Uncategorized

SAMEEHA C


Me kikeyi a bakin qofa kika zo kika zauna anan Samee.


Kaga,ta nunawa Sameer kwandon abincin,’Momy ce takawo Mana tace idan mun gama karyawa tana fallo tana jiranmu Dan Allah muje yanzu muji abinda takeso muyi mata Kar mubari tayi ta jiranmu har ranta ya 6aci,bayani takewa Sameer kamar wata doluwa Sameer ya numfasa ya tallafo Sameeha da hannunsa daya,dayan Kuma ya dauki kwandon yace.


‘Taso muje muyi wanka mu shirya Kinga bamaje mata ahaka ba ko karyawa bamiba zatayi mun fada nabar ‘yar mutane da yunwa Wai ya akai nayi baci jiya ko kaya bamu sauyaba.

   Shiru gaba daya sukayi acikin zuciyoyinsu tabbas abinda yafaru adaran jiya na Nan Amma azahirin gaskiya abun na neman kaucewa daga bakunansu duk kansu sun kasa sanar da junna abubuwan daya wakana cikin mafarki ne ko a zahiri.


Duk wani shiri sun gabatar dashi Sameer dakansa ya hadawa SÂMÊĒHÂ ruwa tashiga (bayi)tayi wanka atamfar da zatasaka shiya fito mata dashi sannan yafada bandakin danya Bata waje ta kintsa ganin duk ta takure jikinta kunya da tsoransa sun bayana afuskarta,da hanzari tayi gaggawar shiryawa ta fito Fallon Dan shirya (dining)da duk abinda zasu buqata naci Sameer na shiryawa adaki,hadaddan wani yaddi yasako kalar daya daga cikin kalolin jikin atamfar Sameeha yaddin ya amsheshi yai Masa kyau sosai matuqa gaya abinka da kyan angwanci yafito da kyansa da ‘yar yarintarsa yasami Sameeha tsaye tana hada musu brk,fas tana ganinsa tayi qasa da sauri da murmushi afuskarta ganin kyan da angwan nata yasha tace.


“”Barka da fitowa hasken farin wata Sha kwallo,da murmushi ya fara aika mata kana ya furta.


Ai idan kaga wata to lalai zakaga Zara Sameeha ke tadabance acikin mata nadade Ina godewa Allah daya bani mace Mai hankali da ladabi da biyayya Mara son abin duniya Ashe duk dagewar danayi akanki ba banza ba ke kyautace daga Allah nasan nayi dacan mata mai kyaun suffa da zuciya ki zauna yau Ni zan ciyar da matata da wannan hannayen nawa Kamar dai jiya Amma fa nima sai kin ciyar Dani da kyawawan hannayenki masu albarka ki fara kwasar ladanki tun daga yanzu ba wata kunya.


Kash gashi hannun nawa ciwo yakeyi Samee,ta qarshe maganar cikin zolaya.


Ko zai cire sai an bani ahaka Kinga idan ma ya fita ta hanyar samun lada ya cire saina baki nawa.


Amma ai…….Kinga Sai fa kin ciyar da Dan jaririn mijin Nan naki ko Zaki Kira Umma,harara ta jefawa Sameer tace.


Au zolayata kake Allah zan fasa.


Ya haquri samee na kina fasawa Ina saka miki kuka.


Qato dakai.


Lalalalalalalala Ni dinne qato……..Sameer ya bare baki Yana kukan qarya idonsa Sameeha ta faka ragowar kazar data dako musu daga oven ta dumama tazari cinya guda daya qatuwa ta Danna Masa abaki charaf ya Kama hannun Sameeha da hannunsa yana kokawa da cinyar kaza a baki,kunya ce ta dabaibaye Sameeha tafara qoqarin kwacewa tana dariya shima Sameer dariyar yake ya qara riqeta gam Yana zolayarta ahaka cikin nishadi da Jin dadi suka karya tsaf suna hira a tsakaninsu Sameeha ta Dan saki jiki da Sameer sosai sukasha soyyaya akan tebir din cin abinci.



“““““Fallon baki duk masu aikin suka taru maza da mata suna jiran Momy ta qaraso,Mai girki da mai goge goge sai Mai share harabar gidan daban ruwa wa fulawowi da mai wanki da guga harda Mai gadi da dan’aike wato Mai cefane kowa kaganshi kulle yake da ‘yan kayansa Yana jiran hukuncin da Hajiya zata bada gaban kowa na dukan 3-3, shigowa tayi tasha kwaliya kayan jikinta ba qaramin amsarta sukayi ba ga wani dadadin qamshi da giftawa tayi sai yadaki hancinka sai wani basarwa take tana hada Rai kamar wace aka aikowa da saqon mutuwa,kushin taje ta zauna adosane tafara kada qafa tana duban kowa dai dai dasukayi tsuro suna jiran Mai zata furta, numfashi taja kana tace””””””


“”Nataraku ne badan komai ba sai Dan sallamar wasu daga cikinku,babu wanda ya 6atan ko yayi abinda yakarya dokata daga cikin dokokin Dana shimfida muku illa wata dama Dana samu yanzu da zan amfani da ita acikinku akwai wa’yanda zamanmu dasu yazo qarshe badan komai ba sai Dan zamansu atare dani bazai amfaneni da komai ba Dan haka zan sallameku kuje gaba ko Allah yasa ku samu wani gidan aikin ku cigaba nidai nawa ya qare daga yau,Momy ta qare da duban wani dattijo.


Baba Mai gadi Allah yasoka baka daya daga cikin muta Nan da zan sallama Ina fatan zaka tashi ka koma bakin aikinka.


Godiya nake Hajiya Allah yaqara girma da daukaka,baba Mai gadi yamiqe da qullin kayansa ya fuce daga dakin.


Jalolo kaima baka daya daga cikin Wanda zamansu yazo qarshe agidan nan katashi kabani waje,,.


Da girman kujerarki Hajiya badai mutum da aljan ba Nan gani Nan Bari maqiyanki faddawanki masoyanki Adama mahassadanki ahagu godiya nake farar tumfafiya jalolo yamiqe yafita Yana Mai fasawa Momy kai.


Duban balla Mai wanki da guga Momy tayi kamar zai fashe da kuka tace.


Bala…….Hajiya tuba nakeyi ayi mun aikin gafara Babu inda zanje in rufawa kaina asiri da yarana sama da gidanki Hajiya ki taimakeni yadda Allah yataimakeki ki rufan asi…………Kai dallah rufe min baki anan Bala wani irin gaggawa ne haka bakajira abinda zai fito daga bakina ba kacika mun kunne da haushi ko dadin surutunka zai hanani zartar da abinda zuciyata ta ayana ne.


Tuba nake Hajiya kaina bisa wuyana duk agigice nake wallahi.


Kasani sarai bana Son ban-badanci idan nace zanyi Babu Wanda ya isa ya hanani koya sakani katashi kaban waje ka koma mazauninka Kar in qara bude baki katsomomin wannan dagajajjan bakin naka kagane.


Na gane hajjaju Godiya nake Hajiya Allah shi qara girma ya Raya zuri’a,Bala ya miqe yabar dakin.


Tafa dakai da ladi da suwaiba Ina Mai baku haqurin Gama aiki agidan nan badan kun 6atan  kona gaji dakuba nariga dana sanar daku Babu wani amfani dazakuyi yi mun idan kuna tare dani Dan haka kowane zan bashi (1000k) yaje yaja jari kudin sallama idan Kuma kunsami wani gidan kwa iya cigaba da aikinku.


Gaba dayansu sukayi godiya tabbas kudin da Momy tabasu shiya wanke tabon da zuciyarsu ta samu tun sanda Momy tasanar dasu su hada kayansu ba yanda suka iya mai gidan ta sallamesu hade da kudi masu yawa bazasuga qosawarta ba ko rashin adalcinta ahaka sukayi sallam da sauran ma’aikatan kowane yayi hanyar garinsu Yana jimamin rabuwa da gidan daula duk rashin mutuncin ‘yan gidan zakaci Mai kyau kasha Mai kyau ka kwanta amai kyau har Wanda ke kusa dakai ya dandana……..



*SHIN MAI MOMY TAKE NUFI DA SALLAMAR MAI SHARA DA GIRKI DA BAWA FULAWOWI RUWA?.*


*MAI YASA TAKE NEMAN SAMEER DA SAMEEHA?*


*SHIN MAFARKI SUKAYI KOKO A ZAHIRI NE?*



*_By,Mmñ @ff@ñ✍️_*

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button