haba da junna aka yiwa Sameeha nasihar zaman haquri da girmama momy da danginsu gaba daya aka shafa Addu’a akai part dinta da ita hade da akwati biyu da momy tabawa Sameeha kyauta na sutura.
‘Yan kawo amarya sun watse kowane na yaba kyan da dakin Sameeha yayi da kayan da aka maqara mata kamar wata ‘yar manya surutu dai na mutane???? aka bar Amarya da qawarta Zee da qanwarta Moona suna jiran qarasowar angwaye,koda su Sameer suka shigo da abokansa kan suyi nashi part din part din momy yanemi uzirin shiga shi kadai abokansa suka tsaya jiransa bai dau wani dogon lokaci acikiba yafito dauke da ledar guda biyu a hannu suka dunguma sai nashi part din,afallo suka iske amaran nan dai akasha barkwanci da tsokana abokan Sameer sukayi musu nasiha dai dai gwargwadon iyawarsu saboda duk suna da aure su ukun zee ma ta Dora Dan abinda tasani sukayiwa Sameeha sallama tana kuka sunayi abokan Sameer namusu dariya suka fito Sameer yarakosu bakin mota sukaja suka tafi ya koma part dinsa.
Rarrashin abar begensa yashigayi da qyar yashawo kanta ta iya tsaida hawayenta jin yace zai tsotso duk wani digon hawayen daya digo akan kuncinta idan yaganshi bashiri ta goge da mayafinta sukatashi Dan gabatar da Sallah suyiwa Allah godiya da ciki musu burinsu dayayi nakasancewa mata da miji atsakaninsu,bayan sun idar da Sallah sunyi Addu’o’i sosai ga Ubangiji Sameer yajanyo musu ledojin guda biyu ya bude,kajine guda biyu banqararru sai tiriri suke sunsha gashi sai qamshi suke daya ledar kuwa madarace ta kwali ya fiddo da ita ya ajiye dakansa yaje kicin ya dako faranti da cofi guda daya yadawo ya ajiye,hannu yasa ya zuba madarar akofi daya ya yago kazar ya kaiwa Sameeha bakinta da sauri ta kauda kai hade da girgiza Kai, hade fuska yai lokaci daya yace.
“”Kina son nayi kuka ko Samee ta, girgiza kai ahankali tayi wani hawaye yasubuto daga idonta zuwa kuncinta da sauri ta dafeshi da lifayarta don kar Sameer ya gane,sake Kai mata kazar yai akaro na biyu dai dai bakinta hade da cewa”*idan baki kar6a ba Allah zan cire lifayar nan nabaki ta qarfin tsiya har sai Naga tumbinki ya kusa fashewa,ido???? SÂMÊÊHÂ ta zaro cikin tsoro da faduwar gaba tace,Ni kam na qoshi,ko duk jikina kunnene bazan yardaba ki amsa kawai kici konayi abinda na furta,sanin kanta ne Sameer zai iya aikatawa ba yanda Sameeha ta iya Sameer yadinga yago (BAQAR KASH????)wato kaza Mara qashi????,yana ciyar da Sameeha da hannayensa cikin shauqin so da qaunar junna harya fara ci shima idan yabata saiya gutsiri inda ta gutsura haka madarar ma ta inda tasa bakinta tasha ta nan shima yake sawa ya shanye harda tandewa Dan ya nishadantar da abar sonnashi harta samishi kukan shagwaba wai ta qoshi shima alokacin ya qoshi yahada kayan yaje yasa naman afirij da madarar yakai sauran kayan kicin ya wanko hannunsa ya dawo fallon.